04&5

77 4 0
                                    

💧💧 *SILAR WAYE..?*
          

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
    Wattpad@Feedohm.

*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR🌹_*

*04 & 05*

       ***Kai tsaye k'aramar asibitin garin mu na nufa gurin Dafta tare da addu'ar in same shi kad'ai ba tare da marasa lafiya ba, tafiya nake ina hawaye tare da nema ma kaina mafita domin ba zan tab'a yadda da k'wamacalar da Gwaggo ke neman yi mani ba kalmarta tayi mani ciwo matuk'a, wai uwar da ta haifeni ce ta bud'e baki tace inyi aure ko na sati biyu ne in fito, ita dai burinta ta mallaki abun duniya, abunda zai k'are na d'an wani lokaci, ba tayi tunanin zafin zawarci ba! Ba tayi tunanin yadda rayuwata zata kasance ba, a tunani na ko wacce uwa burinta bai wuce y'arta yin aure na din din ba, shi yasa wani sa'in har tunani nake anya ita ce uwata? Anya ita ta haifeni? Sai dai tsantsar kamar da muke kad'ai ya isa ya tabbatar da haka.

Bansan na isa gurin ba sai dai tattausar muryar Dafta da naji yana fad'in "Kibi a sannu karki fad'awa dutse Hindu."

Na d'ago na kalleshi yana tsaye daga cikin d'akin magani da alama wata yake ma allura, ya mayar da kanshi ga abunda yake yi yayin dana taka tudunkar asibitin na k'arasa bakin tagar ina jiran ya sallameta.

Sai da ya kammala komai ta fito sannan ya kalleni da rikitattun idanunsa yace "Come in, zagayo in ji wa ya tab'a mani Hindu idonta yayi canza launi daga madara zuwa barkono." Yayi mana alama da hannunshi da in zangayo.

Na zagaya ciki  na samu kujeran da marasa lafiya ke zama na zauna tare da sadda kaina k'asa hawaye na bi mani kumci.

A hankali yace "Menene Hindutah.?

Nayi shiru sai shashshekar kuka nake.

Tsam ya mik'e ya dawo kusa da ni ya zauna bisa teburin gabana tare da rank'wafo fuskarshi dai dai tawa har ina iya jin k'amshin kanunfarin dake fitowa daga bakinshi, na lumshe idona a hankali tare da sauke ajiyar zuciya.

  A tausashe yace "Fad'a man me aka maki mana Hindu? Gwaggo ce ko amarya koko Sabura? Yanzu mutun yasha bulala."

Cikin kuka na tambaye shi "Ka san kano.?

Ya gyad'a kai idonshi na saman fuskata, a natse yace  "Na sani mana Hindu, ko had'uwar mu ta k'arshe ai na fad'a maki naje ko? Please ki bar kukan haka ki fad'a mani matsalarki, ko wani abune ya faru a kano.?

Nayi shiru nak'i cewa komai, tattausan hannunshi naji saman hab'ata yana fad'in "Kalle ni Hindutah..."

Na d'ago muka had'a ido tsigar jikina ta tashi yarrr, a hankali ya saka babban yatsan shi na dama ya goge mani hawayen dake ambaliya a saman fuskata, ya sumbaci goshina sannan yace "Bana buk'atar fitowar wasu, now fad'a mani me ke faruwa.?

Taya zan iya fad'a mashi so nake mu gudu daga garin muje nesa muyi auren mu a matsayina na y'a mace? Na sadda kai kasa ina tunanin ta inda zan fara.

" Hindatuh....! Ya fad'a cikin wata irin siga.

A hankali nace "Ai kana sona ko ZAKI..?

Ya gyad'a kai yana murmushi, tare da tausasa muryar yace " Fiye da SO nake maki  Hindu.. "

Nayi jim kafin ince "Y'ar gidan Habi mak'wabtan mu itama Muntari ya sota sosai ai.."

Yace "Umhum..?

Na kalleshi sannan nace " Da aka k'i yadda suyi aure sai suka gudu kano wata hukuma ta d'aura masu auren su."

Ya murmusa yana kallona a hankali yace "Basu k'yauta ba."

SILAR WAYE..?Where stories live. Discover now