3

63 5 3
                                    

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

     *© Ummyn Yusrah*

       *3*

A hankali take buɗe idanunta, tar! Suka sauƙa kan fuskan ƙannwar mahaifinta. Ƙara  rungumeta ta yi, cikin kuka take faɗin,
  "Gwaggo Habi! Sun kashesu, sun raba mu da kowa,sun mai da mu marayu."
Tausayin su ne ya ƙara kamata, ta goge ƙwallar idonta ta ce,
"ki yi shiru, akwai Allah. Addu'a ya kamace su a yanzu ba kuka ba."

Kai ta ɗago, ta kalleta da jajayen idanunta, ta ce,
"In bar kuka? Ta yaya zan daina kuka ba yan abun kukan ne ya samemu Gwaggo? Duk da aka kashesu, ba mu da kowa fa yanzu. Ban san sai yaushe ruwan idona zai daina zuba bisa zaluncin da cin zalin da aka mana. Har abada ba zan daina ba, zan rayu ne, ina addu'ar Allah ya yi wa duk wanda ya yi mana wannan cinzalin irin abin da ya yi mana, shi da dangin shi." Ta ƙarashe maganar tana sake kife kanta a jikin Gwaggo Habi.

"Na ji, koma mene ne ki yi haƙuri, ki tashi mu tafi don yanzu unguwar ba kowa, don ko jiya sai da akasake kawo musu wani harin."
Cewar Gwaggo Habi

"Ki je kawai, ni zan zauna a nan, gara nima su zo su kasheni, don a yanzu rayuwata ba ta da wani amfani."
Ta mayar mata da amsa

"Yesmeen! Ba zan iya barinki a nan ba, yanzu duk danginmu mu uku kawai muka rage, domin Yaya Atika ma, da ke Kano, yau sati biyu kenan da rasuwarta da iyalanta, sakamakon gobarar da ya kama a gidansu cikin dare, wanda ba a san musabbabinshi ba. Ki ta shi mu je da taimakon sojojin nan, na samu na shigo garin nan."

Ba ta kuma cewa komai ba ta miƙe suka yi waje, tana mai juya kalmar gobara da ta yi ajalin yayar  babansu ita da mijinta da yara shida.

Harara ta zabga wa  sojojin, don aganinta ba su da wani amfani, tun da har za a yi wannan ta asar ba su yi yunk'urin hanawa ba.

Fita suka yi daga konannen gidan zuwa wajen motarsu, da ta sojojin da suka yi wa Gwaggo Habi rakiya. Ba zancen diban kaya, don komai ya ƙone, wanda ta dawo da su ma, wajen mai ba ta labarin nan ta baro su.

Kallon gidan kawai take yi, ta ƙara rushewa da kuka shi ke nan ta gama rayuwarta a gida?
Shikenan yanzu rayuwarta ya koma wani garin?
Me yasa ba suyi jinkiri ba,  har sai ta dawo su haɗa da ita su kashe?
Me yasa ta kasance a raye?

Runtse idonta sake runtse idanunta ta yi, yayin da ta ji direban Gwaggo Habi
ya tada motor. har suka bar garin Jos ba ta buɗe idonta ba, sai da ta ji tsayuwar motar da suke ciki, sojojin da suka yi musu rakiya suna fatan a sauka lafiya.

"Oh! wato nan aka  zuba mutanenmu?" Cewar Gwaggo Habi da suka zo wucewa, daidai firamaren wani gari.

A hankali Yesmeen ta furta sunan garin, "Tilden Fulani."  mutane ne birjik afilin makarantar, mafiya yawansu, mata ne da ƙananan yara sai maza ƴan tsiraru, ko wanne ka kalleshi kasan fitowan rashin shiri ya yi.

Tsayawa moton ta yi, suka fito don duba ƴan gudun hijiran ko Allah zai sa su ga wasu daga cikin y'an'uwansu.

Ƴan gudun hijira ne da suka haura sama da mutane dubu uku a cikin makarantar, ajujuwan da ke ciki, shi ne wajen kwanansu, rijiya guda ɗaya tak! Suke amfani da shi, wajen sha, girki, ibada, wanka wanki, da sauransu. A haka kuma ƴan garuwa ke zuwa ɗiba don samun taro sisi.

Kan simintin da ya farfashe ya yi rami shi ne makwansu, babu tabarma balle katifa, ga buhun shinkafa uku da garin masara biyu da gwamnati ta aiko musu dashi don girkawa.

Gefe guda kuma, ga yara birjik! sai kuka suke ba iyaye ba ƴan uwa, duk an kashesu.

Shin wazai tallafi rayuwar wad'annan yaran?

Suwa za su mayemusu gurbin iyaye?

Wani irin rayuwa za su fuskanta?

Wazai tallafi rayuwarsu ya ba su ingantattaciyar kulawa?

A haka rayuwarsu za ta ƙare, ko kuma za su sami masu tallafa musu domin zama manyan gobe?

"Allah ka dubemu, ka zama  gatanmu ka  kuma jagoranci rayuwarmu da ni da wadannan bayi naka."

"Amin Yesmeen! Addu'ar ce kawai mafita a garemu baki ɗaya.
Ta ji Gwaggo Habi ta amsa mata, ba tare da sanin zancen nata ya fito fili ba.

Juyawa ta yi ganin yadda wasu yaran ke kuka da kiran iyayensu, ya ƙara karyar mata da zuciya. Cikin sauri ta nufi mota, tana mai fashewa da kuka. Ji take kamar zuciyarta zai fito ya tarwatse tsantsar zafi da nauyin da ya mata.

Kai ta duƙar jikin kujerar da ke gabanta, ta cigaba da kukanta.

Gwaggo Habi kuwa duk dube-dubensu, ba ko ɗaya cikin danginsu, haka suka juya, tana sharar ƙwallar  da ba ta so Yesmen ta gani, don gudun ƙaruwar tashin hankalinta.

Ba wanda ya kuma magana, har suka iso cikin garin Bauchi. Kai tsaye unguwar Fedral low-cots suka nufa gidan Gwaggo Habin.

Suna isa, ta wuce ɗakin Gwaggo Habi, ka tsaye ta nufi banɗakin da ke ciki don ɗauro alwala, ta yi biyan bashin sallolin da ke kanta.

_2020_

YESMEENWhere stories live. Discover now