7️⃣

1 0 0
                                    

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

*KARKASHIN KASA*

*NA*

*MURJANATU UMAR*
*
VOTE ; WATPAD : MAIYAMMA*

🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹
🥀🥀🥀🌹🥀🥀

*KARKASHIN KASA*

🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🥀🌹🌹🌹

7️⃣

Ummi dai ta koma Yar kallo don ita duk Wanda ya nemi kaimata hari kaucewa take ;Bata manta abinda ya faru ita da sale ba .Mai ba fulawa ruwa yaso ya shishige mata Amma kullum sai dai ta kare da banka mishi harara, Shi Kuma ya kare da ban hakuri ,Rannan da ya ganta sai cewa yayi ke dai so kike ki zama matar mai fulawa ,ai nan da nan ta banko mai harara gami da tsuki ,tun daga ranan Bata Kuma bi takansa ba.

Amma ummi fa kullum cika take da mamakin kubra akan lamarin soyayyar su da Hashim,don cewa take duk ranan da Bata ga Hashim ba a ranar sai ta wuni zazzabi,ita dai ummi Bata kallo tana ta'ajibin irin wanan son ita Kuma kubra ta kare da Mara dariya tana haha yarinya duk radda kika nutsa ba mai kamo ki.

Kubra na yawan jin haushin duk Wanda ya taba saurayin ta ; haka ya taba faruwa saboda wata rana Buzu maigadi ya biyo Hashim Alan lallai sai ya rankwashe shi don ya Kira shi Buzu ,to dama shi Buzu maigadi ya kijinin a Kira shi da buzu ta fi son a Kira shi da sunan sa ,don ya kam ce "don Allah baku San suna na bane ? Sunana Yusuf."

Su ummi sun fito kenan suka hanga Hashim a kwata a guje kubra tayo wurin sai balbale Buzu take da masifa ummi kuwa na gefe sai babbaka dariya take ,kubra ta cika tayi fam don haushin Amma Bata ce ma ummi komai ba tayi rau da Ido kamar zatai kuka tayi wurin Hashim tana
"Sanu injin dai baka ji ciwo ba ?" Duk ta rude
Shi Kuma ya fito Yana "a'a banji ba"
Ummi ta Kara wurin tace "sannu Allah Kara kiyaye gaba " kubra dai ko kallonta Bata yi ba shine ya amsa.

Dan buzu ma na dariya Yana cewa"kubra masoyiyar Hashim sai hakuri,mitumin naku ne yayi kuskure ;ya Kira ni da Dan buzu gashi na jawo ya fada kwata Wanda hakan ya daga hankalinki ."

Hashim ne ya gyada Kai yace "zamu hade dai"
Kubra zatai magana ya Hana ta yace "haba sahiba kyale shi yaci bashi"

Hashim ya fito ta raka shi har wurin dakin su sanan ta dawo ta wuce su ummi,ummi ta zaro Ido ta juyo ta dubi Buzu"ka jamin wallahi"
Ya murmusa yace "rabu da su ,su suka sani"

Yau su mommy da Aunty mum tare da sauran yara gidan zasu dawo daga hutun da suka tafi na wata Hudu, kananan yaran an bar su wajen wata kanwar kakan su Najwa ,Bayan haka Kuma akwai yaran yan uwan Alhaji Usman da suke zaune a gidan ,akwai Kuma Wanda suka tafi hutu tare da iyalansa ,ita Kuma ummi a lokacin ne ta cika wata uku da zuwa gidan ,haka zalika yau ne Alhaji saminu da Hajiya samina masu gidan su kubra suka dawo Bayan duba lafiyar su day suka je yi ,saboda tun Bayan rasuwan Yar su wato zaliha wacce suke hi da ita ,sukan sami hawan jini ,yau dai gidajen ya kacame kamar sallah. Yau kam su ummi sun San iyayen gidan su sun dawo don ko sun Sha aiki .

A ranan ne kubra tace ma ummi "ke fa Dan takuran nan ya dawo"
Ummi tace "waye?"
Kubra tace "Fahad man dama ya bi su hajiya can ne don ya tabbatar da samuwan lafiya su kafin likita ya sallame su,to gashi yanzu ya dawo sai wani bubude hanci yake Yana wani harare_harare yake,Allah sa hajiya ta tsawatar masa ,hajiyan ma tace in dawo kusa da ita don jina take kamar yarta zulaikah, Murmushi take kawai don ta kwantar mata da hankali tare da cewa Allah jikanta yasa Aljannah makoma ,Ina g tana Shirin yin tunanin sai ince addu'a take bukat hajiya ,sai in dauko mata Al kur'ani ince mata ta karanta abinda ya sauwaka inyi ficewa ta in Bata guri."


" Kubra naji dadin yadda kike mata ,haka zai taimaka wurin samuwar lafiyar ta ,Allah biya ki ya barki da Hashim ." Cewar ummi

Ta kalkale da dariya tana cewa"kingan shi can wallahi ba Wanda Nike so kamar shi duk in ban ganshi ba ,nikan kwana cikin bacin Rai."

✍️ maiyamma's library.

KARKASHIN KASADonde viven las historias. Descúbrelo ahora