💧💧 *SILAR WAYE..?*
©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm.*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR🌹_*
*07****Bayan sun gama magana da Farouk ta janyo wayarta tayi dialing number delu, sau d'aya tayi k'ara ta d'aga tana fad'in "Hilo Mamy, ina dai ta bada hakuri."
Mamy tace "Ki zo yanzu ina nemanki Delu."
Delu tace "To Mamy, ina hanya ai nasan baki kiran banza."
Ta yanke wayar ta ba tare da ta k'ara cewa uffan ba domin ita irin wad'annan mutanan ne da basa k'aunar a rab'esu sosai shi yasa ta cika wulak'anci da izgili ta yadda duk k'wak'war mutun ba zai so zama da ita ba.
Ita kam delu ko abincin da take ci bata k'arasa ba ta d'auki ficicin gyalenta ta sagala a kafad'a ta fice tana bawa autanta sallahun yaje ya fad'awa Gwaggota ta wuce kar don haka kar ta aiko mata dambun da tace da marece. Awa d'aya ta kaita cikin garin katsina dan ma sai ka hau machine ya fiddaka titi daga k'auyen mu sannan kake samun motar tafiyar, amma da ace mota ce daga k'auyen mu zuwa katsina to bazata wuce minti talatin ba.
A falo ta isken Mamyn tana shafa Jan farce a k'umbarta, ta samu gefe ta rakub'e tana maimaita "Hakuri dai nake badawa Mamy, a yafe mani nayi kuskuren tsoma baki a inda ban kai ba."
Sai da ta k'are abunda take sannan ta juyo gurinta cike da izza tace "Ba shegen surutunki na kira ki ki mani ba, so nake ki samo ma Farouk yarinya k'yak'yk'yawa a k'auyen ku mara galihu."
Delu ta rangad'a gud'a tace "Ahab! Duke wanda yak'i ta delu ai ya t..." Sai kuma dafe bakinta tana kallon Mamy da ta kafeta da ido..
A sanyaye tace "Mamy nace fara ko bak'a, y'ar duma duma ko kuma siririya k'aramin alhaji ke buk'ata.?
Mamy ta watsa mata harara ba tare da tace komai ba.
K'asa Delu tayi da k'ai ta kuma rusunawa tace "Nace har da auta za'a samo ma wa.?
Ta daka mata tsawa cikin k'osawa da zancenta tace " Ke dai anyi wawiya Delu! Ina ce farouk nace ki samo mawa? Me ya kawo Haydar a zancenki? Ki kiyayeni tun kafin in ci maki mutunci! Autana yafi k'arfin ki nemo mashi matar aure! Mutun ne cikakke mai cikar kamala! Kin tab'a ganin Aliyunah...? Ta tambayeta idonta k'yar saman fuskarta.
Delu ta girgiza kai tana jib'i tace "Wane mutun Mamy? A gafarceni ban tab'a ganinshi ba sai dai sunanshi.."
Cikin kakkausar murya tace "Kamar yadda baki tab'a ganinshi ba haka nake so zancen shi ya bar bakin ki..!
Delu tayi tsit tana mazurai, yayin da ta kuma kallonta tace "Tashi ki bani guri, nan da sati d'aya ki kawo yaran har gida ya zab'i wacce yake so! Kar ki manta mara galihu....!
Ta mik'e jikinta na rawa tayi hanyar kitchen, ta soma kakkab'e kakkab'e duk da ba'a sakata ba, yayin da take jin ranta yayi fari tas kamar an zunduma ta aljannah, sai dai tunaninta ya tsaya cak ga yaran da zata kawo ma Mamy! Ita kam wace yarinya ce k'yak'yk'yawa kuma mara galihu a k'auyensu? To ma me yasa sai mara gata? Ta tallabe kumatu tana neman mafita.
Tafi minti uku tsaye sannan ta jijjiga kai had'e da tab'e baki tana fad'in "Ina ma ina da y'a mace.!"
Mamy kam ji tayi duniyar baki d'aya ta juya mata "Haydar.! Ta fad'a a fili tare da furzar da iska mai zafi ..
" Ban tab'a ganin d'an da yake k'in uwarsa ba..!" Ta ja tsaki ta mik'e ta soma safa da marwa.
Tana son ganinshi!Kamar an tsikareta ta janyo wayarta, ta shiga rubuta d'an gutun message " _Duk inda kake da daddare ka zo gida ina nemanka._ "