HABEEYTAH

4.4K 54 8
                                        

*HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
    *UMMUH HAIRAN*

_Please ki biya kafin ki karanta nidai bazanyi Allah ya isaba Amma ban yafeba, da masu fitarmin da masu karantawa basu biya ba kuda Allah_

*2*

Da sauri ya fita ya dauki boxes dinsa ya sanya ya koma ya sake kamota jikinsa yace “Hab...beey meye inane garin yayane ciwi naji miki" daga kanta tayi idanunta a lumshe yana zubar hawaye tana qara riqe cikinta ya dagata da azama ya fita da ita ya kwantar ta ya fice.
Sama ya haura da sauri ya shiga knowking qofar da zata kaishi dakin baccin Granny, bugun taji bana hankali ba ta miqe da sauri ta fito ta bude taganshi tsaye tace “lfy?" Hannunta ya kama yace “bansan meye matsalar ba amma Habeey batada lfy sai riqe cikinta takeyi"

Binsa tayi suka nufi qasan suka shiga dakin suka tarar da ita a qasa cikin ysnayin azabar ciwo, da sauri suks matsa suka kalli juna yace Granny ko asibiti zamu kaita ne tanajin jiki fah" tsugunnawa Granny tayi tace “cikinta wata nawa ne?" Yanakai hannunsa zai dauki Habeey din yace.
“Wata bakwai..." Bai iya qarasawa ba saboda yanda yaji ta fara jijjiga a guje sukayi waje cikin tashin hankali suka sanyata a mota Granny tayiwa security mgn suka rufa musu baya suka nufi wani asibitin kudi dake cikin garin azare.
Suna zuwa suka dauketa suka nufi wani daki da ita suka fara kulawa da ita, sunsha wahala ta sosai kafin susa mata ruwan naquda saboda ganin ana Shirin yin biyu babu, da taimakon Indurcing din da sukayi mata da Kuma jajircewarsu suka ciro mata kyakkyawar qatuwar yarta me masifar kama da Taheer suka duqufa wajen ceto tata rayuwar.

Fita sukayi da jaririyar da nufin kaita dakin da zaake kula da ita Taheer dake zaune ya hade kai da gwiwa sai bugawa zuciyarsa takeyi ya dago da sauri ya nufosu Dr yayi masa murmushi yace.
“Anyi nasarar ciro maka baby girl dinka tana cikin qoshin lfy saidai batakai lkcn haihuwa ba zaa kaita dakin kulawa ita kuma uwar tana cikin halin commer sakamakon hatsarin jijjiga data samu saidai ku tayamu da addu'a Allah ya dawo da ita cikin hayyacinta nan da qarfe biyun rana idan ba hakaba komai zai iya faruwa.
Ba Taheer ba hatta Granny saida cikinta ya kada wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yace “Dr kada kuyi sakaci don Allah Tanada muhimmanci a rayuwata" dafashi yayi yace “insha Allahu komai zaizo da sauqi"

Matsawa yayi ya leqa fuskar yar tasa kyakkyawa da ita ya sauke ajiyar zuciya tare da miqa hannu ya karbeta ya zauna ya zuba mata idanu yanajin wani tausayin kansa da Habeey da Kuma yar tasu da yake fatan ta zame masa raba gardama ko kamar da yarinyar takeyi da Mom dinsa ya isa yasa zuciyar Mom tayi sanyi tabarsa ya auri Habeey dinsa.
Da wadannan tunane tunanen Granny ta matso ta kalli yarinyar tace “masha Allah Lele kamar kumbo kamar katanta ga tukuicin sabawa ubangiji nan ka samu sai kayita kallonta a matsayin yar zina..." Ji yayi qirjinsa ya buga yace “Granny don Allah kada ki qara fadamin haka nifa banson a dangantamin yata da laifin dana aikata ba ita tayiba"

Karbarta likitan yayi yace “muna buqatar jini uwar ta zubar da jini sosai zaa daura mata" miqewa yayi yace “zaa iya diba a jikina jininmu iri dayane"
Dakin da zaikai babyn ya shiga yayi Mata abinda ya dace sannan ya dawo suka nufi Lab suka debi jinin nasa duk da haka saida aka nemi qarin leda daya aka siya aka sanya mata.
Ranar a asibitin dukkansu suka kwana saida asuba Granny tace yaje ya nemo musu kayan amfani ya kawo musu, aikuwa taga hauka kaya kamar zasu bude shago ya kawo musu lkcn da aka fito da kayan fada Granny ta farayi tace maza ya rage yakai gda aiba dawwama zasuyi a asibitin ba.

Zama ya nemi  guri yayi yace “saidai ki rabar bazasu koma ba gdanma akwai ukun wadannan" bata qara cewa komai ba ta koma ta zauna tare da kiran wayar governor Waziri.
Tun jiya yake Kiran wayar Taheer yaqi dagawa ganin kiran mahaifiyar tasa yasashi dagawa da sauri zuciyarsa na bugawa saboda tunanin ko meyene dalilin Kiran da safe haka.
Sallama yayi mata tace “lfy Lau Wazir ka fadawa Safinah Habeebah budurwar Taheer ta haifi ya mace me kama da ita yanzu haka muna tare anan azare..." Wata firgita Alh Waziri yayi yace “what Inna haihuwa kuma? Wai dama da gaske yaron nan yakeyi ciki yayiwa yarinyar nan haba Inna ya zakiyimin haka don Allah ya zaayi ki daurewa yaron nan gindi yaci gaba da iskancinsa kina gani fah tun jiya da mukayi masa mgnr sa ranar aurenss da Saudat ya fice bai sake waiwayenmu ba kiran duniya yaqi dagawa qarshe ma yasa uwarsa a blacklist haba Hajiya wannan ai zubar mana da qimane da mutunci, kamarni ace....."

Katseshi tayi da cewa “koma mene aikin gama ya gama Taheer yayiwa budurwarsa ciki ya kawomin ita gata a hannuna kuma dama ai tarbiyyarku ce hakan abinda yaranku sukeso shi zakuyi musu saboda haka shima ku barshi da abinda yakeso sannan qaddarar yaya tanakan kowa itama ba haks iyayenta sukaso ba rubutun tawadar ubangijine sai ta hadu dashi sunyi wannan abin kunyar"
Kashe wayarta tayi ta karbi babyn a hannun Taheer dake shigowa ya zauna yana kallonta tana goge mata jikinta tana shafa Mata zaitun tare da tofa Mata addu'o'i a jikinta tasa mata Pampers ta sanya Mata kayan sanyi tace “kayi mata huduba kuwa?" Girgiza kai yayi ta Kuma cewa “saboda me?" Bude runannun idanunsa yayi yace “na rasa sunan da zansa Mata  Granny” murmushi tayi tace “kasa Mata Safinatul Najah" da sauri ya dago yace “sunan Mom?" Daga masa kai tayi tace “eh akwai ma'ana a cikin hakan"

Ajiyar zuciya yayi ya karbeta yayi mata hudubar yanajin qaunar yarinyar tana mamaye duk wani gurbi da qaunar uwarta ta rage a zuciyarsa dagowa yayi yace “tun ranar da na fara bata rayuwar Habeeytah Allah ya jarabceni da qaunarta har inajin kamar mutuwa zanyi idan ban aureta ba Granny nasani Habeey batasona saboda tana kallona kallon mafi munin qaddararta don Allah ki shigemin gaba muyi aure da ita badon kaina ba saidon maslahar rayuwarmu dukkanmu da ta Safnah"
Mamakine da tausayinsa ya cika zuciyar Granny ta dafashi ya dago kansa kawai sai taga hawaye yana shatata a idonsa tace “subhanallahi Lele meye kuma abin kukan a cikin wannan lamarin mutum ko yaqi Allah ai bazaice maka aa ba saidai babbar matsalar shine daidatawar yarinyar nan da mahaifanta"
Share hawayen yayi ya miqe ya matsa gaban gadon da take yace “ban damu da kowa yaso tarayyata da Habeey ba burina kawai itan ta amince dani ta daina yimin kallon da takeyi min Granny inason Habeeytah nini kadai na dace da zama mijinta saboda nine silar kowacce irin lalacewa tata"..........
#*UMMUH HAIRAN*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 01, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DUBAIWhere stories live. Discover now