02

97 9 0
                                    

💧💧 *SILAR WAYE..?*
              ( _FITATTU BIYAR🌹_)

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
    Wattpad@Feedohm.

*INA KIKE JAMILA UMAR? JANAF! ALHERIN ALLAH YA TABBATA GAREKI DA KUMA ZURI'ARKI BAKI D'AYA..*

*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR🌹_*

*02*

  *KATSINA SAHARA SUITES.*

     ***D'aki mai lamba 103! Gurin yayi tsit baka jin sautin komai sai nishin mutane dake cikin d'akin mace da namiji suna k'wance bisa makeken gado yayin da suka lullub'e ilahirin jikinsu kaf blanket fari k'yal.

Cikin wata irin sigar y'ar budurwa tace "Marry me boy..!"

Bai bata amsa ba wayarsa k'arama company tecno keypad dake gefen pillow ta hau ruri, don haka ya yaye bargon ya fiddo da kanshi waje had'e da d'auko wayar yana dubawa, ganin wanda ke kiranshi ya saka shi mik'ewa zaune da azama tare da sakata a speaker ya d'aura bisa cinyarsa yana fad'in "Hello Oga! Good evening."

Daga d'ayan bangaren aka amsa da "Evening Boy, kana ina yanzu.?

Ya kalli Alina da ta fiddo kanta waje tana kallonshi fuskarta d'auke da wani shu'umin murmushi, ya mayar mata da martani sannan yace " Muna tare da Alina d'iyar Alhaji Sa'id a sahara suites but mun gama komai zan iya fitowa yanzu idan ka buk'ata."

Takaici ya cikata, sam baya da sirri ko kad'an a rayuwarsa komai munin abu zai iya fad'a muddun aka tambayeshi. Ta watsa mashi harara had'e da maida kanta bisa pillow ta juya mashi baya.

Bai damu ba ya cigaba da fad'in "Should I come? Ai ban takura oga, tun jiya muke tare da ita, kuma she's not kinda sweet da mutun zai gagara barinta, nima i just manage ne tunda an riga an saba.."

Ta juyo a firgice tana kallonshi, sam baya da mutunci ko kad'an ita kanta bata san tsotsan da ke sawa tana lik'e mashi ba, ta ja d'an siririn tsaki tana watsa mashi harara lokacin da d'ayan bangaren aka amsa "Ok, ka sameni BG za'a kawo kud'in wannan yaron da daddare, sai mu san yadda za'a tsara abun
"

"Ok 30minutes.." Ya fad'a tare da yanke wayar yana kallonta.

Kamar tayi kuka tace "Boy."

Ya kanne mata ido tare da sumbatar wuyanta yana fad'in "Alina dear."

A hankali tace "Da gaske manage kake dani.?

Ya gyad'a mata kai yana murmushi, yayin da ta zabga mashi harara tana fad'in "Allah ya isa.."

Ya kanne mata ido yana fad'in "Ni kike ma Allah ya isa don na fad'i gaskiya bak'ya da taste d'in da zan gagara fita Alinah.?

Ta watsa mashi harara, a hankali tace "Stupid.!"

Yace "Nice name! Alina mai sunaye kala kala."

Shiru ta masa domin muddun tace zata biye mashi yanzu nan zai manna mata hauka, ya mik'e yana jefa mata wani shu'umin murmushi tare da zura jallabiyarsa, ya d'auki boxer d'inshi ya maida babu maganar wanke najasar dake jikinsa.

Ya rank'wafo ya sumbaci kunnenta yana fad'in "Sai yaushe.?

Kai tsaye tace "Wa? Ni? God forbid! Kai nemo someone more sweeter than me."

Ya k'yalk'yale da dariya yana fad'in "Don't tell me daga yau shikenan? Haba Alinah! Gaskiya na fad'a ba k'arya ba."

Tayi banza dashi tare da gyara k'wanciyarta, ya had'a tarkacensa ya zuba a k'aramar jakkar dake gefen gadon fuskarsa d'auke da murmushi, sannan ya d'auki keys d'in motar shi ya sab'a jikkarshi a kafad'a ya juya yana fad'in "Am leaving, sai munyi waya."

SILAR WAYE..?Where stories live. Discover now