DUKIYAR MARAYU

10 1 0
                                    

*°🔘°DUKIYAR MARAYU°🔘°*
            *1441H/2020M.*
        
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼*
*G.W.A Welfare.*
*Wattpad at Neatlady11.*

*SADAUKARWA GA:-*
*My real friend ZEEYSD😘.*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*


*SHAFI NA 13&14📑*

*__________📖* Gaban ta ne yake fad'uwa nan take tsoron Allah ya shige tunani ta fara in Allah ya karb'i ranta a wannan lokacin tace da Allah me? Ja da baya take tana kallon mai shagon yana matsowa kusa da ita fuskar sa dauke da murmushi.

Runtse ido tayi gaban ta na fad'uwa, hannu ya mik'a da niyar tab'a ta tayi wuf ta zille ta bud'e k'ofar a guje ta fice daga shagon.

Reception din ta koma ta kalli inda ta bar Amna sai dai babu ita babu dalilin ta, dube-dube take ko zata hango ta amma bata ga mai kama da ita ba, hankalin ta ya tashi sosai ta fara kuka tana kiran sunan Amna.

Zama tayi a wajan ta kifa kanta a cinya tana kuka sosai, ji tayi an dafa ta yasa ta d'ago wata nurse ta gani tsaye a kusa da ita tace, "Ba kece wacce kika kawo Amna Aminu ba?."

Cikin sauri tace, "Eh nice tana ina?" Nurse din tace, "Ina kika shiga ana Neman ki  tun d'azu?".

" Naje nemo kud'in da zan biya kud'in gado amma har yanzu ban samu ba."

"Ok to kar ki damu yanzu haka kanwar ki tana k'ark'ashin kulawar likitoci sabida Allah ya kawo Dr fisabinillah ya bata umarnin a shiga da ita kulawa ba tare da ko sisin ki ba."

Farin ciki ya mamaye zuciyar Munasa ta rasa wacce kalar godiya zata yi kallon nurse din tayi tace, "Dr fisabinillah shi kuma haka sunan sa yake? A ina zan ganshi dan nayi masa godiya?".

Murmushi nurse din tayi tace, " Ai baza ki tab'a ganin sa ba dan yanzu haka yayi nisa a hanyar Abuja, shi yana taimako ne ba tare da kin San shi ba kuma baya so ki sanshi that why ma bai cika shigowa gari ba kuma in ya shigo baya kwana biyu ya bar Kano, kije yanzu wajan yar uwar ki sai ki dawo na baki Labari Dr. "

Nuna mata d'akin tayi ta nufi d'akin zuciyar ta cike da mamakin wannan bawan Allah.

A kwance taga Amna idon ta a bud'e da alama ta farka wata nurse na tsaye a kusa da ita yana cike-cike takarda, Munasa na shiga ta k'arasa wajan Amna ta rike ta tana kukan farin ciki, kallon ta nurse din tayi tace, "Yawwa gwara da kika shigo tun d'azu data farka take Neman ki ba wani ciwo taji sosai ba duguwar da kanta yayi yasa ta suma amma yanzu Alhamdulillah komai yayi dai-dai nan da safiya ma za'a iya Baku sallama, ga kud'in magani da Dr fisabinillah ya bayar a baku yana fatan Allah ya bata lafiya" ta fad'a tana mik'o mata y'an d'ari biyar-biyar masu yawa.

Karb'a tayi tace, "Nikam Dan Allah waye wannan bawan Allah mai taimako?."

"Mutum ne kamar ki kuma da ace lokacin da ya shigo kina nan da kin ganshi yau to daman shi haka yake so ya taimaka miki ba tare da kin Sanshi ba kuma yana gama abinda zaiyi a yanzu ya wuce Abuja mu da mu kuma ganin sa kuma za'a jima gaskiya."

Munasa tayi murmushin farin ciki tace, "To Allah ya saka masa da alkairi ya raba shi da iyayen sa lafiya ya bashi yara na gari."

Suka amsa da amin ta fice ta barsu a d'akin.

Zama tayi kusa da Amna tace, "Sannu my k'anwa ya kike ji yanzu?".

Mik'ewa tayi zaune tace, " Alhamdulillah naji sauki sosai sannu kinji Yaya ta Allah ya baki miji na gari."

