*°🔘°DUKIYAR MARAYU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad @Neatlady11.**SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD🥰.*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 19&20📑*
*__________📖* *DAURA.*
Tun lokacin da Uncle Yusuf ya karb'i kud'i a hannu du Yakubu yana fita bai wuce ko ina ba sai gidan su buduwar sa in yayi mata albishir da gobe za'a kawo kud'in auren ta.
Cikin kankanin lokaci aka fara shirye-shiryen biki, cikin kwana uku akayi biki a aka gama amarya ta tare ta gidan ta, tun shigowar amaryar gidan ta mallake komai babu abinda uwar gidan sa wato Ramlatu ta isa tayi tana ji tana gani ita da y'ay'a ta wata tazo ta kwace mata miji.
Sannu a hankali amaryar ta dinga karb'e masa y'an kud'in har ya dawo bashi da komai abincin da zasu ci ba gagarar su yake, tashin hankalin sa yayi a dole sai ya nemo inda su Yakubu suke amma ya rasa.
Haka yake ta bulayin Neman su amma babu su babu alamar su a Daura, cikin lokaci kad'an ya fara nadamar abinda yayiwa y'ay'an K'anwar sa.
Kamar kullum yana zaune a tsakar gida yayi tagumi Ramlatu tazo ta kalle shi tace, "Mai gida ina fad'a maka Wallahi baka fara nadama ba wai ce maka akayi hak'k'in marayu wasa ne da za'a had'a baki da kai a cutar dasu? Kud'i sun rife maka ido ka manta wacece Rukayya a wajan ka yau tsahon shekara nawa baka tab'a neman inda y'ay'an ta suke kuma sunan wai kayi nadama sabida kud'in sun k'are ko? Hmm ina tausaya maka wallahi baka ha komai ba" tana gama fad'a masa hakan ta bud'e labule ta shiga d'aki.
Hawaye ne suke zuba daga idon sa tabbas yayi kuskure Wanda bazai tab'a gyaruwa ba kud'i sun rud'e shi an cuci marayu dashi, a fili yace, "Dole na shiga Kano na nemo inda suke na nemi yafiyar su kuma na basu hak'uri sannan a karb'i dukiyar su daga wajan wad'ancan mugayen" ya a gama fad'in haka ya Mike a fusace.
💞💞💞💞💞💞💞
A hankali take bud'e idon ta Wanda suka yi mata nauyi, dishi-dishi take gani hakan yasa bata gane na kusa da ita a hankali idon ya bud'e ta kalli gefen ta taga Amna a zaune tana kuka sosai, rife ido tayi nan take abinda ya faru ya fara dawo mata da sauri ta yunkura zata mik'e Amna tayi sauri ta rik'e ta tana kuka tace, "sannu Yaya ta Allah ya baki lafiya."
Kallon Amna tayi tace, "Amna meye ya same ni? Me akayi min?" A rud'e take mata wannan tambayoyin idon ta na zubar da hawaye.
Mata dattijuwa ce dake kusa da ita ta k'araso ta zauna kusa da ita ta rik'e hannun ta tace, "Ki daina kuka Munasa Allah yana tare dake kuma zai bi miki hak'ikin ki akan duk Wanda yayi miki wannan aiki Allah sai saka miki, nice matar Baba mai gadi nasan baki sanni ba, tashi muje na taimaka miki ki gasa jikin ki."
Wani irin kuka ta saki mai tab'a zuciya ta cikin kukan tace, "Kenan yayi nasara a kaina? Yayi min fyad'e ya raba ni da abinda ko wacce y'a mace ke tak'ama dashi na shiga uku Allah ka kawo mala'ikan mutuwa ya d'auke ni na huta" ta fad'a tana k'ara sautin kukan ta.
Kuka sosai Amna keyi cikin tausayin yar uwar tata, dakyar aka lallab'a Munasa ta mik'e tayi wanka ta gyara jikin ta amma har lokaci bata daina kuka ba ji take ina ma ta cire jikin ta ta yar Dan gabad'aya ta tsani kanta.
YOU ARE READING
DUKIYAR MARAYU
ActionLabari ne akan yara Wanda suka taso cikin gata da jin dadin sai dai mutuwa tayi musu yankan kauna inda ta dauke iyayen nasu gabadaya, sun sha wuya sunga rayuwa koya rayuwar su zata kasance.?