15.Interval

278 23 13
                                    

💠💠💠💠💠
©®2020.



                   *♡MAKTOUB¸.•💥*
                   ((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))


*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/K6BGdPZvW8

*LAST FREE PAGE.🏃*

🅿»1⃣5⃣:#Iɴᴛᴇʀᴠᴀʟ

      Wani irin shiru parlon ya d'auka na musamman,tsakanin su Daddy an rasa samun mai magana sai kallon-kallo da ake maimaita yi tsakanin su da family'n Fawad da suka zo neman auren,can da aka jima Dr Haroun mahaifin Badriyah yayi k'arfin hali yana sauke wani irin ajiyar zuciya ya furta "Anya kuwa maganar nan haka yake? Mu dai duka nan abunda muka sani da wanda aka sanar damu maganar neman auren *ISMAT* ne ya zaunar da mu,yanzun kuma munji kun zo mana da wani batun daban,me haka yake nufi kenan?" Maganar da Dr Haroun yayi a lokacin yasa mutane sake yin shiru da farko,but daga bayan kuma here musu ya kaure tsakanin families d'in biyu,yayin da family'n Fawad ke ganin ba dai² su Abbah suke fad'a ba,suma suna ganin sune a kan dai²,su dai b'angaren Fawad da suka zo meman aure ne suka yi ba dai² ba,all because su basu san wani batun Badriyah ba na Ismat suka sani,ganin haka yasa Proff Junayd da tun zuwansu bai ce komai ba numfasawa yayi magana "I think ya kamata tunda abun nan yazo da jayayya tsakanin mu,me zai hana baza'a kira yaron aji daga bakinsa ba,gudun kada muyi abu kai tsaye,kou kuwa me kuke gani?!" Yana fad'in haka duka hankalin kowa sai ya karkata kan ayi hakan,here mahaifin Fawad Engineer Dawoud ya d'aga waya kafin ma ace Proff d'in yayi nufin hakan ya kira shi yasa wayar a free yadda kowa zai ji me yake fad'a,Fawad dake zaune cikin parlor ya mik'e k'afafu a saman table hannunsa rik'e da remote yana powering TV kiran mahaifin nasa ya shigo masa,ya d'aga wayar yana kallon sunan da ke yawo kan screen d'in a hankali ya lumshe idanunsa yana sakin murmushi ya kai wayar kunnensa,before yayi magana Eng. Dawoud d'in ya fara magana "Fawad! Kana ji na?" Fawad da ya rufe idanu murmushi kwance saman fuskarsa ya amsa "Ehh! Abbuh" Eng yace "ina so ka fad'a min wace ce ka tura mu neman maka aurenta yanzun?" Shiru ya fara yi na wani d'an lokaci,hak'oransa a waje yana sakin murmushi because he made sure dole za'ayi hakan kafin ya furta "Abbuh! Ni fa *BADRIYAH* nace muku sunanta,wani abu ya faru?" Ya k'are maganar kamar bai san me ya haddasa ba,Eng na jin Fawad yace haka ya furta "Alright!" Kafin Fawad ya sake magana har ya katse kiran,wani irin gumi ne suka fara ketowa jikin Barraq tun da yaji maganar da Fawad yayi a waya,ransa a mugun b'ace muscles d'insa sunyi rad'a² kamar za su tsaga jikinsa,idanun san nan lokaci d'aya suka birkice suka sauya colour,banda tauna tooth d'insa kamar zai ci babu idan ya gani babu a bunda yake,haka su Daddy ma duk sunyi shiru sun kasa cewa komai,tsananin mamaki yasa sai maimaita abunda kunnuwansu suka ji suke but sun kasa zartar da ko wane irin hukunci,Egn da ya gama magana da Fawad a waya ya juyo yana numfasawa ya furta "hope duka kunji abunda ya faru,and kun fahimci inda maganar yake yanzun?" Abbah ne ya d'ago a zafafe zai yi magana da sauri Daddy ya rik'e gefen rigarsa ya hanashi abunda yayi niyya,Daddy dake sakin murmushin k'arfin hali yana girgiza kai yace "Haka ne mun fahimta kam yanzun,think mun samu tangard'a ne wajen fahimta saboda mu da aka bamu maganar ba'a bambance mana ba,but tsakanin Ismat da Badriyah duka d'aya ne,babu matsala in sha Allah" tunda Daddy ya fara maganar Barraq ya kafe shi da kallo with his coloured eyes,tun d'azun da yaji an ambaci Badriyah zuciyarsa ta tunzuro,and duka burinsa shu ne ya gansa a gida sai dai babu halin yin hakan because bai isa barin wajen ba,but jin maganar Daddy na kusan k'arshe yasa shi zabura yayi mik'ewar da bai yi niyya ba,da sauri Daddy ya kai hannu zai rik'osa,kafin ya kai ga yin hakan tuni Barraq ya nufi k'ofa yana tafe yayi taking excuse,within seconds har ya fice,Daddy hankalinsa a mugun tashe ya bishi da kallo,ba ya so yayi magana bak'in su suyi wani zargin shi yasa kawai ya rabu da Barraq d'in,but ya fi kowa sanin halin Barraq a yadda ya fita d'in nan dole ya san za'a samu matsala,addu'ar sa a lokacin bai wuce Allah ya tsare Barraq d'in ya isa gida lafiya ba,shi kansa Abbah bai so aka ce d'an uwansan ya yi saurin zartar da hukunci ba,idan a son ransa ne so yayi su hana neman auren kawai but ba zai iya jayayya da Yayan nasa ba,dole ya hak'ura yayi shiru a gurin but underneath ji yake kamar ana boiling masa zuciyarsa,jira kad'ai yake yayi ido hud'u da Badriyah yaji abunda yake faruwa tsakaninta da yaron because bai yarda da abunda ya faru ba yanzun,dole there's something behind,har aka kammala maganganu Proff ya bada sadaki suka ajiye maganar akan za su fara tuntub'ar Fawad suji lokacin da ya yanke Dr Haroun bai san me suke cewa a kan maganar ba,sai da suka fara sallama da su Proff Junayd za su tafi,su Daddy kad'ai suka yi musu rakiya aka rabu cikin mutunci kamar yadda aka had'u.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 02, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MAKTOUBWhere stories live. Discover now