014

50 5 0
                                    

   💧💧 *SILAR WAYE..?*
          

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
    Wattpad@Feedohm.

                   *014*

       **Wani sabon kuka ya suɓuce mani, wanda na rasa shin na farin ciki ne ko akasin haka? Idan ba gizo idona yake mani ba, to babu shakka Aliyunah ne tsaye a gaba, a take na fizge hannuna daga riƙon da Farouku yayi mani, na faɗa saman faffaɗan kirjinsa na rungume shi, tare da zagaye hannuna a bayan sa, wata sassanyar ajiyar zuciya na saki lokacin da wani ni'imtaccen ƙamshi ya daki hancina, tsigar jikina ta tashi yarrr.. domin wannan ne karo na farko dana taɓa rungume wani namiji a rayuwa ta..

Delu ta rafka salami tana faɗin "Laha'ila! Yau naga tsiya da wasali, ke kam Hinde kanki ɗaya kuwa? Kin san wa kika rungume? Ƙanin mijin ki fa ne.?

Na ƙara ƙwantar da kaina bisa ƙirjin sa yayin da na soma faɗin "Ƙarya kike, wannan Aliyu nah ne kuma zuwa yayi ya ɗauke ni daga nan gurin, ko Aliyunah? Dan Allah mu tafi, kar ka tsaya sauraren su, wallahi bana son shi bana ƙaunar shi, hakanan Gwaggo ta liƙa mani shi, kawai ka dauke ni daga nan, mu tafi nesa muyi rayuwar mu, na san ba zan taɓa nadamar binka ba."

  A fusace Mamy ta matso gurin, ta fizgoni da ƙarfin tsiya daga ƙirjin sa, yayin da ta ɗaga hannu da niyyar kifa mani mari, yayi saurin riƙe hannun yana kallon ta da idanu sa da suka sauya kala, cikin wata irin raunanniyar murya ya shiga faɗin" Dan Allah karki daketa Mamy, me yasa baku da uzuri ne? Shin baƙya tunanin zafin marin da yayi mata ya sa ta firgita take faɗin waɗannan kalaman? Koko baƙya tunanin nayi mata kama da wani Aliyun da ta sani.?

Farouku kam tsaye yayi yana kallon mu kamar sakarai , duk zafin zuciyar shi ya gagara cewa ko da Uffan tsabar mamakin dake neman daskare shi.

Saɓanin Mamy da tace "Bar ni in ci uban ta Haydar, baka ji me take fada ba? Ai ko a makance ta laluba ka ta san kafi ƙarfin ta nesa ba kusa ba, me zai sa tayi gigin taɓa maka jiki bayan tana a matsayi matar ɗan uwanka. ?

  Ya juyo ya kura mani ido, cikin wata irin daskararrar murya yace" Hindatu ne sunanki ko? Kiyi hakuri, wannan ba Aliyun da kika sani ba ne, wata ƙyil kama muka yi, wannan Aliyun ƙanin mijin ki ne! Kuma ina roƙan da ki fitar da wancan Aliyun a zuciyar ki, domin kin riga kin mashi nisan da har abada ba zai taɓa samun ki ba.!

  Wasu Siriran hawaye na hango ƙwance a ƙasan idon sa, wanda ke tabbatar da babu gaskiya a cikin kalaman sa.

A fusace na fincike hannuna daga Mamy ina faɗin" Sake ni! Ƙarya kake, wallahi kai ne Dafta Aliyu! Ko cikin gigin mutuwa nake zan iya gane ka, zan iya gane ka koda da muryar ne, na san kawai ka faɗi haka don ina auren wancan banza! Ai zan iya saki na, dama kai nake jira! Na faɗa maka bana son shi bana ƙaunar shi, da kai kadai nake so muyi rayuwa Aliyunah! Ba zan taɓa ɗaukar wancan shashashan a matsayin miji ba, ka faɗa mashi ya sake ni yanzu Aliyu dan Allah..! Na ƙarashe maganar idona ƙyar cikin nasa, yayin da hawaye ke duganya kamar an buɗe famfo.

A tsawance ya ce "Bani bane Hindu! Ki dawo cikin hankalin ki, ke matar yayana ce..!

Ya juya da azama ya bar falon da sassarfa, shin idan ya faɗa mata shine Aliyun ta me zai amfana mata? Mene makomar su? Shin da wane matsayi zata kalle shi? Tsohon saurayinta ta da take ƙauna koko ƙanin mijin ta da bata so? Shin zata haƙura ne ta ƙwantar da hankalinta ta zauna da ɗan uwanta shi koko zata yi borene? A iya fahimtar shi muddun ya sanar mata da shine Aliyun ta ba zata taɓa rusunawa ba a halin da take yanzu, ba zata taba ƙwantar da hankalinta ba! Ba kuma zata taba samun natsuwa ba ta zauna da ɗan uwanshi,  Shin ya Farouku zai ɗauke shi? Ya sani sarai yana da zafin kishin tsiya, ba zai taɓa saurara mashi ba duk da yana ɗan'uwan shi, haka zai cigaba da zargin shi yana son ta har tsawon rayuwar su! Rumtse idon shi yayi gam yayin da wasu zafafan hawaye suka silalo! Shin ya zaiyi? Wannan ce ƙaddarar su kuma dole su su amshe ta hannu biyu biyu...

SILAR WAYE..?Where stories live. Discover now