12.In-laws

122 19 7
                                    

💠💠💠💠💠
©®2020.

                   *♡MAKTOUB¸.•💥*
                   ((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/K6BGdPZvW8

🆓 Pᴀɢᴇ..

🅿»1⃣2⃣:#Iɴ-ʟᴀᴡs

     _Ban yi niyyar k'arasa labarin ba,ban yi niyyar fad'a kowa yaji ba,na so ace baku yi maganar ba kuma,damuwa da maganar ci gaban littafin *MAKTOUB* yasa kuka ji asalin abunda ya faru,kun had'a ni da wanda ba zan iya wofintar da buk'atar ku ba,but har ga Allah idan aka sake min irin haka sai dai kuma wani labarin idan Allah ya nufa zan sake rubutu amma banda wannan kuma,sam da yawan mutane basu iya magana ba,ni bance dole ne kowa ya karanta ba,abun nan ra'ayi ne idan kuna iyawa ku bi,if not kuma ku barmin abu na,as i said zan sake maimaitawa,idan gyara kika gani ki nemi number na muyi magana,ba na son wannan rainin hankalin,idan aka kuma min haka na rantse da sarkin da rayuwata take hannunsa duk yadda muke da mutum zan ajiye alak'ar mu gefe,duk ma wace ce ko waye billah zan yi muku abunda baku tab'a tunani ba,ku baku san mutumin da yake kauda kai akan al'amuranku ba,duk hakur'in sa idan ba zage² yayi ba bakwa gane yana jin haushi,shin mu ba-mu da zuciya a cikin kirjinmu ne? Ko kuwa dai waliyyai ne mu da baza mu nuna bacin rai ba? Wannan ya zama na k'arshe,duk mai gyara ya bini PC,Allah duk wacce ta sake min irin wannan rainin hankalin da sunan gyara na rantse da Allah za ta sha mamakina ranar,ina da hak'uri sosai,ina kuma karb'ar duk wani gyaran da za ku min,ban tab'a wulak'anta kowa ba,idan kina ganin kin yiwa wasu gyara ko kin musu magana basu yi responding ba wannan ra'ayinsu ne,tsarinsu daban na-wa daban,but ba na d'aukar cin mutunci,Allah bai wulak'anta ni ba ke/ku baku isa kumin ba,saboda haka a kiyaye,wannan ya wuce,Allah kyauta na gaba._

