🔟

1 0 0
                                    

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

  *KARKASHIN KASA*

             *NA*

   *MURJANATU UMAR*

      
*WATPAD : MAIYAMMA*

  🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹🌹
         🥀🥀🥀

  KARKASHIN KASA
🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹
        🥀🥀🥀

         🔟

   Yau ne aka kawo sabuwar zuba ajin su ummi mai suna huda ;huda diyar wani attajiri ne  Amma ba irin mashahurin attajiran nan ba dai_dai ,ita dai Huda irin shagwababbun yaran nan sanan Kuma ita ce Auta ,akwai surutu har da na siyarwa da dariyar mungunta .Ranan da aka kawo ta islamiyar sai Kace faran shiga makaranta da kyar aka raba ta da maminta .

  Bayan mallam yace ta zauna a wurin ummi sanan yace ya mata kawa wato ummi,ta kalle ummi sanan Kuma ta bar kukan shagwabar yan aji wasu na dariya wasu na ta'ajibin gambasheshiyar budurwa da shagwaba,sai Kuma ta koma kallon ummi tana murmushi,ummi ta mayar mata ta dauke Kai. Mallam  ya fara karatu sai ita Kuma ta fara surutu karshe dai sai da mallam yai Mara kashedi sosai Tai Shiru.
  Da mallam ya gama karatu sai ya tashi wani yaro yace ya karanta abinda ya karanta yanzu ,budar bakin yaron sai yace
     " Mallam na manta "
  "Amma Kai sakarai ne ,ka wani bude baki galala kana kallon mutane."

Mai Huda za tai in ba dariya ba sai da tayi ma ishinta tukum ta tsaya.karshe mallam ya kora ta waje ,Bayan an gama aji mallam  yayi mata fada sosai sanan yace taje Tai sallah.

    Bayan ta idar da sallah sai ta kama neman ummi Bata ganta ba sai kawai Tayo aji ta iske ta a aji,ta karaso da sauri tace mata
" Ke Nike ta nema Ashe kina aji"

Ummi kam mamaki ya Hana ta magana ,ita da suka hadu dazu da ita .

  Haka dai ummi ta kasance da Huda tun bata kulata har dai suka kulla kawance ,wasa _wasa Huda ta koya ma ummi Shan ice_cream ,dariyan mugunta da kwalliya don har gida take biyo ummi duk da taga ummi Yar aiki ce Bata kaymace ta ba ,duk abinda ta sai ma kanta sai ta siyo mata Kuma ta koya mata yadda ake anfani dashi .

  Nan dai ummi ta Bata shawara Akan ta daina dariyan mugunta a gaban mallam da surutu karshe ta aminta ta Kuma daina.


  *Ayi hakuri da wanna sai mun hadu anjima*

✍️ *maiyamma's library*

KARKASHIN KASATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon