4.Pleaseth

146 25 16
                                    

💠💠💠💠💠
©®2020.

                   *♡MAKTOUB¸.•💥*
                   ((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6

🆓 Pᴀɢᴇ..

🅿»4⃣:#Pʟᴇᴀsᴇᴛʜ

       *It seems like baku yi appreciating zuwan book d'inba 😕 saboda yadda kuke ignoring,anyways duk yadda kuka yi dai² ne thanks all for da love,this is the right time dama da akace zan fahimci true lovers d'ina,wato na maida book paid shisa duk kuna kallo babu wanda zai iya comment sai kad'an daga ciki,groups d'ina kam dama ku ba'a saka ku lissafi,wannan sabon kune ayi abu baza ku tanka ba,billah i feel ashamed on u,kun yi matuk'ar ba ni mamaki,sai dai ba zan ce komai ba,wad'anda suka min fatan alkhairi da addu'o'i,i have nothing to pay u back,thank u so much habibtiiys,ILYSM.😘 Wattpadians hala kunyi bacci? I see no vote fa,why ne? Idan babu chanji gaskiya 😢 zan koma posting whatsapp kad'ai tunda haka kuke so.*

💕

      Yayi murmushi yana lumshe idanunsa a hankali yace "Later za ki sani" b'ata fuska tayi tana hararar gefenta tace "ni dai a'a ka fad'a yanzun" ya sake yin murmushi then a hankali yace "yeah! Na iya kad'an" tayi murmushi tace "Nima na iya shuwai²" yayi murmushi a hankali cike da mutuwar da jikinsa yayi yace "sai an jima?" Ta kad'a kai kamar tana gabansa tace "Allah ya kaimu" yace "ayi karatu lafiya" tayi murmushi tace "thanks" ya lumshe idanunsa a hankali yana relaxing kansa a saman bed yace "alright! Bye" tace "bye" sai suka ajiye wayar tare,juyi ta sake yi ta mirgina,tana sakin murmushi aka bud'e k'ofa da k'arfi har sai da ta tsorata ta juyo,idanunta suka sauka kan Badriyah da ta shigo tana hawaye,cikin tsoro Ismat tayi sauri ta tashi a firgice ta rik'ota tana kallonta hankalinta duk ya tashi ta fara magana "what happened habibtiiy? What's wrong with u? Me aka miki please?" Kuka Badriyah ta fashe da ta zauna saman bed,da sauri Ismat tayi kneeling a gabanta idanunta sunyi rau² kamar za ta fashe da kuka duk ta birkice tace "please talk to me dear,waye ya tab'a ki? Ke da waye please?" Badriyah ta kasa magana sai kuka take,jikin Ismat ya fara tsuma da sauri ta d'auki wayarta hannunta banda rawa babu abunda yake yi ta fara kiran line Jawahir,mintuna biyu Jawahir ta d'auka da fad'in "Hello dear!" A firgice Ismat ta furta "Yaa Jawahir me aka ma habibtiiy take kuka?" Jawahir ta fara dariya tace "Me kuwa za ayi mata? Kema kin san halin mutuniyar ki ai" hurriedly Ismat tace "please Yaa Jawahir ki sanar min abunda akayi,kinga fa kuka take tunda ta shigo" bud'a hannu Jawahir tayi tace "tou ni dai ban san me aka yi mata ba,amma ki tambayi Yaa Barraq ko da shi ne suka samu matsala" Ismat ta zaro ido a tsorace tace "tare suka zo?" Jawahir tace "Ehhh!" Ismat tace "Alright! Sai an jima" Jawahir bata gama amsawa ba Ismat ta katse kiran,Jawahir tayi murmushi ta bi wayar da kallo kafin ta ajiye ta fita,juyowa Ismat tayi tana kallon Badriyah da har lokacin ta k'i yin shiru tace "please habibtiiy wani abu ya had'a ki da Bhai?" Banza Badriyah ta mata kamar bata ji ta ba,ta sake maimaitawa for da second time tana tunanin Badriyah za ta amsa mata,but sai taga ta k'i cewa komai,hankalin Ismat duk ya dad'a tashi,sai kallon Badriyah take kamar za tayi kuka tace "shi kenan tunda ba za ki fad'a ba,amma kin san idan kin ci gaba da kuka kanki zai yi ciwo kou?" Ta fad'a tana k'ok'arin sharewa Badriyah fuska,still Badriyah bata kalleta ba tana ci gaba da sauke hawaye kuma ta k'i cewa komai,kasa samun nutsuwa Ismat tayi a hankali ta sake d'aukan wayarta ta fara kiran line Bhai