🍀🍀🍀🍀🍀
*DUKIYAR MARAYU*
🍀🍀🍀🍀🍀
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad @Neatlady11.**SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD🥰.*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 33&34📑*
*__________📖* "Muhammad Sulaiman shine cikakken suna na an haife ni a nan kano nayi karatu na a kasar Uganda, mahaifina Alhaji Sulaiman Isa yana da kud'i sosai fiye da tunanin ki ni kad'ai Allah ya bashi a matsayin d'ah daga ni Allah bai sake bashi haihuwa ba hakan ya sa ya d'auki son duniya ya dora min tun ina karami na, mahaifiya ta Hajiya Salamatu ita kad'ai ce matar Dady tun auren saurayi da buduwar bai sake aure ba har ya bar duniya lokacin ina kasar Uganda ina karatu, na gigita sosai da rasuwar mahaifina dan ya nuna so fiye da tunanin ki yadda yake nuna min so ko mahaifiya ta bata nuna min irin sa."
Haka na cigaba da karatuna na likita har na kammala bayan na gama kuma sai na koma na shiga aikin DSS wato dan sanda na farin kaya, bayan gamawar karatu na na dawo gida gabadaya da zama hakan yasa Mamy ta ta takura min sai na nemo matar aure amma kuma kar na sake na samo wacce ta fita kyau."
"Mamy tana da wata kawa aminiya wacce ta yarda da ita fiye da kowa take nuna mata so amma ita kuma a gaban idon ta tana nuna tana sonta amma a bayan idon ta babu wacce ta tsana sama da Mamy, ko meye ya faru da gidan nan sai Mamy ta kira Hajiya Safiya ta sanar da ita kuma duk abinda tace Mamy bata canjawa a haka za'a bar shi."
"Abinda ya sani na na zama almajiri kuma musaki shine akwai wani shararraren da daba da ake so a kama a cikin unguwar ku kuma yaki kamuwa sabida mutum ne mai wayo duk wata dabara da zaiyi ya gujewa yan sanda ya sani, ba wai yabon kai ba na kware sosai wajan iya batar da kama Wanda in baka sanni b ka ganni baza kace ina da wani abin hannu ba kai ko ka sanni din babu Lallai ka gane ni, hakan yasa a wajan aiki aka zabe ni akace naje na gwada sa'a ta duk da ni babba ne a wajan aikin sai dai na bawa wasu umarani haka nima na sama na suka umarce ni kuma na yarda na karb'a."
"Lokacin da muka fara had'uwa dake shine lokacin da kina sauri kika bige ni baki sani ba ganin yadda kika girmamani take son ki da kaunar ki suka shiga cikin zuciya ta duk da ban gane so bane na dauka kawai kin burge ni ne kawai, tun daga wannan ranar da naga nan ne wajan wucewar ki ya saka na dawo wajan da zama na kuma fara binkice a kan ki har na San labarin ki gabadaya hakan yasa na tausaya miki sosai kuma nayi alkawarin sai na d'aukar muku fansar duk abinda akayi muku, ranar da kika taimaka min kika bani kud'i ranar na tabbatar son ki nake kuma ba karamin so nake miki ba amma na daure na jure ban sanar dake ba, lokacin da kika tambaye ni sunana rasa abinda zance Miki nayi ban San lokacin da nace miki Mudi ba amma harga Allah ko a family din mu babu mai wannan sunan" ya k'arasa maganar yana dariya.
"wallahi Munasa da sonki nake kwana da sonki nake tashi ban tab'a son wani Abu a raina ba kamar yadda nake jin ki, haka na cigaba da dakon sonki kuma ina aiki na har na samu nasarar kama Wanda nake nema na samu kyakykyawan yabo a wajan aiki har na samu karin girma, a wannan lokacin ne na samu labarin anyi raping dinki hankali ya tashi sosai ban tab'a jin b'acin rai kamar ranar ba har wani d'aci na dinga ji a baki tsabar b'acin rai, lokacin da Amna tazo tace kince na gudu sai naki sabida wannan shine damar da zan samu na zama tare da ke hakan yasa naki tafiya yan sanda suka zo suka kamani suka kaini gidan ku, a yadda na same ki ba karamin tausayi kika bani zuciya ta ta dinga zafi ji nake kamar ta tashi na shak'e wannan Uncle din naki dashi da Usman din nan kuma nayi alkawarin d'aukar miki fansa tun a lokacin Dan wallahi sai DUKIYAR Ku ta dawo hannun Ku, lokacin da aka daura aure sai na rasa yadda zanyi dake dan bana so na nuna miki waye ni a wannan lokacin hakan ya saka kawai na d'auke ki na kaiki wannan gidan a matsayin gidan mu amma a zahiri gidan Babah ne kuma Babah d'aya ce daga cikin masu aikin gidan mu da jinin mu ya had'u sosai, duk abinda nayi miki a lokacin nan ba'a son raina bane sai ina so naga zaki iya zama dani a wannan rayuwar ko baza ki iya ba, lokacin da nace kije asibiti har na baki kud'i na fita ina fita na samu wannan mai keke napep din da kika hau na biya shi kuma nace ga Asibitin da zai kaiki ni kuma na shiga gidan su abokina da nake shiryawa na canja kama na hau mota na nufi Asibitin, Shiyasa da kika hau kike ce ya kaiki asibiti mafi kusa ya kaiki wannan Dan nasan daman baki San asibiti sosai a unguwar nan ba Shiyasa nayi haka."
YOU ARE READING
DUKIYAR MARAYU
ActionLabari ne akan yara Wanda suka taso cikin gata da jin dadin sai dai mutuwa tayi musu yankan kauna inda ta dauke iyayen nasu gabadaya, sun sha wuya sunga rayuwa koya rayuwar su zata kasance.?