9️⃣

1 0 0
                                    

https://www.facebook.com/tambari-writers-association-106345791122870/

     *KARKASHIN KASA*

              *NA*

*MURJANATU  UMAR*

*WATPAD : MAIYAMMA*

🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹

   🥀🥀🥀🥀

🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹🌹
            🥀🥀🥀🥀

Haka dai Al'amarin yaci gaba don Fahad ya Hana ummi zumunci da kubra Yana ganin ita ke sa samari na ziyartar kubra da Wanda ya dace da Wanda bai dace ba wai ummi ba natsetsiya bace ,sanan Hashim ba ajinta bane.

    Da wanan cin zarafin Fahad ya raba ummi da kubra ;ummi taji haushi ba kadan ba sanan ga sanadin da yace zai mata na barin aiki ,ita ba diyar kowa ba dole ta lallaba ta rufa ma kanta asiri ta tsaya inda take ,sanan ta nema ma kanta mafita tasa kanta islamiyan rana Bayan sun gama aiki take tafiya.

    Yau Alhamis ba makaranta ,saboda haka Bayan su ummi sun gama aiki sai ta dauko littafanta tana bita ,taba cikin bita baba saude ta Aiko Indo Akan ta zo ta Kira ta ta kaiwa bakin yaran gidan abinci ,maimakon ta isar da sakon sai ta tsaya neman ba'asi tana cewa"sannu Alhudda _huda kin wani dauko littafi kina karantawa kamar kin fi kowa ne mts! Mutum ba dangin iya balle na baba tunda kika zo nan bamu taba ganin kinje ganin gida ba ,sai auki rabe_rabe Allah ya kyauta,kije ki dauko abincin su Yaya Abdul _hakim ki Kai musu ."

   Gaskiya ran ummi in yayi dubu ya baci amma sai ta danne don gaskiya ta fada Kuma ta Saba da jin wanan gori tuni,taje ta dau abinci ta Kai parlour tana jerawa akan dining table ,a parlour Kuma akwai jama'a da dama,wannan shine abunda ya Kara Bata haushi  wato ita kadai suka Bari da aiki ,a cikin zuciyar ta tace "Allah Kaine gata na ka taimake ni ka sadani da iyaye na !"
  

   Tana cikin zancan zuci taji an fusgo ta an juyad da ita zuwa ga kallon jama'an maimakon he
Jeran abinci ,sai ki Tai an ce wanan ba mummy bace (baby mummcy)

   Ita Kuma abin ya Bata mamaki Kuma ya kusan sata  kuka ;sai irin rikon da wannan mutumin ya mata alhalin shi ba muharaminta ba ,ita Bata ji sauran zance ba Amma taji ance "wallahi  na zata mummy ce Amma Naga wanan gentle ce ba kamar shagwababiyar ba sai dai kamar tasu ta baci ,ya sake mata hannu ya koma ya zauna suna ci gaba da ta'ajibin lamarin.

   Bayan ta gama jera abinci ummi ta shiga daki taci kuka har ta gaji Tai Shiru don kanta,ita bakin cikinta wanan da ya rike hannunta mai kama da yahudu Wanda ya Ara halinsu ya yafa duk ya watsar da dabi'u Malam bahaushe masu kyau

    Washe garin juma'a akai dinner taya yaran gidan murnan gama karatun su cikin sa'a.An ci an sha anyi kade_kade ,su ummi Kuma sun Sha aiki don ranar jiki kam yai ciwo ,ranar asabar kuwa Bayan ummi ta gama aiki dama an raba musu tun bayar tafiyar Yaya Ahmed  wato wasu suyi aiki da safe wasu suyi da  rana wasu da yamma so yau aikin safe ne da ummi ta gama aiki ta hau shiri lokacin makaranta nayi ta wuce.

   A makarantar su ummi akwai yaran talakawa Dana masu kudi saboda neman ilmin addini don a wurin Allah talaka da mai kudi duk daya ne sai Wanda yafi tsoransa ,ummi dai talaka ce sanan Bata ma San iyayenta ba ,Amma ta gode Allah da ya Bata ikon fita wurin neman ilmin addini ta.

✍️ *Maiyamma's library*

KARKASHIN KASADonde viven las historias. Descúbrelo ahora