💧💧 *SILAR WAYE..?*
©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm.*015*
***Zuciya ta ce ta tambaye ni, shin ina zan je? Kai tsaye na amsa da in shiga duniya, wata ƙyil na samu rangwamen rayuwa, yayin da wani sashe ya gargaɗe, shin idan na shiga duniya me zan taras? Ta iya yiyuwa in taras da abunda ya fi nan muni, na sanya bayan hannu na share hawayen dake malala daga ƙwayar idona..
Banda inda na ya wuce ƙauyen mu alkhairi a tattare dani, don haka na nufi tasha na nemi alfarma da ƙyar aka kai ni har garin birchi, sannan na samu machine da ya ƙarasa da ni ƙauyen mu, saboda babu ɗan machine ɗin da bai sanni ba, tunda na shiga ƙauyen mutane ke nuna ni suna kallo na ko wanne da abunda yake saƙawa a ranshi, har na shiga gidan mu na taras da Gwaggo zaune bisa tabarma tana bakacen gero, zaro ido tayi tana kallona a firgice yadda ka san ta ga abun tsaro, kafin ta rafka wani bahaggon salati tana faɗin n "Na shige su! Me zan gani Hinde? Lahiya kika dawo? Kar dai ace bai same ki budurwa bane suka koro ki? Ni dama nayi zargin haka, tun naga kina zuwa asibiti a sace gurin Dafta na san ba zai rasa lagude ki ba."
Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya tokare mani maƙoshi, sai naji me yasa na nufo nan ma? Me yasa ban ɗauki shawarar shiga duniya ba? Ji bi kalaman da mahaifiyata ke faɗa, na ɗaure bance komai ba na faɗa ɗaki, na ƙwanta bisa katifa sai lokacin idanu na suka fara fidda ƙwalla, ta hankaɗo labule ta faɗo duk ta birkice tana ƙara tambaya ta" Wai lafiya na ganki Hinde? Koroki suka yi.?
Kai tsaye nace "Lafiya, da kaina na taho, don bazan iya zama dasu ba Gwaggo, wallahi mugaye ne, basu da imani."
Ta ce "Sannu annab Hinde! Shugaban masu imani, to wallahi ƙarya kike! Gafara tashi maza in maida ke tun kafin na ƙwashi ƙwal ubanki, shashasha wacce bata san arziki ba. "
Na fashe da kuka na shiga sanar mata duk abunda ya faru, tun daga zuwa na gidan har taho wa ta, ban ɓoye mata komai ba, har fyaɗen rashin mutunci da Farouku tayi mani, sannan na ƙara mata da cewa Farouk ɗan uwan Aliyu ne Daftan da ta sani! Ta rufa mani asiri ta kashe auran nan ba zan zama dashi ba.
Ai kamar na ƙara tunzura ta, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, ta shiga auna mani zagi, da alkaba'ai sannan ta fincike ni ta dauki hijabinta, ina kuka ina haɗata da girman Allah amma bata saurareni ba, haka muka koma gidansu Farouku, yayin da nayi na damar zuwa ƙauyen namu, na ji me yasa ban shiga duniya ba? Me yasa na koma gida.?
Ashe dawowar tawa tana tare da musiba kala da kala.
Gwaggo ta maido ni har falon Mamy ta shiga bata hakuri kamar zata yi mata sujada..
Da ƙyar Mamy ta amince suka amshe ni, tare da kashedi mai zafi akan duk ranar da na ƙara komawa gidan, to zata saka a ɗaure iyayena, saboda su ne suka daure mani gindin da nake guduwa daga gidan mijina..
Gwaggo tace "Hakan ma ba zai ƙara faruwa ba, ayi Hakuri a yafe mata, sannan dan Allah Mamy ina roƙan alfarma da ya daina dukanta, duka Hinde nawa take da zai shirge ta? A dai tausashe shi Mamy."
Kai tsaye Mamy tace "Sai ki faɗa ma ƴar ki idan tana ƙarfin rama wa, ya doke ta to ta ɗaga hannu ta rama, ba zan damu ba, amma ba zan hana Farouku hukunta matar shi ba, muddun tayi mashi rashin kunya." Ita kanta ta faɗi haka ne saboda ta san babu yadda za ayi in rama duka gurin Farouku, sai ma in ƙara ja ma kaina masifa, domin ko kaɗan ƙarfin mu ba ɗaya ba.
Gwaggo ta zaro ido waje tana faɗin " Ina ita ina rama wa? Ai sai dai ta haƙura.!
Mamy ta ce "Better..!