d'inta,dai² lokacin shigowarsa kenan cikin gidan ya d'an tsaya compound wajen mai wankin sa da ya kawo masa kaya,yana jin wayar yana ring ya wuce bai d'auka ba sai da ya kai kayan bedroom ya ajiye saman resting chair,ya fito da wayar daga pocket yana dubawa yaga Kid sis ce ta kira,a hankali yayi calling nata back,cikin azama Ismat dake juya waya a hannunta tun d'azun da ta kira taji bai d'auka ba tayi answering call d'in da fad'in "Bhai me ka yiwa habibtiiy take kuka please?" Had'e rai yayi yace "ita tace miki na yi mata wani abu?" Ta kad'a kai a hankali kamar tana gabansa tace "No! I'm just asking" yace "Ban sani ba,dama kiran da kike yi kenan?" Ta marairaice fuska tace "Bhai ka ga fa tunda ta shigo take kuka,kuma har yanzun bata bari ba" kafin ta sake magana ya katse kiran yana jan tsaki,a fili ya furta "shirme",waistband ya rik'e yana tsaye a inda yake sai ya rasa me zai yi? Because kiran wayar ya mantar da shi abunda yake niyyar yi,a hankali ya juya ya fara k'arewa room d'insan kallo,ya sake yin tsaki sai kuma ya juya ya nufi hanyar fita,da sassarfa ya dunga tsallake staircases yana zuwa corridor ya tsaya k'ofar bedroom d'insu yayi knocking,Ismat dake tsugune gaban Badriyah kamar mai neman alfarma tace "Yes!" Barraq ya turo k'ofar yana had'e rai ya shigo da sallama,Ismat kad'ai ta amsa tana kallonsa kamar za ta fashe da kuka,ya k'araso yana kallon Badriyah dake share hawaye a dake yace "Me aka yi miki kike ma mutane kuka? Ko dan ban zane ki ba?" Saurin d'agowa tayi sai kuma ta sake fashewa da kuka "Hey! Hey!!" Ya fad'a da wani irin murya a fusace yana nufarta,jikin Badriyah ya fara rawa saboda ta tsorata ta fara ja baya,sai da ta kai k'arshen bed sannan ta fara magana da muryar kuka "Ni dan Allah ka rabu da ni,kawai sai ayi min abu kuma ace bazan ji haushi ba?" Wani kallo ya fara watsa mata cikin hayaniya yace "uban me aka miki?" Ta sake fashewa da kuka tace "tou ba a gabanka tayi min ba?" Matsowa ya fara yi gashin jikinsa sun fara mik'ewa yana kallonta yace "Idan kika sake bakinki ya sake furta wani magana a nan gurin sai na b'arar miki da hak'ora,ke sha³r ina ne? Jawahir ba gaba take da ke ba? Ohoo! Da kika ga ban zane ki gaban Mama ba,ban yi miki maganar abunda kika yi ba shi ne kika samu bakin magana yanzun wai wani anyi miki abu baza ki nuna fushi ba,tou nuna fushin naki mu ga!" Ya k'are maganar cikin tsawa,saurin rik'e arm d'insa Ismat tayi cikin rawar murya ta furta "I'm sorry bhai,please forgive her" sai tayi saurin had'e hannayenta tana rok'onsa hawaye suna sauka kan fuskarta,saurin kallonta yayi yana making snapped muryarsa cike da warning yace "Ki rufe min bakinki a nan wajen kema,ko na ce kiyi magana?" Da sauri ta kad'a kai,ya juya a fusace yana kallon Badriyah "saboda kin iya rashin kunya shi yasa ba kya ganin kowa da mutunci,kowa kin maida shi sa'anki,yaushe kika zama haka? Nawa shekarunki suke duka?" Saurin d'agowa tayi tana tura baki,a fusace ya kad'a mata hannu cike da gargad'i ya furta "mind u! Idan kika bari naji wani kalma ya fito daga bakinki za kisha mamaki na yanzun" tura baki ta sake yi ta fara k'unk'uni k'asa² sam bata tab'a zaton zai ji ba tace "tou ba ita ta tsokane ni ba?" Gigitaccen marin da ya falla mata lokacin yasa bata tantance inda take ba sai da ta d'auki wasu sa'o'i sannan ta dawo dai²,cikin masifa Barraq yana nuna ta with his index finger ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,sai da yayi mata tas² then ya juya a fusace zai fita,a guje Ismat ta bishi tana ba shi hak'uri bai kulata ba har suka sakko k'asa lokacin