DUKIYAR MARAYU

14 2 0
                                    

*°🔘°DUKIYAR MARAYU°🔘°*
            *1442H/2020M.*
        
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad @Neatlady11.*


*SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD🥰.*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*




_Kar Ku manta dani a addu'ar ku😰 exams na dada tawowa._


*SHAFI NA 27&28📑*

*__________📖* Mik'ewa Garbati yayi yace, "Kai malamai ya ishe Ku haka kuyi mana shiru, kowa ya bar nan anjima a dawo" cikin harare-harare ko wacce ta bar wajan.

D'aki Gambo ta shiga ta kalli Aysha tace, "ke fad'a min gaskiya meye tsakanin Ku da Usman in kuma kika yi min k'arya sai na karya ki".

" Mama abinda ya fad'a gaskiya ne amma ni Wallahi bayan shi bana zuwa wajan kowa kum....." Saukar marin da taji a fuskar gane ya hana ta k'arasawa, cikin fushi da tashin hankali tace, "Dan uban ki daman abinda kike yi kenan? Ashe da gaske ba sharri yayi miki ba ke yar iskar sace kina da hankali kuwa Aysha? Meye dalilin ki na aikata haka eye?".

Kuka ta fashe dashi tace, "bafa laifi na bane ba shine ya dinga lallaba ni har na yarda kuma ni dan ina son sane da bazan amince ba dashi ba".

" Uwar son sa kike dan uban ki so ne ya rife miki ido har kika bada mutuncin ki Dan baki da hankali baki San me kike ba, gashi nan ai Kin cuci kanki kuma kin cuce ni waye zai aure ki bayan kin gama raba kanki tun a waje kin bani mamaki Aysha ina wayon ki ya tafi," shiru tayi sannan ta cigaba sa fad'in, "Amma babu komai ta inda aka hau ta nan ake sauka Wallahi Dole Usman ya aure ki ko yana so ko baya so tunda shi ya lalata ki".

Garbati dake tsaye a bayan su yace, " Dolen sama Wallahi dan bazai lalata min y'a a banza ba daga shi har iyayen nasa babu Wanda ya isa ya saka a fasa auren nan indai ina raye, ke kuma zan zo kanki ne" ya fad'a yana nuna Aysha tare sa ficewa daga d'akin.

B'angaren Dije da Yakubu sun saka Usman har sai da ya sanar dasu gaskiyar shine silar lalacewar ta,  Dije tace, "Tunda abin haka ne kuwa indai ni na haifi Usman bazai auri Aysha ba wallahi dan ina son sirika mai mutunci ba yar iska ba, kwantar da hankalin ka Usman babu Wanda zai aura maka Aysha babu kai babu ita".

Wani sanyin farin ciki Usman yaji yana ratsa shi ko babu komai hankalin sa ya kwanta dan shi har ga Allah ya gabatar da Rufy ne kawai daga baya kafin auren yasan yadda yayi ya zame amma shi bazai auri wacce ya sani a waje ba shi sai hazifazar alkur'ani, Uncle Yakubu yace, " Nima ina bayan ki babu Wanda zai aura masa lalatacciya dama iya Usman din take bi da yafi amma waye yasan adadin mazan da take zuwa wajan su, dan haka nima na janye kaje ka auri wacce kake so."

Bayan wasu lokaci kowa ya dawo parlour ya zauna ana jiran hukuncin da za'a yanke, Gyaran murya Yakubu yayi yace, "Tunda abin ya zama haka ni na janye had'a auren Aysha da Usman kowa yaje ya nemi Wanda zai aura" Dije dake kusa dashi tace, "Shine dai-dai dan d'ana bazai auri karuwar gida ba" ta fad'a tana hararar Gambo.

Garbati ya gyara maza shima yace, "Naji hukuncin da ka yanke amma ka sani Wallahi tallahi indai ina raye sai Usman ya auri Aysha tunda shine ya lalata ta dole shine zai aure ta ko kuna so ko bakwa so sai anyi auren nan dan bai isa taci banza ba Wallahi" Gambo ita tace, "Fad'a musu dai gwara su sani tun wuri".

DUKIYAR MARAYUWhere stories live. Discover now