8

40 2 3
                                    

HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

           *YESMEEN*

              © *Ummyn Yusrah*
       
                *8*

Har wajen magrib Gwaggo Habi na kwance, ga wani matsanancin ciwon kai da zazzaɓi da ya sameta, ta kuma taƙi yadda ma Alhaji waya a sanar mai kasancewar ba ya gari.

Har wajen k'arfe takwas na dare, ba wanda ya leƙo duba Gwaggo  a cikin gida, sai Zahra ita ma sai ta faki idanunsu, take shigowa gudu-gudu ta dubata ta fice. Mommyn Hanifa ma ta zo ta duba ta, Hanifa kuwa tun da suka shigo ɗaga ta,  ba ta koma ba, ji take kamar ta cire ciwon ta mai da jikinta don har da kukanta.

Ganin har tara ba sauƙin, ya sa Yesmeen ƙiran Hajiya Amira Likita kuma ƙawa ga Gaggon, ta shaida mata halin da take ciki, cikin sa a, ta sanar da ita ga t nan zuwa, yanzu ta fito daga asibiti za ta wuce gida.

Ba a jima ba kuwa ta iso, koda ta yi sallama cikin dakin, Zarah ce kawai ta amsa mata, Hajiya Talatu kuwa da ƙyar ta amsa gaisuwarta. Ba ta damu ba, tunda ba yau farau ba, sai dai ba za ta iya biye wa shirmen nan nasu ba, matuƙar ta zo, za ta yi sallama ta kuma gaida Hajiyar koda kuwa ba za ta amsa ba, gidan ta ta zo dole ta sauƙe nauyin da yake kanta.

Har bakin gado ta isa, bayan sun gaisa da Yesmeen ta ce,
    "Haba! Hajiya. Ki rage yawan sa damuwa a ranki, ki riƙa kiyaye lafiyarki, komai fa ɗan haƙuri ne da juriya, lafiyarki a yanzu ya fiye miki komai, kin sani sarai zuciyarki daf! take da taɓuwa, amma kin kasa sarara wa ranki. Allah ba ya barci, ya kuma fiki sanin halin da kike ciki, ki yi addu'ar jinkirin ya zame miki alkairi. Ba amfanin baɗi ba rai. Da haihuwar yuyuyu ai gara guda ɗaya ƙwaƙƙwara.

Murmushi Gwaggon ta yi, dalilin fahimtar da ta yi na inda hausar tata ta dosa. Ta goge hawayen da ya gangaro mata ta gefen idanuwanta, cikin sanyin murya ta ce, "Kina nema ki sake ja min magana ko? Ba ruwa ne."
"Kai! Amma dai fankan-fankan ba ta kilishi wallahi. Ba sai ki zaune mutum ba ki huta, yadda aka yankoki da arhan nan tiƙeƙiya."

Baki Gwaggo ta taɓe, ta ce,
"Ai sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi likita."

"Ni gyara in gwada jininki in gani." Ta faɗa tana ciro abun gwajin jinin cikin jakarta.

Ta kai kusan minti bakwai tana gwadawa, tana ƙarawa ganin yadda jinin ya hau sosai ya sa ta yi tunanin ko daga abun gwajin nata ne, sai dai duk amsa ɗaya yake ba ta.

Ɗagowa ta yi cikin salonta na tsokana, har da karkata kai, ta ce,
"Oh! Allah sarki! Har na manta yaushe rabon da in ci gumba, ga shi da alama nan kusa zan ci son Raina, don abun namu ne, maganin a kwaɓemu."

"Aniya bi aniya. Ina nan daram! Sai dai ki ci ta wani wajen, amma ba nawa ba. Mutum ai ba a raba shi da damuwa, mussan ma idan kika yi dubi da ƙaddara ta rashin dangi da ya far mana lokaci guda, dole hakan ya sami gurbi a zukatanmu, duk kuwa da ƙoƙari da nake yi wajen ganin na rage." Cikin yanayi na tausawa da hali n da suke ciki ta ce,
"Da gaske jininki ya hau sosai wallahi! Ki na buƙatar kulawa na musamman, idan so samu ne, a tafi asibiti, ki kuma ƙara ƙoƙari wajen ganin kin rage yawan tunanin."

