💧💧 *SILAR WAYE..?*
( _FITATTU BIYAR..🌹_)©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers.*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm.*UWATA ABUN ALFAHARINA HAFSAT SALISU BASO! DA KUMA GWAGGO TA TA KAINA AMINA SADA RADDAH, ALHERIN ALLAH YA TABBATA A GAREKU TARE DA DUKKANIN ZURI'AR SADA ABDU RADDAH! ALLAH YA ALBARKA CE KU BAKU D'AYA, YA KUMA HASKAKA RAYUWARKU🌹..!*
*GAISUWARKU DABAN TAKE DA TA KOWA, MOMMA (XOXO), UMMI AISHA, AYUSHER MOHD, AUNTY HAJJA CE, K'AWATA SLIMZY, DA DUKKAN Y'AN K'UNGIYAR HASKE💡.*
*HAKA KUMA KARAMCINKI DABAN NE SISTER FATIMA MAROK'I💞*
*INA KIKE HALIMATOU TA? WATA K'YIL SAI NACE HAJIYAR LONGRICH SANNAN KI AMSA! NA GAISHEKI K'YAUTA BAIWAR ALLAH🌹..!*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI.*
_Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talakai, wanda ya bani damar fara rubuta wannan littafin lafiya ya kuma ara mani lokaci da rayuwa Allah na gode maka! kura kuran da zamu rubuta Ubangiji ya yafe mana, darasin dake ciki Allah ya bamu ikon amfani dashi._!_Ban rubuta wannan littafin domin cin zafari ko take hak'k'in wani ko wata ba! Kamar yadda nake fad'a babu ruwana da kowa duk abunda yayi dai dai sa rayuwarka ko ta wani na kusa da kai ka dauka hakan na faruwa a ko'ina, ban sanka ba! Ban sanki ba! Ba labarinki bane! K'irk'ira ce._
*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR_🌹*
*01*
***Tunda ta doso layin gidanmu zuciyata ta gama tsinkewa da lamarinta yayin da zuciyata ta cigaba da harbawa da k'arfi da k'arfi na kalli Dafta a sanyaye had'e da sakar mashi murmushin yak'e wanda ya fi kuka ciwo yayin da ya mayar mani da martani yana fad'in "Kin k'i bani dama in turo ko *Hindutah* ? Idan nayi magana kice sai Ubangida ya dawo alhalin ke kanki baki san lokacin dawowar tashi ba, kuma ai ga tsoho nan yayansa ne zai iya yin komai a madadinsa, ni dai a taimaka man in turo iyayena."
Na rausayar da kai ina kallon Gwaggon mu da ta shigo zauren idonta k'yar a kanshi tana faman kiran "Dafta! Dafta..!!"
Ya sosa k'eya cike da kunya yana sunne kai, a hankali yace "Mama ina wuni.?
" Lahiya lau Dafta, ya allurai da magani.? Ta tambaya har lokacin idonta k'yar saman fuskarshi bata ko k'yaftawa."
A sanyaye yace "Alhamdulillah."
Kai tsaye ta kuma fad'in "Dafta kai dai har yanzu bakayi wayon rik'o bak'ar leda ba idan ka tashi zuwa tad'i sai dai ka zo tsinkai tsinkai daga kai sai biro a aljihu! Ni bansan uwar da kake rubuta mata ba.!"
Ba shi ba hatta ni sai da naji kamar na nutse k'asa don kunya, gashi ta kuma k'i kawar da idonta daga gareshi, sai binshi take da kallo sama da k'asa.
A hankali yayi k'asa da kanshi ba tare da yace komai ba domin idan da sabo yaci ya saba da rashin mutuncin gwaggota.
Na kalleta na b'ata fuska ina turo baki cike da takaicinta, yayin da ta zabga mani harara ta kuma cigaba da fad'in "Kai bur wallahi, ace mutun baisan ungo ba, sai dai a heso turare a mak'alo biro a aljihu a zo a cika mana zaure da k'arairayin banza, d'an tsiran d'ari uku ya gagara a taho ma budurwa dashi saboda jarababben mak'o irin na y'an boko! Ni kam na gaji da tsayuwar banza aradun Allah." Ta watsa hannu baya had'e da furzar da dusar goron dake bakinta.
Kamar inyi kuka nace "Haba gwaggo dan girman Allah meye haka kike yi? wallahi yana bani ni ce bana k'arba."
Ta zabga mani harara tana fad'in " Dallah rufe mani baki makauniyar arziki! Samna da bata san ciwon kanta ba, ana neman k'wato maki y'anci kina neman bad'a mani k'asa a ido."