Tayi murmushi tace, "Amin Amna, wai me kika yiwa Uncle ne yayi miki wannan dukan?".

Tsaki tayi tace, "Hmm Bari dai na samu sauki sosai wallahi har shi sai na koya masa hankali nasan wannan shegiyar matar tasa ce taje ta had'a mu akan naje na ja musu kunne akan abinda suka yi miki shine taje tayi min k'arya to wallahi zata San ni tayiwa wannan abun."

Baiwar Allah ita ta manta ma da wani Abu da suka yi mata duk da har yanzu tana jin rad'ad'in yajin amma rashin lafiyar Amna yasa ta manta ma, shiru tayi mata Dan tasan ko tayi mata magana baza ta ji ba yanzu.

Ajiyar zuciya tayi tace, "Amna ban tab'a ganin mutum irin wannan Dr ba ba Dan shi ba da ban San yadda zanyi ba Allah yayi masa albarka baza mu tab'a mantawa da taimakon  sa gare mu ba har abadah."

"Haka ne kam Yaya ta nima baki ji yadda ya burge ni ba wallahi Allah ya bashi yara na gari".

Suka amsa da amin suka cigaba da hira sama-sama.

Da safe wajan k'arfe goma da rabi aka basu sallama tare da magunguna suka fito daga asibitin hannun su na sark'e Dana juna.

Tafiya suke a k'asa suna yar hira sama-sama har suka gifta wani waje, cak Munasa ta tsaya tare da komawa baya tana kallon gefe d'aya, kallon inda take kallah Amna tayi tace, " Yaya ta me kike kallo ne?".

Bata yi mata magana ba ta juya ta nufi inda take kallah, itama binta tayi itama Dan ganin inda zata nufa.

Da murmushi a fuskar ta ta k'arasa wajan wani mutum dake zaune yana jiran na Annabi, sallama tayi masa tace, "sannu bawan Allah".

D'agowa kai yayi ya kalle ta yace, " Sannun ki kema akwai abinda kike nema ne?".

Tsugunawa tayi tace, "baka gane ni ba nice wacce na bige ka jiya ina sauri."

Murmushi yayi yace, "Auho na gane ki ya kike?."

"Lafiya lau nake Zan wuce ne nace bara nazo mu gaisa, a nan kake da zama ne?".

" Eh a nan nake sai dare yayi nakan je inda muke kwana, gaskiya nagode da ziyarar ki kece mutum ta farko da kika tab'a kawo min ziyara."

Murmushi tayi cikin kud'in da aka basu a asibiti ta ciri naira dubu d'aya ta mik'a masa tace, "Ga wannan ka siyi abinci kuma insha Allah zan dinga kawo maka ziyara."

Gigicewa yayi yana zuba musu godiya harda hawayen farin ciki kamar tasan tun safiyar jiya rabon sa da abinci, godiya ya dinga yi mata har ta gaji da amsawa ta mik'e tayi masa sallama suka bar wajan.

Da kallo ya bisu nan take kaunar Munasa ta cika masa zuciya.

Kallon ta Amna tayi tace, "Ina kika samo wannan mutumin? Yaya ta mai kwashe-kwashe."

Dariya tayi tace, "almajiri ne bashi da hannu ga k'afar sa a shanye duk tabo a fuskar sa wallahi tausayi yake bani Shiyasa nima na taimaka masa a cikin wannan kud'in kuma xan dinga kawo masa ziyara a kai akai."

Amna tace, "to shikenan amma dai kibi a hankali kin San halin da muke ciki."

Cigaba da tafiya suka yi har suka iso bakin gate din gidan, bud'e musu Baba yayi yana yiwa Amna ya jiki, Munasa ta kalle shi tace, "Baba lafiya na gidan a cike?".

" Eh yau Usman ya dawo yana ciki."

Murmushi ya bayyana a kan fuskar ta Usman Dan har abada baza ta tab'a mantawa da taimakon sa gare su ba.

Cikin farin cikin mai taimakon su  yazo ta nufi cikin gidan da sauri.


Topa Usman ya dawo shin har ynz da wannan mummunan kudurin nasa akan Munasa? Shin in akwai zaiyi nasara ko kuwa?.



#comments
#vote
#share


© *NEAT LADY.*

DUKIYAR MARAYUWhere stories live. Discover now