page 39&40

25 4 2
                                    

🍀🍀🍀🍀🍀
*DUKIYAR MARAYU*
🍀🍀🍀🍀🍀
            *1442H/2020M.*
        
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad @Neatlady11.*


*SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD🥰.*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*



*SHAFI NA 39&40📑*

*__________📖* Ganin bata motsi yasa ya fito a guje a harabar gidan suka had'u da Yakubu bai tsaya yi masa bayani ba kawai ya ja hannun sa suka koma, ganin yadda Dije take hankalin sa ya tashi ya shiga kiran sunan ta amma bata ko motsawa idon sa ya kai inda Bilkisu take ganin halin da take ciki ya sa ya d'ago kai ya kalli Usman ya kasa furta komai sai bakin sa dake rawa alamun yana so ya fad'i magana amma ya kasa.

Ganin haka yasa Usman ya kinkimi Dije ya fita da ita da sauri ya sata a mota sannan ya sake dawowa cikin bakin ciki ya d'auki tilon kanwar sa itama ya sata a mota ya fita daga gidan da gudun tsiya.

Shi kuwa Yakubu gabad'aya jikin sa yayi bala'in sanyi ya kasa motsawa daga inda yake har Garbati ya shigo ya same shi dakyar ya saka ya mik'e suka hau mota suma suka bi bayan Usman.

Asibin kusa da su sika nufa suka yo sa'a kuwa can Usman din ya kaisu, a reception suka had'u sai zagaye yake ya kasa tsayawa Garbati ya k'arasa wajan sa yace, "Usman ya jikin Dijen?".

"Sun shiga da ita har Yanzu basu fito ba". Zama Garbati yayi baice komai ba, sai da aka kwashe mintina talatin sannan likitan ya fito ya kalle su gabadaya yace su biyo shi office.

Bin bayan sa suka yi suka shiga da sallama, likitan ya kalli su yace, "Tsakani da Allah a cikin Daren nan ya akayi kuka bar yarinya k'arama kamar wannan ta fita waje har a samu nasarar yi mata fyad'e mai muni kamar wannan? Yarinya sai zubar da jini take kamar wacce ta haihu." Usman ne yayi k'arfin halin cewa, "yanzu a wanne hali take ciki?".

"Mun samu jinin ya tsaya anyi mata dinki yanzu ta samu bacci amma Gaskiya Ku kai report wajan y'an sanda Dan bai kamata a bar irin Wannan masu b'ata yaran suna abinda suka ga dama ba."

Yakubu yace, "Ita kuma Dije ya jikin nata?". Likitan ya cire glass fuskar sa yace, "Sakamakon mummunar razana da tayi ta samu cutar b'arin jiki amma kar Ku damu indai zata shan magani tana zuwa ganin likita abin zai zo da sauki, ta farfad'o ita amma sai kuka take kuma a halin da take ciki bai kamata a bar ta tana saka damuwa ba so zaku iya shiga ciki Ku ganta."

Jiki a sanyaye suka mik'e suka shiga d'akin da suke kwance tun a bakin k'ofa suke jiyo muryar Dije tana kuka, tsayawa Usman yayi cak ya kasa k'arasawa ciki ya tsuguna a wajan ya fashe da kukan bakin ciki.

A ciki suka samu Aysha da Gambo da Amna Dije na ganin shigowar su ta sake fashewa da kuka tana fad'in, "Usman ya cuce ni ya cuci rayuwar kanwar sa ya rasa wacce zai lalata a duniyar nan sai kanwar sa da suke ciki d'aya wannan wacce irin masifa ce na shiga uku ni Dije" ta fad'a tana k'ara fashewa da kuka sosai har muryar ta ta daina fita sosai sabida yadda bakin ta ya fara komawa gefe.

Sai a lokacin su Garbati suka fahimci Usman ne yayiwa Bilkisu fyad'e su Kansu abin ya tab'a su dan basu d'auka akuyancin nasa ya kai haka ba.

Dije tace, "Na rasa yadda zanyi da raina Ashe haka uwa ke ji in akace yan lalata yarinyar ta? Wayyo ni Dije na shiga uku".

DUKIYAR MARAYUWhere stories live. Discover now