Mom tana zaune parlor tana magana a waya,tunda suka fara tahowa take kallon su har suka sakko za su wuce,da sauri tace "za muyi magana later,ina da wani d'an uzuri da ya taso min na gaggawa yanzun" sai ta katse kiran,lokaci d'aya ta furta "Hey! Duka ku zo nan" a tare suka juya jin muryarta because duk basu san tana zaune ba,Ismat tana share hawaye a hankali ta fara wucewa kusa da Mom then Barraq dake had'e rai,suna zuwa ya zauna kad'an saman wani armchair ya k'i yarda su had'a ido da Mom,but kallo d'aya za ka yi masa ka san ransa a mugun b'ace yake saboda yadda yake tauna hak'ora kamar zai ci babu,yadda nerves d'in kansa suka yi rad'a² kamar za su tsaga goshinsa su fito,Mom ta kalleshi ta kalli Ismat a hankali ta furta "Maza ina saurarenku ku sanar da ni abunda yake faruwa" saurin kallon Barraq Ismat tayi,ya kautar da kansa bai kalleta ba yace "nothing Mom" Mom ta kalli Ismat tace "me ya had'a ku?" Kai Ismat ta fara girgizawa then tace "ba da ni bane Mom" wara ido Mom tayi da sauri tace "ban gane ba? Idan ba ke bace waye? Me kika yi nace?" Kallonsa ta sake yi then ta sake cewa "Mom ba ni bace fa,shi da habibtiiy ne,ni hak'uri kad'ai nake basa" "habibtiiy?" Mom ta tambaya da mamaki,Ismat ta gyad'a kai tace "Ehhh" da mamaki sosai akan fuskar Mom tana bin staircases da kallo tace "when ta dawo gidan?" Ismat tace "yanzun babu jimawa",juyawa Mom tayi tana kallon Barraq ranta a b'ace tace "didn't i told u of what's right? Me kake son zama Barraq? Babban kwabo ko me? Kana so yaran nan su raina ka kou?" Saurin kallonta yayi yana marairaicewa yace "Mom ba fa yadda kike tunani bane,laifi tayi ban hukunta ta ba kuma ta zo tana yiwa mutane kukan banza" wani kallo Mom tayi masa tace "laifi kace?" Ya kad'a kai yace "sure Mom" ta kad'a kai tana kallonsa tace "wane laifi ne tayi maka? Yarinyar da ina kula wakenku sam bai nuna tukunya d'aya? K'aramar yarinya ka maida ni da za kace min ta yi maka laifi na yarda? Yaushe ma kuka zauna waje d'aya ban sani ba har tayi maka laifin?" Ismat ta d'ago a hankali ta saci kallon Barraq yadda taga yayi shiru ya kasa tankawa Mom ita kuma sai fad'a take masa a gabanta al'halin bata san abunda ma ya faru ba,da sauri a wani irin sanyaye tace "but Mom kada kiyi hukunci da abunda baki sani ba,tare suka je can fa" a fusace Mom ta juyo kan Ismat tace "how dare u told me tare suka je?" A sad'ad'e Ismat tana sunkuyar da kai tace "I just know" Mom tana yi mata wani kallo tace "saboda tare kuka je da su?" Ajiyar zuciya Ismat tayi tana lumshe idanu tace "A'a Mom munyi waya da Yaa Jawahir ita tace sunje tare" kallonta Mom ta dunga yi ta kasa magana,kusan mintuna uku then tace "je ki kawo min wayar muga" a hankali ta tashi ta fara tafiya,har ta d'anyi nisa da fara haura stairs d'in Mom ta daga muryarta tace "ku zo tare da Badriyah" ta amsa a hankali ta wuce bedroom d'insu da niyyar aiwatar da umarnin Mom,tana shigowa ta tarar da Badriyah ta fito daga bathroom fuskarta da alamun danshin ruwa,ta wuce ta fara d'aukar wayarta then tace "kizo Mom tana kiranki" saurin kallonta Badriyah tayi tace "Okay" suka wuce tare Ismat a gaba tana binta har suka sauko k'asan,tunda ta hango Barraq dama taji gabanta ya fad'i a hankali wani irin tsoronsa ya dunga shiga jikinta,sai tayi saurin sunkuyar da kai,bata yarda ta sake d'agowa ba har suka k'araso,Mom tana kallon fuskarta da yayi jaa ta gefe tace "come here dear" tana mik'a mata hannu,saurin tahowa tayi ta kwanta jikin Mom a hankali Mom ta zubawa fuskarta idanu tana kallo tana shafa gurin tace "me ya same ki a nan nake ga kamar