page 35&36

18 2 0
                                    

🍀🍀🍀🍀🍀
*DUKIYAR MARAYU*
🍀🍀🍀🍀🍀
            *1442H/2020M.*
        
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad @Neatlady11.*


*SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD🥰.*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*



*SHAFI NA 35&36📑*

*__________📖* Kiran sallar da akayi ne ya dakatar da Muhammad daga abinda yake niyar rubutawa, d'ago kai yayi ya kalle ta bata kula shi ba hakan ya saka ya mik'e da sauri zai bar parlourn dan ya san halin mahaifiyar sa kome akeyi indai akayi kiran sallah shikenan an dakatar dashi sai an idar, ya rik'e handle din k'ofar ya jiyo muryar ta tana fad'in, "Daka kayi tunanin kasha kaje in an idar da sallah ka dawo ka rubuta sakin nan na fad'a maka". D'aga kai kawai yayi ya murd'a k'ofar ya fita.

Yana fita yayi ajiyar zuciya mai cike da farin ciki bai tsaya wani tunani ba ya hau mota ya fice daga gidan.

Munasa kuwa tunda ta koma part dinta take aikin kuka Wanda bata San dalilin sa ba kiran sallah kawai ya saka ta tashi tayi sallah, haka tasha zaman ta har bacci ya dauke ta akan sallaya.

Mamy kuwa bayan an idar da sallah ta zauna zaman jiran Muhammad amma shiru bai zo ba hakan ya sa ranta ya b'aci ta dau waya ta kira shi amma layin sa a kashe, kwafa tayi ta mik'e taje ta kwanta itama.

Bashi ya dawo gidan ba sai da ya tabbatar Mamy tayi bacci motar ma a waje ya barta dan kar ta ji karar mota ta farka, a hankali yake tafiya har ya isa d'akin da Munasa take ya tura k'ofa ya shiga da sallama, a kwance ya ganta kan sallaya sai baccin ta take hankalin kwance, murmushi yayi ya zuba mata ido yana kallon ta tabbas Munasa ba baya bace wajan kyau Allah yayi mata baiwa mai tarin yawa, d'aukar ta yayi cak ya dora ta akan gado yana k'ok'arin zare mata hijjabin da tayi sallah ta bud'e ido.

Saurin mik'ewa tayi tana kallon sa shima kuma ita yake kallo yace, "Koma ki kwanta gani nayi kamar hijjabin zai takura miki". Bata ce komai ba ta koma ta kwanta Dan bacci ne a kanta sosai, shirin bacci yayi shima ya koma jefen ta ya kwanta tare da matsowa jikin ta sosai.

Washe gari da wuri ya shirya ya bar gidan lokacin ko Munasa bata tashi ba sabida baya so su had'u da Mamy, lokacin da Munasa ta tashi a kan bedside ta ga farar paper ta d'auka taba dubawa,

_morning lovely wife I hope kin tashi lafiya? Na fita ne amma ba jimawa zanyi ba zan dawo akwai abinci a kitchen kije kici dan Allahu in bai miki ba zaki iya dafa wani, I love u._

bata San lokacin da murmushi ya subuce mata ba ta lumshe ido tana tunanin fuskar sa, tunowa da tayi maybe ma yanzu ya sake ta Sai taji ranta ya b'aci jikin ta yayi sanyi haka ta mik'e tayi wanka ta fara gyare-gyare.

Bayan ta gama gyara parlourn da d'akin da take ta shiga kitchen ta d'auki abincin ta bud'e ta fara ci, tana cikin ci Mamy ta shigo parlourn ko sallama babu mik'ewa Munasa tayi ta durk'usa har k'asa tace, "Barka da safiya Mamy an tashi lafiya".

Haka nan kawai Mamy taji ta burge ta take duk masifar da ta shigo da ita taji ta gushe tace, "Lafiya Qalau, ina Muhammad". K'ara kasa da kai tayi tace, " Ya fita nima ban tashi na ganshi ba."

DUKIYAR MARAYUWhere stories live. Discover now