DUKIYAR MARAYU

61 5 1
                                    

*°🔘°DUKIYAR MARAYU°🔘°*
            *1441H/2020M.*
        
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*WattpadNeatlady11.*


*SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD.*

*TUKWICi GA:-* *Khadija Deey😘 writer of KULULU much love my Dije.*

_Special gift to Gaskiya writer's members😁 Allah ya kara had'a kanmu, ya kau da idon makiya masu bacci da ido a kan mu😉 ana ruwa suna irgawa._🤣

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*




_Aye aradun Allah in banga comments kamar ruwan sama ba ko hmmm☹️._


*SHAFI NA 9📑*

*_________*📖 Buga k'ofar d'akin Usman take amma babu alamun za'a bud'e gajiya tayi ta juya da gudu ta koma inda ta bar Amna, babu laifi ruwan ya tsagaita ba kamar lokacin da suka fito ba.

Amna na kwance inda ta barta sai rawar sanyi take hak'oran ta na had'uwa da juna, d'ago kanta Munasa tayi ta dora akan cinyar ta kawai ta fara kuka mai tsuma zuciya, babu abinda take tunani sai iyayen ta da tilon yayan su tabbas mutuwa tayi musu yankan k'auna da ace mutuwa tana shawara da baza ta bari a dauke masu iyaye ba sai dai kash in lokacin mutum yayi ko yana cikin mahaifiyar sane sai ya tafi.

Mai gadi ne ya fito hannun sa rik'e da buta da alamun ruwa zai kama, kamar wasa yake hango su zaune Munasa na faman kuka, da sauri ya k'arasa wajan ya kalli Munasa yace, "Munasa me kike yi anan da wannan ruwan haka?".

Da sauri ta mik'e tace, " Dan girman Allah Baba ka taimaka min Amna taza mutu tun d'azu jikin ta yake rawa," d'urkusa yayi ya wajan ya tab'a wuyan ta yaji zafi rau kamar garwashi yace, "Subahanallahi haka zazzab'i ya rife ta?."

"Eh Baba tun d'azu ne kuma," daukar Amna yayi suka nufi d'akin sa, kwantar da ita yayi ya bud'e wata yar jaka karama ya d'auko pctml ya daga kan Amna ya saka mata a baki aka kora da ruwa.

Kallon Munasa yayi cikin tausayawa yace, "Kiyi hak'uri kinji komai na duniya mai wucewa ne wata rana sai labari, duk Wanda ya cuci maraya Allah bazai barshi ba Allah yana sane da halin da kuke ciki kuma shine zai fitar daku, daga yanzu duk abinda kike so ko yake damun ki kizo ki fad'a min zan baki ko meye kinji ko?."

D'aga kai tayi tace,"Baba gabad'aya gidan nan babu Wanda yake son mu duk sun tsane mu gwara ma Yaya Usman yana kawo mana abinci kuma yace shine indai ina son Abu naje na fad'a masa duk yafi su mutunci har su Uncle din."

Cike da mamaki Baba yace, "Usman din ne yake kawo miki abinci? Kuma yace in kina son Abu ki tambaye shi?".

" Eh shine, duk yafi son mu a cikin y'an gidan shine kawai baya dukan mu baya zagin su Abba."

Baba mai gadi ya girgiza kai cike da mamakin Usman a ransa yace, _Tabbas da wata a k'asa ba haka kawai Usman zai kula dasu ba akwai abinda ya shirya sai dai fatan Allah ya kare su daga sharrin sa._

"Baba ya naji kayi shiru" Munasa ta katse masa tunani tana kallon sa, murmushi yayi yace, "babu komai Munasa, gashi kayan jikin Ku sun jik'e yanzu dame zaku kwanta? Ko zaki je ki d'auko a d'akin Ku?."

DUKIYAR MARAYUWhere stories live. Discover now