DUKIYAR MARAYU

24 2 0
                                    

*°🔘°DUKIYAR MARAYU°🔘°*
            *1441H/2020M.*
        
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad Neatlady11.*



*SADAUKARWA GA:-*
*My Real friend ZEEYSD.🥰*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*





_Alhmdllh cikin ikon Allah yau gashi na dawo a cigaban wnn littafi, kamar yadda kuka sani rashin comments yasa na maida shi na kud'i hakan yasa nake ganin masoya na na asali wajan ganin sun siyi littafin sun karanta, Allah ya sani ba da gaske nake ba wnn dalili yasa duk wacce ta turo min katin waya da niyar siyan wnn littafi na mayar mata dashi Dan bani da niyar siyar dashi, waya da kuma message's din da nake samu yasa zan cigaba da rbt wnn littafi Dan banyi tunanin ana sonsa kamar haka ba Shiyasa nima bazan juyawa masoyana baya ba amma in bana samun comments yadda ya kamata xan ajjiye alk'alamin rbt wnn littafin wannan shine hukuncin Dana yanke, nagode da kaunar da kuka nuna min._💗💘🥰

_Barka da sallah ina fatan anyi sallah lfy an gama lfy Allah ya maimaita mana amin._


*SHAFI NA 11&12📑*

*__________📖* Amna da gama wankan ta kenan ta niyar fitowa taga yarda Munasa ta shigo A rikice kuma da Alamu bama tasan ta shigo ba yasa duk ta rikice itama  tana tambayar ta lafiya?

Ruwa kawai ta tsakarwa kanta tare da yunkurin wanke yajin amma duk da haka ji take kamar yanzun suka zubamata.

Kawai kuka ta fara tsabar yarda take ji cikin muryarta data ji jiki tace "Amna ki taikama min zasu kashe ni yaji suka zubamin A kas...".

Cikin k'araji Amna ta furta "What yaji!!!! Yaji fa kike ce?."

Ita kuwa Munasa ta manta da wata Amna tuni ta cire towel din cikin ta ta shiga cikin ruwan d'umi ko zata ji sauki.

Ganin haka Amna yasa ta fita da sauri zuciyar ta a cushe tabbas yau babu Wanda zai hana ta daukarwa Yayar ta fansar abinda akayi mata.

Cikin b'acin rai take shiryawa tana gama saka kaya ta fito a fusace ta nufi main parlour Dan tasan suna zaune.

Ganin yadda ta nufo su yasa Dije tasha jinin jikin ta Dan da ace Amna ce da shekarun Munasa to da tabbas sai ta gagare su dab yarinyar a tsaye take bata da kunya ko kad'an.

Cike da rashin kunya Amna tace, "gaskiya Aunty da Mommy abinda kuke yi baya dacewa ace Ku d'auki yaji Ku zubawa mutum Ku yanzu in akayi muku hakan zaku ji dad'i Dan tsabar rashin imani ko kuma Dan Baku San ciwon haihuwar ta ba."

A fusace Aysha ta mik'e tace, "Keee karya iyayen nawa kikewa wannan rashin kunyar Dan baki da hankali? A cikin gidan mazajen su kike fa kinzo cin arzuki kike musu wannan maganar, an zuba mata yajin kiyi duk abinda zakiyi ki ke aka yiwa dole ki hak'ura."

"Ke dallah can yi min shiru bada ke nake ba ki bari ki isa tukunna nayi dake ba yanzu ba mahaukaciyar banza kawai" Amna ta fad'a tana nuna Aysha da yatsa.

Juyowa tayi ta kalle su gabad'ayan su tace, "daga yau wallahi na daina daukar duk abinda za'a yi min ko Yaya ta eye muma y'ay'a ne kamar kowa" tana gama fad'in haka ta juya ta bar wajan.

DUKIYAR MARAYUWhere stories live. Discover now