💧💧 *SILAR WAYE..?*
©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm.*013*
***Na a daɗe zaune ina tufƙa da warwara, sannan na tashi a sanyaye na cire hijab ɗina tare da tura ƙofar ɗakin na rufe sannan na cire kayan jikina na ɗaura ɗanƙwalin na faɗa makewayi na silla wanka, na fito babu ko mai da zan shafa haka na mayar da kayan da na cire na koma ina leƙen taga da na ga babu kowa a haraba gidan sai na dawo gefen katifar na ƙwantar da kaina ina shiga rera kuka babu ƙaƙƙautawa.
Har ƙarfe sha ɗayan safe ina ƙwance a ɗaki ina kuka, babu wanda ya ƙara leƙo ni bare na yi tunani za'a ce in yi shiru, ga wata azabbar yunwa dake nuƙurƙusa ta, rabon da in ce naci abinci wadatacce tun kafin maganar wannan auren ta kankamata, na shafa cikina a hankali tare da lumshe ido, ƴan guntayen hawayen dake maƙale suka silalo, Allah ya sani ina tausayin kaina na irin wahalallar rayuwar da zanyi a cikin wannan baƙin gidan! Kuma ba kowa ya janyo mani ba sai Gwaggo da Ubangida.
Aliyunah ya faɗo mani a rai, masoyi na na haƙiƙa, sai dai ban san me yasa ya tafi ya barni a lokacin da nake tsaka da buƙatar sa ba? Yaushe zai dawo? Ban sani ba, sai dai ina ji ajikina komai daran daɗewa zai dawo gare ni, mu yi aure, mu yi rayuwa cikin farin ciki, mu haifi zuri'a masu kama dashi..Ba kuma zan taɓa ɗaga ƙafa ba ko na ƙwana ɗaya, zan haukace masu ko ta halin ƙaƙa ne dole in rabu da Farouk, in koma ga muradi na! Idan ban manta ba ai Gwaggo tace ko sati biyu ne inyi in fito, to ba sati biyu kaɗai ba, zan iya jurewa har zuwa lokacin da Aliyu nah zai bayyana...!
Wani nannauyan baccin wahala yayi awon a gaba dani, ban jima ba na soma mafarkin wasu baƙaƙen tsuntsaye suna tsatstsagar tsakiyar kaina, yayin da nasa hannu na kore su amma sai suka sauya halitta zuwa baƙaƙen raƙuma suka soma bina a guje, ihu nake ina gudu bakin raina amma sai da suka cimmani, suka fara zagaye ni, yayin da suka tashi daga raƙuma suka koma wasu baƙaƙen halittu suna wata irin mahaukaciyar dariya.
Ihu na ƙwallah na tashi firgigit ina share jiɓin da ya jiƙa mani hijabi, na yaye hijabin na yar a ƙasa, gabana na dakan uku uku domin ji nake har lokacin waɗannan halittun basu daina bina ba, sannan duk sa'adda dana runtse ido su nake gani suna ƙyalƙyala dariya..
"Ya Allah...! Na faɗa a sanyaye tare da raka tagumi, Allah ya sani ban taɓa irin wannan mummunan mafarkin ba, asali ma na kan share fiye da shekara ba tare da nayi mafarki ba, Meye dalilin wannan mafarkin.? Ban sani ba..
Delu ta faɗo ɗakin kamar an jehota, na zabura na ja baya a firgice ina kallon ta, da na tabbatar ita ɗin ce wani sanyi ya ratsa zuciya ta, yayin da tsoron yayi ƙaura a tattare da ni domin ko ba komai ƴar ƙauyen mu ce kuma na santa ta san ni don haka ganin nata ba ƙaramin daɗi yayi mani ba, cikin zaƙuwa na ce "Innarsu Sabi'u ashe kina nan.?
Ta washe baki tana faɗin"Ina nan mana Hinde, da ina zani.?
Na jijjiga kai, ina share gumi.
A hankali tace" Lahiya ƴar amana? Jiɓin me kike.?
Nayi rau rau da ido, banyi niyyar faɗi mata ba, amma ban san lokacin da na ce" Mummunan mafarki nayi yanzu wallahi, wasu halittu na bina zasu kashe ni."
Ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin" Na shige su! Dama na san za'a rina."
Na zaro ido ina tambayar ta" Me ya faru.?
Ta ce "Yo sharrin su amarya mana Hinde? Ai shine ke bibiyarki, sun ga arziki da ƙafafun shi ba gurgu ba! Kar ki damu zan faɗa ma Tatu idan na koma, dole ta miƙe tsaye idan ba haka ba sai dai ta ganki kin koma gida."