*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
*YESMEEN*
*©Ummyn Yusrah*
_4_
Yau satinsu ɗaya da dawowa, sai dai sam! ba ta jin daɗin abin da ake ma Gwaggon nata, yadda dangin mijinta da uwargidan take mata na gorin rashin haihuwa.
Shekarar ta goma da aure Allah bai ba ta haihuwa ba, kullum cikin gori da baƙaƙen maganganu take sha. Wajen mijinta kawai take samun sauƙi.
Wai da wanne za ta ji ne? yanzun da rashin danginta ko da matsalar kishiya da dangin miji na rashin haihuwa?
Me ya sa mutane suke manta cewar Allah shi ke bada haihuwa ba wayon ka ko dabarar ka ba?
Wa za ta kai wa kukanta a yanzu don ya sharemata hawayenta?
Ƴar uwarta da take gadara da ita, ko kaɗan ba su gaban ta a yanzu, giyar kuɗi na ɗinbanta, ta yi watsi dasu ta samu sabin dangi, su ɗin ba kowa ba ne a gare ta.
Za ta cigaba da kai wa Allah kukan ta, shi zai mata maganin matsalolinta.
Haka rayuwarsu ta kasance cikin gidan, duk da ba wani shahararren arziki ga mijin Gwaggon ba,yana da rufin asirinshi daidai gwargwado, yana kuma iya bakin k'ok'arin shi kan iyalan shi.
Ban baki, rarrashi, nuni da illar da tunani ka iya haifarwa da Gwaggo Habi ke yi wa Yesmeen ya sa ta rage nuna mata halin damuwar da take ciki, a zahirance ta ta ware sosai sai dai, kodayaushe tunaninta ya na wajen ƴa uwanta marayu, ko suna cikin wani hali? duk lokacin da za ta wurga loman abinci a bakin ta, sai sun faɗo mata, ko yanzu suma sun samu sun ci? Idan sabon sutura za ta sa sai ta yi tunanin ko suma sun samu?
***
Da sauri ta shiga gidan kamar za ta tashi sama, ko sallama babu ta nufi falon gidan daidai zata wucesu ta ji ance."Toh jikan marasa kunya, dangin yahudu, iyalan kalan dangi da cssa kai. Kin shigo mana gida ba sallama balle gaisuwa kamar da gadon ubale a ciki." Ta ƙare maganar ta na zabga mata harara.
Idanu ta ƙura wa mai maganar, ji take duk sanda taga matar kamar ta daɓa mata wuƙa don tsana.
Baki ta taɓe, sannan ta ce,
"Sannunku kunkuru." Ta haɗe da gwalo.
Wata daga gefe ta ce,
"Faɗi ki ƙara tantiriya, gida namu ne, sai dai mutum ya zo ya ci arziƙi ya ƙara gaba."
dariya ta yi,
"Ruky kike kowa?
Kalleni tsaf! kin san nafi ƙarfin shigowa gidan nan inci arziƙi, ke kanki kin sani."Gwaggo Habi ce ta fito daga kitchen ta ce,
"Ke Hanifa! Akwai sa anki ne cikinsu, da zaki riƙa musu magana haka? kul ko da wasa, ba na son haka, wuce ciki Yesmeen na ɗaki."
Wucewa ta yi ciki, tana ƙara taunar cingam ɗin bakinta, haɗi da huroshi waje.
Hajiya Talatu, kishiyar Gwaggo Habi, ta ce,
"Ai dole ki korata, tunda kin sa ta gama yi mana rashin kunya, haka dai za ki ƙare a kwashe-kwashen ƴaƴan mutane, da cika mana masai."
Ba ta iya tankawa ba, don maganar ya daketa, kicin ɗin kawai ta koma, tana goge ƙwallar da ke shirin zubuwa.
Ihu yaran suka sa lokacin da ta juya, suna ma Uwar ta su kirari, da 'Sai Mama uwar masu gida.'
D'aki Hanifa ta shiga tana kwalama Yesmeen ƙira.
"Ke wallahi kin cika ƙira kamar makauniya, ki ƙaraso gani ciki, guga na ke yi."
"Dallah ki tashi ki shirya, anjima zamu unguwa."
"Unguwa kuma?"
"Ohho! Ni dai ki tashi ki shirya, zuwa ƙarfe biyu za mu tafi."
"Idan nayi niyar zuwa, ko ban yi ba zaki sani dole kenan?"
"Malaman su ai ma dole ki je Wallahi, bari ma ki gani, ɓata lokacina nake yi, idan na haɗaki da dole ki je Baby."
Fita ta yi tana mitar, mutum kullum maƙale a gida, kamar wata mummunar amarya.
"Me kike cewa?"
"Na ce Allah barmu da wannan ƙawar tawa mai tsoron mutane."
"Idan na riƙe ki, zaki faɗa min wace mummunar amaryar".
"Au! ashe kin ji ni ne?"
"A'ah! kin san na zama kurma."
Gwalo ta yi mata, tare da barin ɗakin.Kitchen ta nufa ta sami Gwaggo Habi na ta haɗa abincin rana, ta ce,
"Umma dama na zo tambayarki ne, don Allah Yesmeen ta shirya mu je wajen hidimar bikin ɗiyar ƙawar Hajiyata."
Cikin kulawa ta kalleta, tare da jin daɗin yadda take ƙiranta da Umma.
"Shi ne sai kin tambayeni? Ai an zama ɗaya."
"Ai na faɗa mata, ta ce ba za ta je ba."
Murmushi ta yi, ta ce,
"Tsokanarki take, je ki shirya, zan mata magana."
_2020_