Love you all for the support ♥️♥️♥️
Kwance yake akan gadon asibiti Mami naxaune saman kujerar dakin Anwar yafara motsa kafafunsa Mami tayo kainai tareda Kiran sunansa.
Anwar! Somebody please call the doctor. Momy tafada a tsawace.
Amrah ta! Abunda yafara Fadi kenan kafin ya bude ido a hankali adaidai lokacin doctor yashigo yafara dubasa.
Kada kidamu yama farfado.
Anwar akwai abunda kema ciwo yanxu? Doctor ya tambaya
Mami suntafi da amrah kuma itace "BURIN ZUCIYATA" kuyi wani Abu please. yafashe da kuka
Haba Anwar baka yarda da kaddara bane itama fa yarmuce kapimu sontane. Abba yafada saima yanxu Mami ta lura dashi a dakin. Shiko Anwar ko jinsu ba yayi kuka kawai yake Yana dafe kansa. Abba fita yayi a fusace Mami tabi bayansa.
Alhaji lafiya? Mami ta tambaya cikeda damuwa.
Nimafa inajin abunda yaronnan keji hakuri nake. Abba yafada Yana girgixa kansa.
Kada kadamu kaga yarone har yanxu. Mami ta fada cikeda tausayawa Dan nata.
Shikenan likita xai bamu sallama sai mutafi gida tunda naga yaji sauki.
Toh! Mami ta koma ciki wajen Anwar.
****
Anan bangaren amrah some take har yanxu Bata farfado ba sunshiga da ita cikin wani daji.
Baaba Anya wannan cikar baxamu dan mata a yane ba? Daya daga cikinsu yafada.
Eh wallahi nima haka nake tunani tafa hadu cikar. Dayan yafada.
Duk kumin shiru babu Wanda xaya tabata cikinku idan akwai yayi mu gani. Bangis yafada cikin tsawa ai ko Babu shiri sukayi shuru.
Uncle. Amrah tafada a hankali Tana bude ido.
Ihu tasaki Tana Yan zare zaren ido.
Yi min shiru! Bangis ya daga mata tsawa takara matse jikinta don tsoro.
Kallonta bangis yayi sai yanxu ya lura ashe tamapi yanda yake tunani kyau.
Matse pink lips dinta tayi Tana goge hawayenta. Nantake bangis ya umurci yaransa dasu Basu waje suka tafi. Matsowa yayi dap! Da ita Yana kokarin riqota, Kara firgita tayi tafara kokarin guduwa. Aiko tasa Kai suka bita.
Gudu take har tagaji gashi duk kayan makarantar datake sanye dasu sun yage nantake ta hango titi Tana Hawa domin tsallakawa wata mota kirar Benz ta kadeta. Su bangis naganin haka suka juya cikin dajin don kar agansu.
Wani mutum ne kyakkyawa tareda wata mace alamun matarsace suka fito cikin damuwa dubawa sukayi baby kowa ga amrah kwance cikin jini.
Habibi. Kadauketa muje asibiti. Cikin kuka matar da baxata wuce 20years take magana.
Daukarta guy din yayi suka nufi asibiti direct mapi kusa.
Toh bari mu leqa bangaren goga muga ya yake🤔🤔🤔
Anwar ne kwance a dakinsa sai faman kuka yake kamar mace Yana ambaton Allah a bakinsa Mami tashigo daukeda tiren abinci. Zaunawa tayi kusa dashi ta dafa kafadarsa.
Son! Tafada cikin damuwa
Na'am ya amsa ciki ciki.
Katashi tunfa jiya daka farfado bakaci komai ba.
Amsa yayi yaxauna Tana fita yakoma kwance yaci gaba da aikin kukansa. Itako meerah hankalinta kwance Amma nuna take tafi kowa shiga damuwa.🙄🙄🙄Bayan kwana 4amrah ta farfado Amma kash! Tamanta wace ita sakamakon buguwa da kanta yayi.
Likita yayi musu bayani. Sun shiga damuwa sosai.
Habibi kaga tunda bamu da ya' kuma bana haihuwa Mai xai Hana muriqeta ?
Jinjina Kai ma'aruf yayi.