shatin hannu?" Hawaye suka kawo idanunta a hankali tana tura baki tace "Yaa Barraq ne ya mare ni" saurin kallonsa Mom tayi cikin fushi tace "Kana hauka Barraq za ka fidda hannu k'aton namiji kamarka da ko wani namijin ka daka sai ka ji masa ciwo ka mareta,laifin me tayi maka kasa hannu ka daketa eh?" Sunkuyar da kai yayi a hankali yana sassauta murya yace "I'm sorry Mom but it's not intentional" a fusace Mom tace "it's not intentional kake cewa? Ni kake fad'a ma haka? Hauka kake za ka mareta? Gaskiya na gaji Barraq da sa ni maganar da kake daga jiya zuwa yau,ni dai ka tattara ka koma bakin aikinka Allah ba mu alkhairi" saurin kallon mahaifiyarsa yayi jin tana cewa ta gaji da ganinsa kusa da ita,kamar zai fashe da kuka yana ci gaba da kallonta yace "but Mom" a fusace tace "but what? Me kake da shi da za ka fad'a min na saurareka?" Saurin kallon Ismat yayi yaga itama fuskarta duk ta yi rau² kamar za ta fashe da kuka,a hankali ya sauke kansa k'asa yace "shi kenan Mom zan tafi gobe in Allah ya kaimu,ki yi hak'uri in sha Allah bazan sake ba" yadda yayi maganar cikin sanyin murya yasa Ismat jin wani irin tausayinsa a hankali ta share hawayen da suka zubo mata ta kalli Mom tana tura baki tace "but Mom bafa ki san me tayi ba kike masa fad'a kuma" juyowa Mom tayi kanta cikin fushi tace "kina son tare masa ne saboda na yi magana? Ko kuwa dan ba ke ya yiwa marin ba?" Sunkuyar da kai tayi a hankali tace "A'a Mom but kin sani ba'a hukunci da abunda aka ji ko aka gani daga tsagi d'aya hakan yana iya zama kamar rashin adalci ne wa d'aya tsagin,and duk gaskiyar da ake nema idan aka yi hukunci da abunda aka ji na gefe d'aya kin sani Mom baza'a tab'a gane komai ba" still Mom tayi tana kallonta,tabbas maganarta gaskiya ne,but ita ta san duk baza su fahimci dalilinta nayin haka ba,ta san wace ce Badriyah fiye da kowa kasancewar rayuwarta kusan duka a gidan yake,tun tana zuwa yi musu hutu lokacin tana yarinya har duka zamanta ya dawo gidan,kusan za ta iya cewa a halayen Badriyah tabbas ta san 75% wanda ko uwar da ta haifeta ba lallai ne ta sani ba,dole take dakatar da Barraq a wasu lokutan,because idan tana zuba ido zafin zuciyarsa zai iya sawa wata rana ya ji mata ciwo ita kuma abunda ba ta fata kenan ya faru,gyad'a kai tayi tana kallon Ismat tace "ko mene ne tayi masa bai kamata yayi mata irin wannan marin ba,duba yadda shatin hannunsa suka kwanta mata a fuska" Ismat ta d'ago tace "tou Mom ba zai sake ba ai in sha Allah ya fad'a fa" harararta Mom tayi tace "rufawa mutane baki,ke ni ban san me yake damunki ba k'iri² kina kallon abunda yayi kin san gaskiya amma sai wani support kike basa" murmushi ne ya kufce mata tana satan kallon Badriyah tace "tou Mom ai kin san itama habibtiiy ba jin magana take ba,kika sani ma ko wani abu yaga tana yi in appropriate to her behavior?" Harara Mom ta sake sakar mata tace "za ki rufe min baki a nan ko sai na b'ata miki rai?" K'ifta idanu tayi da sauri ta rik'e bakinta da hannu tace "I'm sorry Mom na yi shiru Allah,but ki tambayeta ta fad'i abunda tayi ya mareta muji idan itace da gaskiya dama za mu bata hak'uri" juyowa Badriyah tayi saurin yi a fusace jin abunda Ismat take fad'a tace "ban gane na fad'i abunda nayi ya mare ni ba?" Ismat ta d'aga kai a hankali tana kallonta tace "Ehhh! Ki fad'a muji idan ba laifi kika masa ba me yasa zai doke ki tou?" Had'e rai tayi cikin borin kunya ta fara ihu da fad'in "baza'a fad'a ba d'in,kawai dan kinga yana yayanki shi ne za ki zab'esa ki bashi gaskiya,ai na gane abunda kike nufi" dariya Ismat ta fara yi tana kallon