💕
   
       Murmushi Fawad yayi yace "sister mu how are u?" Badriyah ta zaro ido tana kallon Ismat dake dariya k'asa² tana k'unshe baki kada sound ya fita,a hankali ta sake sassauta murya tace "Waye sister ku kuma? It's me fa!" Dariya yayi yace "I think u guy's sai dai kuyi wasa da hankalin wani amma ba nawa ba" Badriyah ta fashe da dariya tana sakin muryarta zuwa asalin yadda take magana tace "ya akayi kasan ba ita bace?" Yace "since kika yi answering call" ta kad'a kai tana kallon Ismat data zuba mata manyan idanunta tace "Ni dai gaskiya ban yarda ba" yayi murmushi yace "why?" Tace "Duk yadda nayi magana da irin muryarta ace ka yi saurin ganewa,ba fa yau muka fara yima mutane haka ba" yace "Mmm! Su ma mutanen da kuke yiwa think suna da matsalar fahimta,but idan ba haka ba duk mutumin da ka sani ai zaiyi wahala ka kasa gane wani abu na-sa" Badriyah dake dariya ta kad'a kai cike da gamsuwa tace "haka ne,but ni dai sai ka fad'a min ya akayi ka gane kai?" Murmushi yayi strictly yace "duk lokacin da na kira sallama take yi min,that's how na fahimci ba ita tayi answering ba" Badriyah tace "that's good,kenan dai kana iya gane komai na ta yanzun?" Yayi murmushi mai sauti yace "sure!" Ta gyad'a kai tana yin murmushi MSI sauti,Fawad da yayi shiru kad'an yana sauraren Badriyah jin bata ce mssa ga Ismat d'in ba a hankali yace "where's she?" Tana ci gaba da kallon Ismat data koma ta kwanta a hankali ganin ba ta da niyyar ba ta wayar tace "Tana bacci" ta k'are maganar cike da zolaya,bud'a idanu sosai yayi kamar ya ji tsoro yace "bacci tun yanzun? Dare ai baiyi nisa ba" tayi murmushi tace "just kidding! Ga ta kusa,let me give her" ya lumshe idanunsa a hankali yace "alright! Thanks",Badriyah tana fad'in haka tayi masa sallama ta fara mik'awa Ismat waya tace "Take please sweetheart" bud'e idanu Ismat tayi a hankali ta karb'i wayar tana yiwa Badriyah murmushi,ta kai wayar kunnenta cikin cool voice d'inta tayi masa sallama,ya amsa yana sakin ajiyar zuciya,a hankali tace "ina yini?" Ya amsa "lafiya k'alau,ya gajiyar biki?" Tana sake adjusting kanta zuwa yanayin kwanciya tace "an gode Allah" yace "kin je rakiyar amaryar ne?" Tace "sure" ya kad'a kai yana lumshe idanuwa yace "but ya akayi ban ganki ba?" Saurin bud'e idanu tayi tace "kaima ka je ne?" Yayi murmushi yace "Munje rakiyar ango yanzun babu jimawa" a hankali tana sakin murmushi tace "Mun taho da wuri mu,because k'afafuna sun fara min ciwo" yayi shiru yana saurarenta har ta kai k'arshe,maganarsa a sanyaye yace "Kina ciwon kafa ne dama?" A tak'aice tace "Ehh!" Ya sassauta muryarsa zuwa yanayin damuwa yace "Doctor fa,kin tab'a zuwa kin gansa kan matsalar?" Tace "Ehh!" Yace "Mene ne yace akan ciwon k'afar?" Tace "he said babu komai it's just an arthritis" yace "babu wani matsalar bayan nan?" Ta gyad'a kai kamar tana gabansa tace "Ehh!" A sanyaye yace "Allah k'ara lafiya" tace "ameen" yace "kiyi taking drugs sai ki kwanta kou da safe za muyi waya!" A hankali tace "na yi ai" yace "Alright! Ki kwanta ki huta tou" Tayi shiru bata ce komai ba sai sauraronsa da take yi,cike da kasala da wannan cool voice d'insan yace "sai da safe?" Tayi ajiyar zuciya a hankali tace "Ehh" a sanyaye da wani irin murya yace "Okay! Sleep tight" murmushi tayi tana jin kamar za ta nutse cikin bed tace "thanks" yayi murmushi jin a yadda ta amsa yace "bye" ta kasa amsawa sai murmushin da take yi,yayi murmushi shima a hankali kamar ba ya son sake yin magana yace "kina son cewa wani abu ne?" Ta gyad'a kai a hankali tace "not at all" yace "ok then?" Ta bud'e idanunta half a hankali da muryar rad'a tace "bye" tana fad'a ta cire wayar a kunnenta ta fara katse kiran,tana d'agowa fuskarta d'auke da wani irin murmushi idanunta suka sauka kan Badriyah da tayi tagumi ta zuba mata idanu ko k'iftawa ba ta yi,ta k'ifta idanunta a hankali ta waiwaya sides kamar mai neman abu,ta sake juyowa taga still ita Badriyah ke kallo,tayi murmushi a hankali tayi waving hannunta a kusa da fuskar Badriyah,murmushi Badriyah ta saki da ya bayyana hak'oranta tace "Wai kina tunanin mene ne?" Ismat tace "kina duniyar tunani mana" tayi dariya tace "Um'um! Ni ba na irin wannan tunanin" tab'e baki Ismat tayi tace "ke d'in?" Badriyah tayi dariya tace "Yap!" Ismat dake komawa ta kwanta tana lumshe idanu tace "please habibtiiy ki d'an sake min massaging k'afafuna" dariya Badriyah ta fara tace "sai dai ki kirasa yayi miki,ni bacci zanyi yanzu" daga kwancen Ismat take kallon Badriyah a hankali tace "Pleaseee!" Tana sake reducing girman idanunta saboda ta samu shawo kan Badriyah tayi mata messaging,Badriyah ta kyalkyale da dariya ta kwanta kusa da ita tana jan spreadsheet,da sauri Ismat ta rik'e kamar za ta yi kuka tace "Pleasee habibtiiy! Kad'an fa za kiyi min" saurin juyawa d'ayan side Badriyah tayi tana rufe idanu tace "ba na sa miki magani ba,ki kwanta za su daina" Ismat dake kallon Badriyah idanunta sunyi rau² tace "shi kenan tunda baza kiyi min ba,dama na san kin daina so na" tana fad'in haka ta juyawa Badriyah baya,dariya Badriyah ta fara kafin da sauri ta tashi tana kallon Ismat da ta ba-ta baya tace "Kin manta!" Ismat ta waigo tana kallon Badriyah fuskarta da alamun tambaya tace "what's it?" Murgud'a baki Badriyah tayi tace "ban sani ba" Ismat ta tab'e baki ta juya tana fad'in "kada ki sani d'in" Badriyah tace "ai dama bazan sani ba" k'wafa Ismat tayi bata sake cewa komai ba,tana jin Badriyah tana dariya ta k'i yarda ta sake kulata a haka bacci ya d'auke su duka sun juyawa juna baya.

MAKTOUBWhere stories live. Discover now