5.Accidentally

147 19 6
                                    

💠💠💠💠💠
©®2020.


                   *♡MAKTOUB¸.•💥*
                   ((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6

     *For u brothers (ATK's) 😍 Kaka's HASSAN ATK & HUSSAIN 80K😜,thanks for the care and support..Ahabbakum-kthiir.♥*

      *I'm really appreciated JAMILA UMAR (JANAFTY)😘,thank u so much habibtiiy,son so fisabilillah.❤*

🆓 Pᴀɢᴇ..

🅿»5⃣:#Aᴄᴄɪᴅᴇɴᴛᴀʟʟʏ

       A hankali ta kad'a kai ta kamota ta kwantar a jikinta tana cewa "I know ke ce auta,but u know abunda bhai d'in kin nan yake yi a times suna b'ata min rai kou?" Saurin kallon Mom Ismat tayi a hankali tace "but Mom babu fa abunda yayi,he just want mun yi abunda ya dace ne,and he's right akan duk action d'in da zai d'auka,idan ba haka ba Mom rayuwarmu zai iya fad'awa a had'ari,mu d'in mata ne dole muna buk'atar wanda zai tallafi rayuwarmu,dole ne sai ana tsawatar mana muke iya bambance tsakanin right da wrong" shiru Mom tayi ta zubawa Ismat idanu tana sauraron jawabinta,ita kanta ta sani maganganun da Ismat take fad'a gaskiya ne,abunda take fad'a mata right away kamar wani gyara ne ma take yi mata a matsayinta na mahaifiyarsu,wanda a wasu lokutan tana yawan ganin laifin Barraq idan yayi wani abun more especially akan Badriyah,Ismat tace "kinga Mom idan bhai bai yi mana gyara ba a nan waye muke da shi matsayin wa da zai gyara mana?" Shiru Mom tayi ta kasa cewa komai,Barraq kam dama since ya mik'e bai koma ya zauna ba,but duk maganar da Ismat take yi fes a kunnensa yana tsaye inda ta barshi,b'angare d'aya na zuciyarsa d'auke da wani irin cheerful expression da hatta fuskarsa sai da ya bayyanar da hakan ya ci gaba da saurarenta yana kallonsu,while gefe guda kuma yake d'auke da wani irin mamakin yadda akayi Ismat take saurin fahimtar duk wani manufarsa akansu amma Mom ta kasa ganowa,tabbas hankali ba shi ne shekaru ba,hankali baiwa ne ubangiji yana iya halittar yaro k'arami sai yayi masa baiwa da hankalin da idan yayi wani abu mutane za suyi ta mamaki,haka idan yayi niyya sai yayi babba mara hankali mutane suyi ta masa kallon sha³ idan yayi wani abun,komai na rayuwa baiwa ne ubangiji yana bawa wanda ya so a lokacin da ya so,sannan ya hana wanda yaso a lokacin da ya so,a hankali Barraq ya juya yana sakin murmushin samun nasara ya kallesu,bai ce komai ba ya fara tafiya a hankali yana jinjina kaifin tunani irin na k'anwarsa,har ya kusa barin gurin Mom tace "Barraq" tayi calling sunansa out,tsayawa ya fara yi a inda yake then ya waiwayo,yaga kallonsa Mom take yi a hankali tace "me za kayi yanzun?" D'an jim yayi yana kallonta then ya d'an yi wearing fuskar damuwa yace "zan fara shirin komawa ne Mom as u said" kad'a kai tayi kad'an tana lumshe idanu then tace "Babu buk'atar sai ka koma yanzun,ka bari ka k'arasa holiday d'inka" murmushi ya saki yana kallon Mom yayi blinking idanu a hankali yace "thank u Mom" tayi murmushi itama daga haka bata sake cewa komai ba,ya juya yana kallon Ismat yayi murmushi ya d'aga mata hannu alamun thumbs up,tayi y'ar dariya kad'an da sauri ta sake rungume Mom tana ihun murna tace "thank u Mom,i love u" tayi pecking cheek d'inta,Mom tayi dariya tana shafa kanta dake jikinta tace "love u alf marra roohii" murmushi Ismat ta dunga yi tana jikin Mom daga nan suka fara hira sama² Ismat tace "Mom yaushe Daddy yace zai dawo?" Shiru Mom tayi tana murmushi tace "Ni ai bai fad'amin zai dawo ba ma" zaro ido Ismat tayi tace "Kai Mom har kema bai fad'a miki ba? Ni dai gaskiya ya dawo i miss him badly" dariya Mom tayi ganin yadda Ismat take b'ata rai ta ja tip noise d'inta tace "kwantar da hankalinki,next week ma zuwa yanzun ya dawo" ihun murna ta fasa sai ta tashi ta fara rawa tana cewa "Yay! Daddy will soon back home" tana tafa hannuwa kamar wacce ke kid'a tana rawa,Mom dake kallonta banda dariya babu abunda take yi tace "ke dai yarinyar nan ba ki da kunya a gabana kika tsaya kina rawa?" Saurin dakatawa tayi ta juya tana dariya ta nufi hanyar staircases tace "na tafi karatu Mom" Mom ta zaro ido tace "dama karatu za kiyi kenan kika tsaya kina rawa?" A gurguje tace "Ehhh Mom,but rawan ma ai kinga ya sani nishad'i,zanyi karatu yanzun babu damuwar komai a raina" Mom tayi murmushi tace "yayi miki kyau,yarinya kamar wata bayerabiya sam ba ta da kunya" ta tsaya daga karshen stairs d'in tana dariya tace "Ai Mom baki ga rawa na ba,wani abun ma sai auren Yaa Jawahir,hoo! Za mu kwashi rawa ni da habibtiiy" Mom ta kad'a kai tace "Allah bada sa'a,ni dama kada kizo kice min ga wani guri yana miki ciwo" dariya tayi da sauri ta juya tace "babu abunda za'ayi Mom",daga haka ta bud'e bedroom ta shiga.

MAKTOUBWhere stories live. Discover now