yada Badriyah take yi tana k'ik'k'ifta idanu alamun rashin gaskiya k'arara a fuskarta strictly tace "Kin gani kou Mom Allah ba ta da gaskiya,ki tambayeta gata muji abunda tayi" a tsawace Badriyah ta mik'e tana yi mata wani kallo tace "Kinga Ismat ba na son haka,meye ruwanki a cikin maganar ma duka?" Ismat da dama halinsu d'aya da Jawahir gurin dariya ta dunga dariya tana kallon Badriyah har saida hakan yasa Badriyah ta sake k'ulewa,Barraq da har lokacin yake zaune bai ce da Mom ga abunda tayi masa ya mareta ba shi kansa sai da abunda Ismat take yi mata yasa shi yin murmushin da bai yi niyya ba,Badriyah kuwa dama da ta gama k'ulewa cikin fushi ta fashe da kuka,tana kallon Ismat dake tsagaitawa da dariya tace "tunda kin zab'esa akai na dama yau ba sai gobe ba zan yi tafiyata,sai kije kiyi ta zama alone,zan bar muku gidan kuyi ta zama ke da shi" tana fad'a ta juya za ta wuce sama da niyyar ta tattare belongings d'inta tayi wucewar ta gida a cewarta,Mom tayi saurin rik'o ta tace "haba habibtiiy me yasa za kice haka?" Ismat ta d'age shoulders tana tab'e baki alamun bata damu ba tace "Mom let her be please,maza ki gaida gida" a firgice Badriyah ta waiwayo jin abunda Ismat tace tana kallonta because bata tab'a expecting such a words za su iya fitowa daga bakin Ismat d'inba all because of bold relationship da take hangowa tsakaninsu tace "kika ce me?" Strictly Ismat tace "cewa nayi ki gaida gida,kou kina ga bazan iya zama ba a gidan mu idan kin tafi?" Yadda tayi furucin tana d'an zare idanu yasa duka su uku suka bita da wani kallon mamakin anya Ismat ce da gaske take fad'in haka ko kuma dai mafarki suke? Because kamar yadda suka yarda kuma suka sani abu ne mai wahalar gaske ace kalaman daga bakinta suka fito,sun san alak'ar dake tsakanin su biyun sun kuma san yaya ne matsayin Badriyah a zuciyar Ismat,tambayar farko da yazo wa duka su ukun shi ne "Mene ne ya zo cikin tunanin Ismat lokaci d'aya har ta iya fad'in idan ta rabu da Badriyah baza ta ji damuwa ba?" Jikin Badriyah banda tsuma babu abunda yake yi tana sake bin Ismat da kallon mamaki tace "kin san abunda bakin ki yake cewa Ismat? Do u really know of what ur mouth said? Kina cikin hayyacinki kika ce hakan?" Ismat tayi murmushi tana lumshe idanuwa tace "of course ina cikin hayyacina nace haka" ba Badriyah kad'ai ba hatta Mom ta ji matuk'ar mamaki da irin kalaman suka iya fitowa daga bakin Ismat but ta kasa samun confidence tayi magana,gyad'a kai Badriyah tayi a hankali tana yiwa Ismat wani irin kallon da na kasa tantance na mene ne,then da sassarfa ta juya ta wuce sama tana fashewa da kuka,tana barin gurin tunanin Mom ya dawo daga yajin aikin da yaje,tana kallon Ismat da mugun mamaki tace "Sweetheart! What really come over ur head? Kin san me kika ce da y'ar uwarki kuwa?" D'aga kai tayi tace "na sani Mom,barta muga idan za ta iya tafiya d'in" Mom tayi still tana kallon Ismat da mamaki but couldn't talk sai kallon da take yi mata duk inda tayi,Ismat tayi murmushi a hankali ta waiwaya gurin da Barraq yake tayi masa murmushi a hankali ta nufesa,saman hannun chair ta d'an zauna tana rik'e hannunsa duka tace "kayi hak'uri bhai da abunda tayi,ni dai na san ba za ka daketa ba idan bata yi maka laifi ba dama,but please i'm begging u daga yau ka daina saurin fushi,kaga ba shi da kyau,kuma ka sani Annabi (S.A.W) ya hana mu yin hukunci a cikin fushi" wani irin sanyi yaji kalaman Ismat sun saukar masa,a hankali yana kallon k'anwarsa da shekaru rututu suke tsakaninsa da ita yayi murmushi yace "in sha Allah kid sis zanyi k'ok'ari na