💠💠💠💠💠
©®2020.*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6🆓 Pᴀɢᴇ..
🅿»7⃣:#Bᴀsᴋᴇᴛʙᴀʟʟɪɴɢ
Kusan a tare motar Aadil da na Fawad suka shigo compound d'in gidan,but Aadil ne a gaba then Fawad,yana gama gyara parking ya bud'e motar,a nutse ya juya d'aukan jakar laptop d'insa da wayoyinsa dake seat d'in mai zaman banza,Fawad ya k'araso yana yi masa wani irin kallo yace "Ina ka shiga yau baka je office ba?" Sai da ya gama tattara belongings d'insa tsaf ya d'ago,a hankali kamar ba zai yi magana ba da farkon yana rufe motar a tak'aice yace "BUK!" Kallonsa Fawad yayi da mamaki a fuskarsa yace "Me kaje yi can?" Yana gama locking motar ya fara tafiya a nutse ya furta "Daddy ya sani zuwa na karb'i Aakiiy" Fawad ya fara biyo bayansa yace "When akayi hakan?" Bai damu da tsayawa ba yana tafiya zuwa hanyar flat d'insu yace "It was yesterday" Fawad ya gyad'a kai a hankali bai sake cewa komai ba,suna shiga parlor Aadil ya zube all his belongings saman table ya wuce bedroom,zaunawa Fawad yayi saman armchair yana zube wayoyinsa shima da car keys d'insa,a hankali kuma sai yayi relaxing kansa saman armchair yana mik'a because ya yi mugun gajiya,shi kad'ai yaje hospital yau duk wasu ayyuka da meetings kuma da suka taso shi ya jagoranta tunda baiga Aadil d'in bama bare suyi 50².
Almost 35 minutes da shigar Aadil bedroom ya fito sanye da bathrobe bak'i wanda yayi masifar k'ara fito da hasken fatarsa ya sake bayyana shi matsayin kyakykyawa ajin farko,cikin takunsa na zaratan maza mai tattare da nutsuwa yana k'arasowa bai kalli inda Fawad yake ba ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa ya fara making call,in less than 3 minutes aka d'auka,idanunsa a lumshe yana matsa forehead d'insa da hannun hagunsa,cikin wani cool voice ya furta "please help and make some coffee,ki kawo yanzun" d'an jim yayi then ya cire wayar daga kunnensa ya ajiye,ya juya ya koma bedroom,lokacin da yake fitowa bayan ya shirya cikin k'ananun kaya,polo t-shirt ne sanye a jikinsa da trouser white sai d'an adon bak'i kad'an a jiki da aka yi rubutu,sumar kansa gwanin sha'awa ya sha gyara kamar ba'a saka masa ruwa,bai gama zaunawa ba aka yi knocking door,a hankali yace "Come in" turo k'ofar akayi a hankali da wani siririn murya aka furta "Assalamu alaikum" ya amsa bai damu ya kalli gurin ba,farar kyakykyawar k'afarta ta fara saukewa cikin parlor'n then a hankali ta shigo tana d'an waigawa ganin bata ga mutum ba,kyakykyawar matashiya ce wacce duka a shekaru da wuya ta k'arasa su Ismat sai wara manyan idanunta take yi,tasowa yayi daga cikin chair da ya nutse ganin bata k'araso ba a hankali yace "Ba ni nan" saurin kallon direction d'insa da taji maganarsa tayi sai kuma tayi murmushi ta fara takowa hannunta rik'e da medium tray na silver,samansa da flask da cups biyu because ta san yana wahala ace shi kad'ai ne,kamar yadda tayi tunani kuwa ta gansu taren dama ta sani yadda suke kamar twins kullum suna manne da juna,tun yarintarsu ma da Mami take bada labari d'aya baya rabuwa da d'aya shi yasa komai nasu tare suke yinsa,yanzun ne da girma ya fara zuwa aka fara samun wasu changes suka fara intervene tsakaninsu,saman table ta ajiye a hankali tace "Masa'al khair Akhiiy" yana lumshe idanunsa ya furta "Kaiifak?" Da yar siriruwar maganarta tace "Alhamdulillah" ya sauke numfashi kad'an yana d'aukan cup,da sauri ta d'auka tace "let me help",ajiyewa yayi ya koma baya,ta matso a hankali ta d'auki cup d'in ta sunkuya tana zubawa,Fawad ya bud'e idanunsa yana tashi zaune,da sauri ta bud'e idanu tace "Akhiiy! Dama ba bacci kake ba?" Yayi mata murmushi a hankali yace "Yeah! Yau nayi stressing kaina da yawa shi yasa" ta yi murmushi kad'an tace "Good evening" yace "Evening,how are u?" Tace "Alhamdulillah! Ya aiki?" Lumshe ido Aadil yayi yana karb'ar cup da take mik'o masa a hankali cikin rashin son magana yace "U can now leave" d'an bud'a ido tayi za tayi magana ya bud'e shanyayyun gray eyes d'insa ya zuba mata su,da sauri ta tashi tana tura baki ta fara tafiya,tana daf za ta fita Fawad ya kalleta yana sakin murmushi yace *"NAINA!"* A hankali ta waiwayo bata amsa ba,yace "Mami ta dawo?" Tace "Ehh! Tana tare da Daddy ma" yace "Alright!" Juyawa tayi ta fara tafiya Aadil ya bita da kallo har ta fita,a hankali ya d'an tab'e baki ya fara shan coffee.
YOU ARE READING
MAKTOUB
Historical FictionNowadays,the words "betrayal" and "deception" is more effective than anything else in the life of humanity... Ya ya za kiji a lokacin da kika bud'a ido kika tarar mutanen da kika amincewa fiye da kowa,kika d'auke su kika kaisu wani matsayi,har...