KARKASHIN KASA 1️⃣

5 0 0
                                    

*

  Da sunan Allah mai rahma mai jikai,Ina salati   ga ma zon tsira Annanbin da aka Aiko ga mutane baki daya da alayansa.Allah sa mana Albarka ciki lamuran mu🙏 amin

    

   🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌹🌹🌷🌹🌹🌸🥀🥀
              🥀🥀

KARKASHIN   KASA

🌹🌹🌹🌷🌹🌹🌹🌸
🌹🌹🌷🌹🌹🌸🥀🥀
                 🥀🥀

             NA

    MURJANATU UMAR

Gabatarwa:wanan labarin kirkiransa akai tun (2000) sanan aka sauya shi zuwa turarenci (2012)

Fata na wanan labarin ya zama darasi gare mu; muyi anfani da Abu mai kyau ciki mu watsar da Mara anfani!

VOTE     WATTPAD: MAIYAMMA

    TUSHEN LABARIN

Hajiya Salma ta farka don yin sallar Asuba sai taga Najwa ba Naja'atu ,ta dauka ko Alhaji ne ya dauke ta ,sai ta tafi Tai sallah bayan ta iddar ne sai Hajiya Salma  ta shigo don su gaisa ,Bayan gaisuwa sai take tambaya Ina Naja'atu sai Hajiya salsa tace" tana wurin Alhaji Ina ga don na farka ban ganta ba !

Hajiya Salma ta yi jugum tace" Anya kuwa mommcy ,yanzu daga wurin Alhaji Nike "
  Sai sai Hajiya salwa ta tafa hannu tana rafka salati
" Shike nan na shiga uku na ga ta kaina......"
Taf Taf suka ki tafiyan Alhaji ,ya shigo tare da sallama don yaji ta Shiru Kuma Yana son yaga 'ya'yan sa sai yazo ya tadda Hajiya Salma na rafka salati.

"Lafiya?" Alhaji ya tambaya " me ya faru kuma?"

  Hajiya Salma tace" Alhaji Naja'atu ce  mummcy tace Bata gani ba ko tana wurin ka?"

"A'a Yaya haka ace Dan mutum ya bace? Bata wurina ,Kai a duba ;hajiya duba wurin yaran nan ko akwai Wanda ya dauke ta!"
  " To Alhaji" ta fita
Hajiya Salma (mommcy) dai sai kuka take ,shi Kuma Alhaji sai lallashi yake Yana kwantar mata da hankali .
Hajiya salwa ne ta shigo
" Alhaji an duba ko Ina ba'a ganta ba "
"Subhanallah!" Alhaji ya Mike da sauri ya fita ya zaga lungu da sako na gidan bai ganta ba .Wasa _wasa sai da ta kaiga an Kira yan sanda.

  Alhaji Usman Dan asalin jihar kano ne Amma yayi karatunsa a Jami'ar Ahamed Bello(ABU) daga nan ya zauna a garin ya fara sana'arsa inda yayi Aure har mata biyu dukan su yan garin zariya Hajiya Salma da Hajiya salwa.

  Hajiya salwa ita ce Uwargida Kuma tana da 'ya'ya Bakwai Wanda a ciki akwai Abdulhakim,Hanifa,kasim, Khalid,Rukkaya,sai twins wato Naja'atu da Najwa.

   Ita ko Hajiya Salma  tana da 'ya'ya hudu.Najib, Haisam,Huwaila da Hana n.kuma saboda Adalcin mai gidan nasu duk kamsu a hade yake .

  Wasu barayi sun sa Alhaji gaba akan lallai ya basu wasu makudan kudi   ko Kuma su sa rayuwan shi a hatsari,Amma da yake Alhaji Usman namijin duniya ne sai yayi biris dasu;Kuma shi mutum ne da ba'a tilastawa ya canja ra'ayi.

Haka Kuma ya farune a sabon gidan sa dake kaduna .Da yake mai son abinka yafi ka dabara duk masu gadin dake gadin gidan da karnukan gidan bai Hana barayin ratsowa ba saboda sun Sami sa'a wurin hatsabibin bokan su.

   Sanda barayin nan suka sato ta sai suka wakilta wani cikin su yaje ya yarda da ita ko ya kashe ta .Ba'a tashi yarda Naja'atu a kowanne kauye dake kusa ba sai da aka Kai kauyakun dake cikin jahar katsina ;aka aje ta a wani gona.

   Sai da hantsi ya dubi ludayi sanan ta fara tsala kuka ,mallam Audu ya zo wucewa ta wurin gonan sai yaji kukan jariri ,har zai wuce sai ya dawo Yana dubawa
har ya hango Naja'atu yai addu'a ya dauka ya tafi da ita gidansa.

  @ Maiyamma's library✍️

KARKASHIN KASAOnde histórias criam vida. Descubra agora