Shikenan Allah tayamu riqo.
Ameen. Suka amsa, miqewa yayi yanufi dakin da amrah take ciki. Zaune ya ganta Tana kalle kallenta.
Hi baby. Yafada Yana zama kusada ita. Hi but who are you Uncle? Tayi tambayar kamar xatayi kuka.
Nidin Uncle dinkine kinmanta shiyasa.
Jinjina Kai tayi. Am sorry don Allah but mene sunana?
Tunani yayi kapin yace "Amrah" jitayi sunan yadace da ita kapin ta rungumesa.
Mike gida Uncle nagaji da hospital dinnan.
Shafa kanta yayi kapin yakoma Yana tunanin.
Who is she? Koma wace yar' Mai kudice don yaddama yaji English dinta is different kamar Yar turawa. Meya kawota wannan babban titi na garin sokoto? Koma meye Insha'allah xai xame mata gata. Shigowar da farida tayi ta katsesu.
Kuce Kuna hutawane? Tafada Tana shafa kan amrah.
Eh anty amrah ta fada tamkar tasanta han ba karamin Dadi yaiwa farida ba.
Honey kuxauna xanje ayi discharge dinmu. Yafita...
Alhaji yaronnan fah kamata yayi mutorasa kasar waje hutu ko yasamu saukin rashin amrah. Mami tafada tareda kallon Abba
Jinjina Kai tayi eh toh xan turasa India a duba Mana lafiyarsa sai asamu Wanda xasu tafi tare don office inada important meeting satinnan.
Toh nima mexan acan Babu Kai? Kawae muturashi tareda Meerah kaga saima a daura aurensu kapin suwuce idan Allah yasa ta haihu kuma mace basai asmata sunan amrah ba tunda yanxu tsawon 5years Abu yakici yaki cinyewa meerah ke kula dashi.
Eh toh ko xuwa jummu'a sai a daura auren dama nima babanta yamin magana. Meerah data samu lbrn aurenta da Anwar kamar tayi hauka don Dadi har wani Kara natsuwa Tana saka manyan hijab wae don Anwar ya Kula shiko ko ta kanta baibi ba burinshi daya yaga BURIN ZUCIYARSA don shi bai yarda ta mutu ba haka xuciyarsa kebashi yadaina xuwa office daga masallaci sai cikin daki yakara xama miskili fiyeda da.
****
Uncle am back! Wata yarinyace kikanin shekara 20 tashigo kyakkyawa kamar balaraba sanye take da riga da dogon wando baki sai Dan karamin veil datayi rolling dashi dayake rigar har gwiwa take.
Ma'aruf Naga yafito daukeda murmushi a fuskarsa can kuma ya gintse. Murmushi Naga tayi.
Am sorry my sweet Uncle Wallahi Lagos dinnan kasan akwai cunkoso that's why na Dade. Cikin daddadar muryarta take maganar.
Amrah kinsan bana iya fushi dake kawai banaso kina fitane. Ma'aruf yafada Yana shafar kanta.
Toh yaxakayi? Ai dole taje bukin kawarta. Farida tafada Tana saukowa daga stairs.
I miss you Antynah, amrah ta fada Tana rungume faridar.
Miss you too. Farida tarungumeta.
Okay yamiki kyau. Ma'aruf yafada Yana wani hade fuska shi a dole yayi fushi.
Sorry sweet Uncle I miss you more. Dariya suka saka su duka kafin ma'aruf yayi magana.
Kushirya Insha'allah on Monday flight dinmu zai daga zuwa India. Ma'aruf yafada Yana shigewa dakinsa.
Ihu amrah tasaki haka kawae tasamu kanta da jindadi kuma ba yaune tafara xuwa India ba but jikinta yabata wanna farin cikin.
Yanxu muje kiyi wanka. Farida tafada suka shiga ciki su duka...Anan bangaren Anwar kamar ba ango ba yau ake daura aurensa da Meerah mutane sai murna suke masa Amma ko ajikinsa. Daga karshe koda amarya ta tare gidan mijnta a waje ya kwana.🤔🤔🤔
Toh fans koyi voting and comment suna karamin kwarin gwiwa pls🙏🙏