6️⃣

1 0 0
                                    

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

    🌹🌹🌹🌹🌸🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹
           🥀🥀🥀🥀
🌹🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹🌹

      KARKASHIN KASA

                  NA

MURJANATU UMAR
VOTE; WATPAD : MAIYAMMA


                    6️⃣

Wuya bata kisa wahala ba wadda ummi Bata gani ba ,ranan ya kirata yasa ta aikin kwashe kwata ,tana cikin aikin ta gaji sai ta Dan huta Yana zuwa ya ganta a zaune bai tambayi ba'a si ba sai ya hau dukanta ,Yana cikin dukan sai ga wani yayan shi ya zo wucewa ya dakatar dashi tare da tambayar shi ba'asi sai yayi mai bayani ,Bayan yaji ba'a si sai yace mai Yana da kyau ka dunga daraja Dan Adam duk inda ka ganshi balle Kai da zaka tafi course wata kasa ,kayi kokari ka rabu da mutane lafiya Mana don duniyan nan juyi_juyi ce !

   Sai yayan shi ya juyo yace"yi hakuri kinji ,tashi ki shiga ciki"
Dama masu zugashi Babah saude ce,in team dinta ke zugo ta tazo ta hada mishi karya da gaskiya,shi Kuma ya hau.

      Ummi ta Sami saukin aiki saboda tafiyar da Ahamed yayi ,da taga ta samin aiki sai ta fara fita waje tana zama kan benci can kofar gida ta tuna baya tana nazarin duniya,to akwai wata yarinya kullum in zata wuce sai ta kalle ummi kamar zata mata magana sai ta wuce ,ana cikin haka sai rannan ta zo wurinta Tai mata sallama ta amsata ta zauna sai Tai Shiru can tace"baiwar Allah lafiya kike sa kanki a tunani,kinsan kuwa Yana da illa!"

   Ummi tace"nasan haka sai dai lamarin rayuwa kan sa dole kayi tunani."

  "  Tabbas nasan da haka donni Naga rayuwa Iri_iri."

       Ni sunana kubra  iyaye na basu da hali Amma dai _dai gwarwado suna wadata mu don har makaranta mahaifin mu yasa mu ,a yanzu haka Ina da shaidar gama sakandire ,nice babba  a gidan mu Kuma mu duka mata ne.

   Bayan na gama sakandire sai Allah ya nufe mahaifin mu da ciwo kafa Wanda yai sanadiyar zuwana aikatau wanan gidan " ta nuna gidan dake kusa da inda suke .

  Tana nemi aikatau ne don na taimaka ma iyayena don mahaifin mu baya iya matsawa ko nan da can komai sai an mashi,Dan kudin da yake dashi duk ya kare wurin neman magani .To Dana haka kawai sai na nema izinin sa inje in samu aiki  ko da aikatau ne ,da ya ki Amma daga baya ya amince Bayan maman mu ta yi mai tuni akan cewar fa bamu da karfi haka ma yan uwan mu balle a samu mai daukar nauyi shi da iyalansa.

   Cikin ikon Allah na Sami wanan aikin a gidan Banda matsala da kowa Banda mutum daya   ya samin Ido bai da aiki sai na zagi na wai talaka ,wai shi ya kijinin talaka alhalin duk sauran masu aikin Irina ne Amma bai Raina kowa ba sai ni  ba irin cin fuska,akwai ranar da na ci aikin da ya sani mai yawa ban gama ba sai dare Kuma hakan yasa na makara.

   Da safe ya tambaye sauran masu aiki aka ce Ina barci ban tashi ba,bai saurare su ba ya kinkimo bukiti na ruwa ya juye min nai firgigib  na tashi numfashi na kokarin daukewa ga karkarwa da rawar sanyi Amma ba tausayi sai ya hau masifa ,sai da yayi mai isar sa ya fita ,Yana fita naje na gyara kaina na hada da yin wanka da ruwan dumi na bi jiki da rub nasa wasu kaya na gyara dakin.

  Sauran masu aikin sai murna suke an min wulakanci wai sunga karyan ji da Kai,don sunga ban shiga harkan su;shine fa suke ga ji da Kai gare ni ,to kinji kadan daga labarina."

  Ummi ta jinjina Kai tace "to ai nima labari na kusan haka yake." Ta kwashe labarin ta duka ta Gaya mata ,ta tausaya mata kwarai da gaske ,sun taba hira sai suka ma juna sallama .Da haka har suka shaku da kubra har gidan su ummi taje ta gaida iyayen kubra ,Tai ma babanta Allah sawake ,sun ji dadi suka sa mata Albarka,Kai Amma ranar ba karamin dadi taji ba don Bata taba samin wasu sun mata irin wanan addu'a bayan su mallam Audu.

   Akwai wani direba a cikin gidan da ummi ke aiki ,Yana Kai yara makaranta Sunansa Hashim tunda ya kyalla Ido yaga kubra a nace mata. Shi fa lallai ita yake so ,tun tana kwauce_kwauce har ta tsinke da lamarin sa saboda matashi ne
Natsatse ga Kuma iya kalami nan da nan yabi ya kalallame ta,har aka wayi gari Bata da abin so a samarinta sama da Hashim;sun tsumduma cikin kogin so don sunyi nisa basa ji Kira!

✍️ maiyamma'slibrary

KARKASHIN KASADonde viven las historias. Descúbrelo ahora