10

76 15 0
                                    

💧💧 *SILAR WAYE..?*
          

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
    Wattpad@Feedohm.

*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR🌹_*

   _Assalamu Alaikum Dan Allah Ku Gafarce Ni Ƙwana Biyu, Uzuri Ne Babba Ya Riƙe Ni, Amma Alhamdulillahi Komai Ya Kammala, Zamu Cigaba Kullum Da Yardar Allah. _

                   *010*

   ***Cikin d'an k'ank'anin lokaci rayuwa ta sauya mani, na nemi farin ciki had'e da walwala na rasa, yayin da na fige na lalace! Babbar matsalata bai wuce Aliyunah ba, da yayi b'atan dawo, na nemeshi na rasa kullun Cikin zarya zuwa nake asibitin da yake amma sam babu shi babu alamunsa, zuwan da nayi ma na k'arshe sai na tarad da an kawo wani sabon ma'aikaci, na ci kukana a ranar kamar raina zai fita..

Gefe guda kuma Gwaggo da Ubangida sun had'e mani kai sunce muddun na kawo cikas ga wannan auren wallahi basu yafe mani ba, kuma sai dai in nemi wasu iyayen ba su ba, don ko zama ba zasuyi dani ba.

Sannan kuma daga gwaggo har ubangida babu wani shirin da suke domin ance ba'a buk'atar komai daga garesu shi yasa suka nad'e k'afa suna hura hanci, babu wanda ya sayi ko da cokali.

Ana saura k'wana uku d'aurin aure, da sassafe sai ga Delu ta shigo kamar an jefota ta d'aga labilen d'akin gwaggo tana fad'in "Tatu dallah kiyi maza ki shirya ke da Baban Hinde kafin in gama karyawa in dawo."

Gwaggo tace "Lahiya aminiyas? Ina zamu kuma.?

Kai tsaye Delu tace " Yanzu Mamy ta kira mu je dake da uban yarinyar birni, ku ga lefen da aka had'a mata. "

Gwaggo ta zaro ido tana fad'in "Yo Delu ba'a nan za'a kawo shi ba.?

Ta rafka mata harara tana fad'in" Sun ce ba zasu kawo kayan su ba masu tsada nan a sace.!

Amarya data fito daga makewayi ta rangad'a gud'a tana fad'in "Ni na ga gidan b'arayi! Wato dan tab'ewa iyayen d'iya ne zasu je ganin lefen ba gurinsu za'a zo gani ba! Kai tur Allah ya raba mu da asara."

Gwaggo ta ja dogon tsaki tace " Eh mu zamu je! Yo Allah na tuba ta ya zasu kawo lefensu bayan sun san da irinku y'an bak'in ciki a gidan? Ai ko ba ku sace ba kun lallaɓa ku balbala masu wuta.!

Ta buga buje ta shige d'akin tana fad'in "Kinga aminiyas, taho muje kawai idan mun isa birchi zan sai maki fanke da dinja."

Delu tace "Ayi haka Tatu.?

Gwaggo tace " Me zai hana? Ai kin gama mani komai Deluwa tunda har kika kai y'ata gidan arziki, kuma insha mana Allahu duk abunda ta rarumo raba dai dai za'ayi."

Delu ta k'yalk'yale da dariya, lokacin da ta bawa gwaggo hannu suka kashe sannan suka had'a duwawu guri gud'a suka sa gud'a..

Ni dai ina k'wance d'aka, babu eh babu a'a ga uban zazzab'in da ya rufe ni.

   Ban sani ba ko da ubangida suka tafi, amma ina k'yautata zaton a hanya suka gamu dashi, domin bai dawo gida ba sai gab da magriba suka shigo shi da gwaggo da Delu, bakin nan hangame suna santin tumulin kayan da aka nuna masu aka ce duk lefena ne.

Haka suka d'auko hoton kayan a wayar Delu, kusan manyan ak'watuna saiti uku, mai guda shidda a Cikin kowane saiti, abunda sukace atamfa ta kai kala saba'in sai leshi manya manya da shaddoji da kuma yadina na manyan masu kud'i da jallabiyoyi, sun ce harda d'ankunnen zinari da zobe guda biyu da kuma sarkok'in azurfa kusan kala sha biyu.

Ina k'wance gwaggo ta shigo ta samu gefen katifa ta zauna had'e da tub'e rigarta tana fad'in "Hinde bacci kike.?

Nayi lamo kamar mai baccin gaske, domin a tunani idan taga bacci nake zata rabu dani, amma sai naga sab'anin haka domin duka ta rafka mani a cinya tana fad'in " Tashi don ubanki mu yi magana tun kafin ta kashe ni."

SILAR WAYE..?Where stories live. Discover now