daina,thanks for the reminder,i love u" murmushin jin dad'i tayi wanda ya bayyana hak'oranta tace "I love u too bhai,but please ka daure kana yiwa Mom bayani idan ta tambayeka abu,ka ga yanzun ni na san Badriyah ba ta da gaskiya,amma da ka yi shiru kaga Mom kai ta yiwa fad'a ba ita ba,please bhai kaga bai kamata ace ana yi maka fad'a a gabanmu ba,tunda kai Yaya ne,amma idan kayi bayani kaga babu wanda zai na ganin laifinka kou?" Sanyayyan murmushi yayi yana lumshe mata idanu a hankali yace "thank u dear" tayi dariya kad'an a hankali tace "tou ka fad'awa Mom yanzun abunda tayi,tunda ita bata san rufa mata asiri ma kayi ba" saurin kallonta yayi yace "ya akayi kika sani?" Tayi murmushi tana kallon Mom dake kallonsu ta kasa cewa komai tace "ban sani ba kawai fad'a nayi,because na san halin bhai na ba ya tab'a yin abu babu dalili,and habibtiiy too,na fi kowa sanin halinta because ni nake rayuwa tare da ita" kad'a kai yayi a hankali yayi murmushi yace "No! Dear ba sai na fad'a ba,tunda kin fahimci banyi da wani niyyar ba haka ma ya wadatar" zuba masa idanunta tayi a hankali kuma ta d'age girorinta duka tace "Ok! Tunda ka zab'i haka shi kenan,but ka yi min alk'awari idan ta sake baza ka sake b'oyewa ba za ka fad'a?" da sauri yace "promise bazan sake ba" dariya tayi ta dunk'ule hannunta a hankaali ta fara matsawa da shi tace "let's have this deal" da sauri ya kawo hannu suka had'a sai suka yarfe yatsu a tare,Ismat tayi dariya tana yin ihun murna,a hankali Barraq ya waiwaya yana sakin murmushi ya kalli Mom da ta zuba musu idanu,sai ya sake yin murmushi ya tashi yana fad'in "Let me go dear,ya kamata na fara shirin tafiya" saurin kallonsa tayi tana ware idanu tace "ina kuma za kaje bhai?" Da sauri ya waiwayo yana kallon direction d'in Mom yace "Baki ji Mom ta ce ta gaji da gani na ba?" Zaro idanu tayi tana kallon Mom kamar za ta fashe da kuka tace "Ni dai gaskiya kada ka tafi sai ka gama hutunka,ai naga itama dan bata san gaskiyar abunda ya faru bane tace hakan" zaro ido yayi yace "No dear gara na shirya na tafi tunda ta ce" kallon Mom Ismat ta dunga yi kamar za ta d'ora hannu a ka ta fasa k'ara a shagwab'e tace "please Mom ni dai ban so ya tafi gaskiya" saurin kallonta Mom tayi ta harareta a fusace kuma sai tace "tunda ba kya so sai ki tattara ki bisa can lagos d'in" zaro idanu tayi tana kallon Mom a shagwab'e ta tashi taje jikinta ta fad'a tana sakin kuka tace "ni dai Mom kiyi hak'uri abunda idan ya tafi sai ya jima zai sake zuwa kuma" Mom dake sauraron tab'arar Ismat babu shiri ta ture kanta daga jikinta tace "tashi ki wuce ki bani guri kafin na sab'a miki" saurin mik'ewa tayi tana kallon Mom hawaye suna sauko mata ta turo baki tace "Mom ni ce fa autar ki" yadda tayi maganar cike sa tab'ara ya masifar bawa Mom dariya,a hankali ta kad'a kai ta kamota ta kwantar a jikinta tana cewa......

      #Za kuga VIP ya canja,saboda masu recharge ne,anyi min maganar babu card na ₦50.

   #The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦500.

*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*

*1-ACCOUNT DETAILS.*

Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.

*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609*

*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*

08165726609

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

*3- OTHER WORLD REMITS*

Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.

       For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.

          

   
#Share pls.
#Asli Smasher.

MAKTOUBWhere stories live. Discover now