💠💠💠💠💠
©®2020.*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6🆓 Pᴀɢᴇ..
🅿»9⃣:#Nᴇɢᴀᴛɪᴠᴇ ᴇᴍᴏᴛɪᴏɴᴀʟ
Wani irin lumshe idanu yayi a hankali ya sake bud'e idanunsa ya sauke su akanta,fuskarsa d'auke da kinda beautiful smile,idanunsa sun d'an yi wani irin sauyawa na lokaci d'aya yana kallonta ya sake mata hannu,hawayen bak'in ciki da suka kawo idanunta suka gangaro saman fuskarta a guje,duk kuma ita ba komai ya fi b'ata mata rai ba a lokacin sama da yadda yake jifanta da murmushi,sosai abun ya k'untatawa zuciyarta,tana kallonsa da wani irin b'acin rai a cikin idanunta bata iya cewa komai ba hurriedly ta juya za ta bar wajen hannayenta rik'e da gown d'inta data tattare,ta tsinto asalin muryarsa cikin wannan cool voice d'in san da ta sani yana fad'in "Thanks dear!" Wani irin k'amewa Ismat tayi a gurin kamar wacce aka yi pausing,jin muryar da ko cikin taron arfa ta had'u da mai shi baza ta tab'a iya mantawa da shi ba a cikin kunnuwanta da kwakwalwarta yana mata yawo,a rikice ta waigo tana yi masa wani irin surprised look hawaye suna ci gaba da saukowa saman fuskarta,ya sake yi mata murmushi a karo na babu adadi,a hankali ba tare da ya sake yin magana ba daga haka ya juya ya fara tafiya.
Aadil dake zaune cikin mota tun d'azun after ya gama yiwa su Naina lik'i yana jiran Fawad ya fito su wuce gida,kamar ance ya d'ago daga nan inda yake zaune cikin mota,his illuminated eyes suka sauka kan Fawad dake rik'e da hannun yarinyar da Naina tasa suka gaisa not too long,wani irin fad'uwa yaji gabansa yana yi sakamakon abunda ya gani a hankali ya zuba musu idanunsa,babu zato yana kallonsu da wani irin yanayin da ya kasa gane na mene ne kawai yaga yarinyar ta fallawa Fawad mari,abunda ya faru akan idanunsa lokaci d'aya ya matuk'ar girgiza shi,sai dai bai san ma lokacin da wani irin smirk ya kufce masa ba,ya sake lumshe idanunsa ya bud'e ya ci gaba da kallonsu cikin wani irin yanayin da ya kasa rarrabewa farin ciki yake ko damuwa? Gani yayi Fawad ya yi murmushi then a hankali ya sake mata hannu,abun da ya faru ya mugun bawa Aadil mamaki ya d'aure masa kai,but bai gama mamaki ba sai da yaga lokaci d'aya yarinyar da take niyyar fara gudu,saboda a yadda ta tattare riga kana kallo za ka san a shirye take ta k'arawa k'afafunta sauri,kawai sai yaga ta yi wani irin juyawa tana kallon Fawad d'in da fuskar mamaki hawaye suna sauka kan fuskarta,bud'a idanu ya sake yi sosai yana kallonsu gabansa sai fad'uwa yake,still a nutsen yaga Fawad ya sake yi mata murmushi bai yi magana ba ya fara tahowa wajen motar da yake ciki. Aadil couldn't stop looking at them har lokacin da Fawad ya bud'e motar ya shiga side na mai zaman banza,ya waiwaya continue looking at him lokacin yana kwantar da kansa jikin seat had'e da lumshe idanunsa ya kasa magana,almost 5minutes yana kallonsa then ya sake juyawa ya kalli inda take,har lokacin tana nan yadda Fawad ya barta rik'e da gown d'inta ta kasa tafiya,Aadil dai mamaki duk ya hana masa tada motar su tafi,sai da Fawad ya d'ago a hankali yana tura hular kansa baya yace "Muje mana,tsaiwar me muke yi kuma?" Tab'e baki Aadil yayi a nutse ya d'auke kai ya tada motar ya fara riding,sun d'auki hanyar komawa gida motar yayi wani irin shiru,though dama hakan ba sabon abu bane a gurinsu,a nutse Aadil ya katse shirun ta hanyar watsowa Fawad tambayar "Me ya had'a ku?" Lumsassun idanunsa Fawad ya bud'e a hankali,kamar ba zai yi magana ba da farko ya dunga kallon Aadil then a hankali yace "Nothing" Aadil ya waiwayo ya kalleshi kad'an yace "Haka kawai ta mare ka kenan?" Saurin bud'a idanu Fawad yayi yace "Na fad'a maka babu komai" Aadil yayi murmushi yace "Akwai abunda kake b'oyewa my friend" a d'an fusace Fawad dake kallon waje yace "Tunda ka sani mene ne abun tambaya?" D'age eyebrows Aadil yayi a hankali ya tab'e baki yace "Saboda ina son sani" siririn tsaki Fawad ya saki then kamar ba ya son cewa komai ya fara sanar da Aadil d'in alak'arsa da Ismat,Aadil dake driven lokacin suna tsayawa dai² get d'in gidansu ya dunga kallon Fawad da wani irin mamaki,but bai ce komai ba yayi horn malam Jibrilla ya bud'e masa get,yana riding motar zuwa cikin compound d'in gidan,a hankali kamar ba ya son magana yace "U made a mistake!" Saurin kallonsa Fawad yayi yana bud'a idanu yace "Mistake wane iri?" Aadil yana gyara parking a carline yace "Me yasa za ka rik'e mata hannu daga had'uwar ku?" Shiru fawad yayi yana kallosa,Aadil yace "U know! Kai ba muharraminta bane right? Besides baku had'a ko wane irin alak'a na jini ba,hasalima baku tab'a ganin juna ba,on ur own speculation nake so ka fad'a min,me ya kamata kayi a had'uwar ku na farko wanda zai bawa alak'ar ku damar d'orewa? Me kake tunanin ita za ta d'auki abunda ya faru tsakanin ku yanzun? Daga had'uwa ka rike mata hannu,duk wacce ta san mutuncin kanta yaya za ta d'auki al'amarin,and then mene ne ya kamata tayi wanda zai ba ta kariya,mutane ba za suyi zarginta ba a matsayin y'a mace da aka ga namiji ya rik'e?" Wani irin kallo Fawad ya dunga yi masa,sai dai ya kasa magana,a hankali Aadil ya bud'e motar yana fita yace "A nawa ganin bata yi ba dai² ba dan ta yi haka,saboda haka kada ma ka fara ganin laifinta because ta yi abunda ya dace a matsayinta na mace da bata tab'a saninka ba!" Fitowa Fawad yayi ya kasa magana har lokacin sai kalaman Aadil dake masa yawo a cikin kai,daga haka babu wanda ya sake magana suka fara tafiya zuwa flat d'insu.
YOU ARE READING
MAKTOUB
Historical FictionNowadays,the words "betrayal" and "deception" is more effective than anything else in the life of humanity... Ya ya za kiji a lokacin da kika bud'a ido kika tarar mutanen da kika amincewa fiye da kowa,kika d'auke su kika kaisu wani matsayi,har...