4️⃣

2 0 0
                                    

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

   🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹🌸
         🥀🥀🥀
🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹🌹
                🥀🥀🥀

    
    KARKASHIN  KASA

             NA

     MURJANATU  UMAR

VOTE WATPAD: MAIYAMMA

               4️⃣

Hajiya sadiya sunan matar da ta taimake Amina ,a cikin kwana biyu ta Samar mata aikin a gidan Hajiya suwaiba .A gaskiya bata ji dadin aiki da wadan nan bayin Allah ba don Hajiya suwaiba da 'ya'yanta sun bata wahala sosai sun bautar da ita Tai Rama Tai duhu,gashi basu da Tarbiyya  ki kadan addini ma basu damu dashi ba saboda basu zauna a kasar ba ,a kasar turai suka zauna basu Dade da dawo ba sun bar yayansu can.

    Kai cin kashin mutanen nan suke yayi yawa ,su suke ta sanan ga wulakanci da uwa uba aiki.Amina na cikin wanan halin ne babban yayan su ya dawo ,Yana ganin Amina halin sa ya motsa ;da yake a turai yayi suna wurin neman mata ,kun San an ce mai hali baya barin halinsa ,a dalilin ya cimma hakar sa kan Amina ya taka ma mum din shi da kanne shi akan su dai na takurata da aiki karshe ma yace shi kawai zata dunga ma aiki,to da yake Dan lele ne kuwa haka aka yi.

   Daga baya suka nemi wata mai aiki aka bar mishi Amina tana kula dashi Kuma ya Hana a hada Amina da masu aiki aka ware mata nata dakin daban .

   Kullum ita ke kaimai abinci  har sannu _sannu yakan jata da hira Amma Bata biye mai sai dai tace eh ko a'a .

    Ranan ta Kai abinci sai yace da ita Yana zuwa ,ya shiga daki ,Bayan an jima sai ya kwalla mata Kira daga daki
Yace "zo ki karba ki kaiwa hajiya"

Taji tsoro Amma sai ta dake ta doshi dakin tana turawa mai zata gani "subhanallah!" Yana tsaye haihuwar uwar sa,Amina Tai waje a guje ;gidan da Bata Kara marmarin koma wa ba kenan.

   Bata zame ko Ina ba sai Tasha ,tana Isa Tasha ta afka motar kaduna ; da taimakon wani tsoho da yaga tana kuka ya tambayeta tace wasu me suka kwace mata jaka shine ya tausaya mata ya biya mata kudin mota .wurin karfe takwas suka Isa kawo ta ma dattijo godiya.

    Ta dai ji ana kiran sunayen unguwan ni; tudun wada,kawo da sauransu,kawai sai zuciyanta yafi kwanciya da tudun wada ,da suka sauka tudun wada sai ta biya kudin mota don dattijo nan ya Bata wasu kudi ta rike .Bayan ta sallami mai mota sai ta kama yawo cikin unguwan ikon Allah har tazo wani babban gida a inda Tai kicibis da wani mutum ta durkusa ta gaishe shi "don Allah mallam ka taimake ni na zo neman aiki ne tun safe Nike yawo gashi har dare yayi ban samu ba ;ya tsaya yayi Jim can yace"ba wai kama mutum rana ya maka dare ba."

Tace "wallahi baba ba haka Nike ba"

"To naji Amma Ina iyayenki?"

"Baba duk sun rasu ,uwar riko na kuma ta kore ni"

  Ya tsaya ya jinjina ya gama kallonta can yace" To Allah shige Mana gaba ;dama gidan can na neman Karin mai aiki."

  Wurin wata tsohuwa ya kaita yace" ga wata mai aiki na samo miki." Saboda kimar shi da take gani ta amshe Amina tayi mai godiya .

Wanan dattijo wato mallam Jibo yai mata sallama ya tafi sai da Amina ta Dade a tsugunne sannan tsohuwar tace "tashi ki shiga wancan  dakin shine na ma'aikata mata."

   Ta shiga dakin ta tarad da masu aiki wajen su goma da take dakin babbane ,da shiga nan suka tsuro mata Ido  sai suka koma yan kallon_kallon su day Amina sai suka koma hararanta suna cewa"kaga yarinya da shegen kyau kaddai ta kwace Mana samarin mu!"sai wata daga ciki tace "haba! Indo har wannan kazamar ta Isa ?haba kyaleta kawai ai a karkashin ki take kece shugaba ,ai kam ta fashe da shewa  tana banmu kashe lantai ,dukkan su suka fashe da dariya  "gaskiyar ki lamtai sai Indo masoyiyar Audi direba ,nan Indo ba mamaki!" Nan da nan sai hira ta barke tsakanin su Kuma suka manta da Amina.

  Ita kam Amina katifa ta samu ta haye tana hayewa sai barci don ta tsaya Tayi sallolinta a hanya kafin ta fara zagaye.

  Washe gari Bayan tayi sallar ta tashi taje ta gaida tsohuwa nan  wato Baba saude  ,ta gaishe ta ta amsa ciki_ciki sai tace "ya sunan ki?"

  "Amina Amma anfi Kira na da ummi ."

Tace "ummi ,aikin ki shine duk wani aiki da ake a gidan nan zaki dunga sa hannu da fahimta ."

Tace "to insha Allah"

  Haka kuwa take aiki kullum ,baji ba gani ,wata rana ma sakar mata aiki ake.

✍️Maiymma'slibrary.

KARKASHIN KASATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang