*°🔘°DUKIYAR MARAYU°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*WattpadNeatlady11.**SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD.*😘Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 10📑*
*__________📖* Sai da cikin ta ya d'aga tayi gyatsa tayi ajiyar zuciya ta godewa Allah, sai a lokacin taji dama-dama ta mik'e tana dafe kai ta shiga ciki.
D'aki ta shiga ta kwanta a k'asa tana kuka tama rasa kukan me zata yi, na rashin iyaye kona rashin gata kona rashin Wanda zai taimaka musu, bud'e kayan ta tayi ta kalli Amna dake kwasar bacci tayi murmushin takaici ta cigaba da birkita kayan ta, ta d'aga wata riga kenan kud'i y'an d'ari-d'ari suka fad'o.
D'aukar kudin tayi nan take hawaye suka cigaba da zuba a idon ta, ko shakka babu wannan kud'in da Aunty Zainab ta bawa Hydar shi kuma ya raba ya bata yace ta ajjiye wata rana zasu yi mata amfani.
D'aukar naira D'ari tayi ta saka a k'asan rigar su da niyar siyo prctml Dan ta ajjiye musu, tana niyar mayarwa taji an fizge kud'in, a tsorace ta d'ago kai Dan tasan kashin ta ya bushe.
Had'a ido suka yi da Aysha ta zuba mata harara tace, "wato bayan bin maza har sata kika fara ko? To wallahi sai na fad'awa Mommy" ta fad'a tana ficewa daga d'akin da sauri.
Tana zaune taji ana kwallo mata kira ba shiri ta mik'e ta fito jiki a sanyaye ta durk'usa ta sunkuyar da kai, Aunty Dije tace, "Wato kedai Munasa kin zama yar iska ko? Bayan bin maza da kike har sata kika fara ban sani ba, sune fa kud'in da nake nema d'azu ne har nake tambayar ki Gambo Ashe ita ta shiga ta sace to Allah ya tona asirin ki shegiya matsiyaci gaton tsiya."
A hankali ta d'ago kai tace, "Wallahi Aunty ban d'aukar miki kud'i ba wannan kud'in Aunty Zainab ce ta bamu su ranar da...." Cikin tsawa Aunty Dije ta katse ta da cewa, "Za ki min shiru ko sai na rusa miki kai dake da Zainab din ai duk halin ku d'aya wannan dai kud'i na ne ba kuma zan bayar ba kuma hukucin sata shine babu ke babu abincin Daren yau, tashi ki bani waje."
Cikin sanyi jiki da rashin abin fad'a ta mik'e ta fice.
_After 1 week._
A cikin kwanakin komai ya dad'a tsauri bata zuwa makaranta kullum sai goma na safe kullum cikin dukan ta ake gwara ma islamiyya tana samun time sosai, a cikin satin aka samarwa Usman admission a Police Academy dake garin Katsina ya tafi badan yaso ba.
Munasa ta rame tayi bak'i zuwa yanzu ta gama sabawa da duk aiyukan gidan, Baba mai gadi ne kawai yake tausaya musu shima kuma a b'oye in ba haka ba k'arsen aikin sane yazo.
After 6 years.
Wata kyakykyawar buduwar ce ke faman sauri akan titi, gabad'aya hankalin ta baya jikin ta so kawai take ta ganta a gida hankalin ta ya kwanta, karo tayi da mutum littafan hannun ta suka fad'i a k'asa, d'agowa tayi ta kalli Wanda ta buge tace, "Dan Allah kayi hak'uri bawan Allah sauri nake ban kula da tawowar ka ba."
D'an murmushi yayi yace, "Babu komai kwashe littafan ki ki tafi babu komai."
D'aukar littafan tayi sai a lokacin ta kalli mutumin sosai a ranta tace _Ayya Ashe Almajiri ne gashi ko hannu bashi dashi k'afar sa d'aya a shanye._
YOU ARE READING
DUKIYAR MARAYU
ActionLabari ne akan yara Wanda suka taso cikin gata da jin dadin sai dai mutuwa tayi musu yankan kauna inda ta dauke iyayen nasu gabadaya, sun sha wuya sunga rayuwa koya rayuwar su zata kasance.?