08

55 5 0
                                    

💧💧 *SILAR WAYE..?*
          

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*💡
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR:- FEEDOHM💞*
    Wattpad@Feedohm.

*_D'AND'ANO DAGA FITATTU BIYAR🌹_*

 *08*

     ***Takaici ya rufeni, na kalli amarya da ta lek'o daga d'akinta ta tallabe kumatu tana kallon wannan abun kunya, na fusata na k'arasa kusa dashi nace "Dallah Malan tashi ka bar mana gida! Wannan wane irin iskanci ne zaka shigo gidan matan mutane har da samun gurin ka zauna, ko kunya baka ji ba."

Ban rufe baki ba gwaggo ta k'wad'a mani bahaggon mari a kumcina na hagu, ta nuna ni da yatsa idonta ta cike da fitina tana fad'in "Sannu asararra mara mutunci! Wato duk abunda kikayi a bayan idona bai isheki ba sai kin zo har gaba kin tata fitsara da rashin kunya irin wadda waccen zindik'in k'aton ya koya maki." Ta k'arashe maganar tare da finciko wuyana ta narka mani dundu a baya.

Ya katseta da sauri yana kallon k'irjina " Bance ki daketa ba, amma duk randa na k'ara ganinta da wani wallahi tallahi duk abunda ya samu mutun shi ya janyo ma kanshi."

Ta k'wantar da muryar had'e da rusunawa tana fad'in "To Alhajin Allah, a dai yi hakuri, kasan Hinden har yanzu yarinya ce."

Yace "Ba komai.."

Ya lalubi Aljihu ya fiddo da naira Dubu guda biyar ya zub'e saman tabarmar yana fad'in "Ki ma ubanta magana idan ba zai dawo don ku ba to gaskiya ya dawo dan ni, sabida bana son auren ya d'auki lokaci.."

Ta dafe kud'in tana fad'in "Ai Hinde taka ce Alhaji, da k'warank'watsa ko gawar ta ce sai na kai maka ita d'aki, ka k'wantas da hankalinka yau d'innan zan kira ubangida in shaida mashi wannan abun abun arzikin.!"

Ya k'washe da dariya yace "Har naji sanyi da billahillazi..!"

Jikinta har k'yarma yake ta shiga godiya, ya juya ya fice yana kallona kamar bak'in maye! Yana fjta Delu na shigowa don haka na fad'a d'akin ina fad'in "Ga d'ayar munafukar nan.!

Ta samu guri ta zauna tana fad'in "Oh ni Delu na shiga uku! Haka kawai Mamy ta kirani tana kuka wai in samo ma farouku matar aure! Nace wa? Ni kam ba zan samo ma wannan mara kunyar mata ba." Ta rik'e hab'a tana yatsina fuska.

Wata zabura gwaggo tayi tana fad'in "Ke Delu? Da gaske.?

Ta yatsina fuska tace "To menene Tatu? Ina ce ni na samo ma tsohon shi mata lokacin da zai auri Mamy.?

Wani jib'i ya biyo ta wuyan Gwaggo ta saka hab'ar zaninta ta share, ta bud'e baki murya na rawa tace " Kuma duk wacce kika kai ita zai amra Delu.?

Delu ta ja siririn tsaki had'e da gyara zaman gyalenta sannan tace " K'warae ma kuwa Tatu, kuma y'ar ka'uye suke so mara gata! Ni kam na rasa irin wannan jarabar ace wai ba za'a auri yarinya mai gata ba, kin san lokacin da bri (bro) zai auri Mamy haka ya dage lallai ba zai auri mai gata ba."

Amarya ta fad'o kamar zata kife k'asa tana fad'in "Ai ko ga Sabura  nan Delu, ko gatan k'wana d'aya bata dashi! yo Allah na tuba wa zai auri yarinya mai gata taje ta dinga shuka mashi rashin mutunci."

Gwaggo ta watsa mata harara "Uban sabura! Hinden fa? Inyi Yaya da ita.?

Delu tace "Kai ni ku rabu dani, ina jin yaranku duk da gatansu."

Gwaggo ta lank'washe murya, cikin sigar tausayi ta soma fad'in "Yo wane gata Hinde gareta Aminiyas? Dan girman Allah ki taimaka ki bashi d'iyata, haba aminiyas ina ce idan kika ji batun k'aruwa gurina zaki fara lallab'owa, kuma ai naga Hinde d'iyarki, idan aka dace ke kika dace."

SILAR WAYE..?Where stories live. Discover now