*°🔘°DUKIYAR MARAYU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad @Neatlady11.**SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD🥰.*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*_BARKA DA SHIGA SABUWAR SHEKARA TA MUSULINCI💃🏻💃🏻 ALLAH YASA MUN SHIGA A SA'A._
*SHAFI NA 15&16📑*
*__________📖* Da sauri ta k'arasa shiga parlourn tana kiran sunan Yaya Usman fuskar ta d'auke da mautuk'ar farin ciki, Usman dake zaune akan kujera ya juyo da sauri dan ya gane muryar ta mai d'auke da zak'i.
Had'a ido suka yi da ita fuskar ta d'auke da murmushi tace, "Welcome back my Yaya koda yake yanzu ka koma ASP Usman," ta fad'a tana kallon fuskar sa .
Kasa magana yayi ya zuba mata ido dan duk yadda yake tunanin yadda ta koma ta wuce nan haka ya bud'e baki kamar dolo yana kallon ta, maganar da ta sake yi ne yasa ya dawo daga hankalin sa yayi murmushi yace, "Welcome sister ina kika shiga ne tun d'azu ina Neman ki?".
Kafin ta bashi amsa Dije tace, " A'a an dawo daga yawon ta zubar din? Dan uwar ki a ina Usman ya zama yayan ki? Keda shi sai sai kallo yarinya tamkar y'ar aikin sa kike."
"Daman itama ta damu dashi ne an fad'a miki? Me zatayi da wani Usman eheee" Amna ta fad'a cikin rashin kunya.
Kallon ta Munasa tayi tayi mata kallon baki kyauta ba ita kuwa ko a jikin ta dan gabad'ayan su haushi suke bata cikin fushi ta bar wajan ta shiga d'akin su.
Uncle Yakubu ne ya fito ya kalli Munasa yace, "A ina kika samu kud'in da aka yiwa waccan Mara kunyar magani?" Jikin tane ya d'au ta fara jah baya cikin rawar murya tace, "Wani likita ne ya taimaka mana amma da tuni Amna ta mutu."
"Ok na gane dole ya taimaka miki sabida kin bashi kanki ko? In ba haka ba babu Wanda zai taimaka miki haka Kawai baki San shi ba, to zaki ci uban ki kuwa yau a gidan nan."
Mik'ewa Dije tayi tace, "Haba nifa naga alama daman a tare da ita kana kallon idon ta kasan da namiji t kwana gashi nan tana warin maza ma" ta fad'a tana k'ok'arin jawo ta.
Kyakykyawan saurayin ne ya mik'e cikin fushi yace, "Haba Dady Ashe daman har yanzu Baku daina takurawa marayun nan ba? Tunda Ku kun kasa taimaka musu ai baza su rasa na Allah ba, to na dawo wallahi babu Wanda ya isa ya cigaba da takura musu babu kamar ke Mommy duk Wanda yayi musu wani Abun zaiga abinda zanyi, Munasa shiga d'aki ki kwanta ki huta kar Wanda ya saka ta aiki yau."
Ganin Munasa ta kasa motsawa sabida tsoro yasa ya rike hannun ta yaja ta zuwa k'ofar d'akin su ya kalle ta yace, "Shiga ciki ki huta anjima kizo ki karb'i tsarabar ki" yana gama fad'a mata hakan ya saki hannun ta ya juya ya bar wajan.
Ajiyar zuciya tayi cikin farin cikin Wanda yake taimaka musu ya dawo badan haka ba da yau ta shiga uku wajan Uncle.
Yana fitowa parlour Dije ta kalle shi tace, "kai Dan baka da kunya daga dawowar ka zaka fara yi mana halin naka na rashin kunya ko? Kasan abinda yarinya ta aikata ne zaka zo ka....." Cikin tsawa ya katse ta da fad'in, "Quite Mommy! Bana son jin wata magana yanzu kuma na fad'a muku kar Wanda ya sake ya tashe ta a bacci in ba haka ba zan sab'awa kowa wallahi" yana gama fad'a mata hakan ya juya da sauri ya fice.
YOU ARE READING
DUKIYAR MARAYU
ActionLabari ne akan yara Wanda suka taso cikin gata da jin dadin sai dai mutuwa tayi musu yankan kauna inda ta dauke iyayen nasu gabadaya, sun sha wuya sunga rayuwa koya rayuwar su zata kasance.?