Hannunsu da ke cikin na juna Gwaggo Habi ta matse tare da faɗin, "Zan kiyaye In Sha Allah! Ina matuƙar godiya da kulawarki gareni."

Yesmeen da tun ɗazu take shiga cikin damuwa da jin ciwon da ke damun Gwaggon nata ba karamin damuwa ya jefa ta ba, ga shi har barazanar taɓa mata zuciya yake.

Kukan da ya taho mata ne ya sa, ta yi saurin shigewa banɗaki, a nan ta ci kukanta, cikin sauti mara ƙara, tare da yi wa Gwaggon matan samun lafiya da yayewar damuwa, ya kuma ba ta haihuwa ita ma ko za ta huta da gorin da ake yi mata.

Cikin kalamai masu kwantar da hankali, da lallashi da kuma ƙara nuna wa Gwaggo illar da ciwonta ke tattare da shi, likita ta yi amfani da shi, don guje wa faɗawarta mummunan haɗarin da ke tattare da cutar ta hawan jini.

Magunguna da allurai ta rubuta, ta ƙira Yesmeen ta zo ta siyo a kemis ɗin da ke cikin unguwar tasu, ta kuma gargaɗeta da kada ta yi nisa idan babu a kusa, ganin dare ya yi, ga shi ita ɗaya, don Hanifa ta jima da tafiya, da ƙyar da lallashi Gwaggon ta tafi.

Cikin sa a kuwa ta samu ba su rufe ba, sai dai, ta sami wasu, ba ta sami wasu ba.

Bayan ta kawo, aka yi wa Gwaggo allura ta kuma sha magungunan da aka samu, sannan likita ta tafi tare da yi musu fatan sauki, zuwa safiya za ta dawo da sauran magungunan da ba a samu ba, ta kuma duba ta.

Har ƙofar gida Yesmeen ta rakota tana ƙara yi mata godiya, ita kuma tana ƙara faɗi mata ta kula da Gwaggon nata sosai, domin a yanzu shi ta fi buƙata.

Sai da ta ga tashin motarta, sannan ta juya da nufin shiga gida. Sake dawowa da baya ta yi, don ƙara tabbatar wa da idanunta, abin da ta gani.

Tabbas Rukyy ce da saurayinta zaune kan wani dakali suna hira, yanayin da ta gansu ba a magana, sai dai fatan Allah ya kyauta kawai. Ta shige tana lissafin shekarun Rukkyn da Gwaggo ta faɗi mata, goma sha biyar, sai dai yanayin girman jiki, ya sa ta girmi shekarunta. Abin mamaki kuma har ta iya sakar wa ɗa namiji gangar jikinta haka.

Hannu ta kai da niyyar buɗe ƙofa, cikin sauri ta janye, sakamakon jin tamkar mutum ta riƙe. Da sauri ta ja baya cikin tsoro ta na faɗin,

"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!"

Ta juya za ta sa gudu ta yi waje, ta ji an chafketa, rintse idanuwanta ta yi, ta shiga jero addu o'i jikinta na rawa, don ta san yau kam gamo ta yi, tunda ba ta taɓa kai sha ɗaya saura a waje ba. Ga kuma cafkar da aka yi mata ɗin ba na wasa ba ne.

Cikin muryar raɗa ta ji ance,

  "Yesmeen! Don Allah ki taimakeni, ko leɓen bakinki in tsotsa don Allah, ko zan iya barci mai kyau yau.

Jin muryar, da kuma maganar ne ya haifar mata da wani irin mummunar faɗuwar gaba, tare da ɗaukewar numfashi na hucin gadi.

*2020*

YESMEENWhere stories live. Discover now