03

70 6 0
                                    

💧💧 *SILAR WAYE..?*
         

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
    Wattpad@Feedohm.

*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR🌹_*

*03*

       ****Ta d'ago labulen d'akin tana fad'in "Yi maza bur suna foda sannan idan kin je ki ce mashi ya taimaka maki da wasu y'an kud'ad'e bani da lafiya zamu sayi magani, kinsan sa'idu bai iya laluba aljihu ba sai dai ya d'irko mana sabulai kamar y'an wakau."

Wani k'ululun bak'in ciki ya turnuk'eni, wai uwa ce ke shiryawa y'arta wannan k'arya? na kafeta da idanuwa da suka kad'a suka yi jawur babu ko k'yaftawa.

Muryar Mai alala na tsinkaya tana fad'in "A'a Tatu cewa zakiyi abun kunya a kanku ba wannan ne farau ba, kullun cikin tik'ashi kuke! banda lalacewa da masifar rok'o meye na yima saurayin y'arka k'aryar ciwo..?

Gwaggo ta zaburo tana fad'in "Bana son munahurci amarya! Har mu zaki fad'awa abun kunya? bayan duk garinku babu wanda bai san a mak'abarta aka kama tsohonki ba yana lalata da mahaukaciya? Mai ya kai wannan kunya.?

Ta dafe kirji tana fad'in "Ni Tatu.?

Gwaggo tace "Eh ke d'in amarya ko k'arya nayi.?

Muna tsaye ni da Sabura har suka gama d'ibar albarkarsu sannan ta kuma korani gurin Sa'idu, haka na fita na rik'e kugu babu uhm babu uhm uhm har ya k'araci karairayinsa ya aje man bak'ar ledar ya tafi yayin da na d'auka na kai mata a d'aki na dire mata sannnan na cigaba da sabgogin gabana..

Bayan kwana biyu ta fita saro gyad'ar da zatayi k'uli ranar alhamis sai gata ta dawo da k'atuwar leda a hannu bakin nan washe yadda kasan an mata albishir da gidan aljannah, ta direta gabana tana dariyar farinciki, sannan ta janyo buhu ta zazzage kayan abisa tana fad'in "Mai Alala zo ki ga abun arziki."

Na sauke idona bisa kayan, gasu nan su taliya, filawa, sukari da sabulun wanka.

Mai Alala ta matso ta zubawa kayan ido cike da mamaki, tayi sannan ta kalli Gwaggo tace "Na shiga uku! Tatu wad'annan kuma daga ina.?

Ta rafka gud'a tana fad'in " Kayan arziki! Ai Alhaji tsoho ya bani su yanzu dana fita."

"Na meye.? Ta tambaya kamar zata kifa.

Kai tsaye gwaggo ta cunno ni da baki tana fad'in " Yo y'ata ya gani jiya da daddare ya k'yasa shine ya fara bani toshiyar baki."

"Ke Tatu? Kina da hankali kuwa? Duka yaushe ya k'ara auren.?

Gwaggo tace " K'wana uku kenan da kawo mashi amarya, to meye a ciki  idan yace yana bid'ar Hinde.?

A sak'wame tace "Kuma sai ki bashi.?

Ta tokare d'ank'wali tana fad'in " Ras..!

"Sa'idun karofi kiyi ya dashi Tatu? Ga kuma Dafta anya kina tsoron Allah.? Mai alala ta fad'a idonta k'yar a kanta.

Kai tsaye Gwaggo tace "Ana maganar arziki bari kira mani dafta amarya, kuma ni me ye ruwana? Wanda yafi bani abun arziki shi zan bawa, kuma da alamu ma Alhaji tsoho ke da rabo domin da zafinsa ya matso."

Mai alala tace "Ai ko da kinci amanar sa wallahi.."

Gwaggo ta zabga mata harara tace "Anya bak'in ciki zai barki kiyi k'ib'a amarya.?

"Ba maganar bak'in ciki Tatu, ki rage son abun duniya! kuma ai ubangida na gab da dawowa nasan bazai yadda da wannan k'wamacalar ba."

Tayi watsi da ita tare juyowa tana fad'in "Yarinya mai goshin arziki ta Alhaji tsoho ga gida ga mota ga kuma baban aljihu ta shi maza ki shirya da daddare yana nan tafe tad'i."

SILAR WAYE..?Where stories live. Discover now