3️⃣

2 0 0
                                    

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

    KARKASHIN KASA

           NA

MURJANATU UMAR

   GODIYA:Ina godiya ga masoya littafin nan;yawan comment shi zai bani karfin Guiwa posting lokaci bayan lokaci

    Vote : watpad ; maiyamma

 

                3️⃣

    Anyi zaman makoki  an kare Bayan larai ta ma mallam Audu kazafi har ya zama ajalinsa bai isheta ba ,sai ta dawo kan Amina wai ita maiyya ce  zata cinyeta don ita ta lashe kurwan mallam Audu har ya mace to da yake kauye ne wasa_wasa Abu fa ya zama babba nan da nan gari ya dauka har iyayen sale sukai mai iyaka da ita Kuma sukai mai mata.

     Iyayen sale sun ja kunne sa da yayi nesa da ita in shi Dan halas ne .kada su sake ganinshi wurita ta.

    Gaskiya Amina Bata taba shiga damuwa ba irin wanan lokacin ,Tai kukan,Tai bakin cikin har Tai Rama kamar wacce Tai rashin lafiya na kusan shekara .

Ranan sai larai tace da ita ta fita daga gidan don Bata da gadon mallam Audu ,duk abinnan da akeyi mallam Ado bai dawo ba .A ranan ne ladidi ta biyo mata akan su je su karbi sakamakon jarabawar su ,a lokacin da suka fita ne suna hira ladidi ke tambayar ta wai lafiya taga tayi Rama ,sai tace"juyayin rashin kawunta mallam Audu take " sai ladidi ta bata shawara akan ta rinka yi mai addu'a ,sai Tai mata godiya.

   Sun karbo sakamakon Kuma yayi kyau .Sun yi sallama da ladidi ;ta wuce gida ita ma Amina ta juyo gidan su larai bata Gaya ma ladidi damuwarta ba ko niyyarta.

   Cikin dare ta fita Bayan kafa ta dauke tun kan gari ya waye  larai Tai mata korar wulakanci ;taci kuka sosai don tasan Tai bankwana da kauyen dabai ,ta yanki daji ta tafi can sai ta yanke shawara  ta samu wuri ta zauna ta huta to da yake barci barawo ne ya sace ta duk da tana tsoron dajin .

  
    Bayan ta farka ne taji Kiran asalatu daga can nesa  wato cikin gari ,tana ta addu'a ta kutsa Kai cikin dajin nan don Neman ruwan Alwala tayi tafiya mai nisa sanan ta samu ruwan Alwala Tai sallah .

    Bayan ta idar da sallah ne, ta kama hanya har ta bullo titi,ga shi har ta gaji  ga kishin ruwa ga Kuma uwa uba yunwa ,sai ta koma tafiya a hankali,Bata Ankara ba sai aka Sha gabanta da mota ,daga kan ta za tayi sai taga wani mutum bakikirin ,baki wuluk mumuna ya fito daga motar sai murmushi yake ya fito daga wanan motar Amma da ganin sa kasan akwai naira sai yace"Ina zuwa yan mata "
"Bansan inda zani ba" cewar Amina
"Me ya faru?"
"Makuwa nayi"

  Abin mamaki maimakon ya tambaya ta inda zata sai kawai cewa yayi "zo muje gidana ki huta sai in kaiki inda zaki"
Ita Kuma Bata kawo komai ba sai tace to

   Sunyi tafiya mai nisa har Zaria ita dai sai mamakin gidan da suka dosa take ,suna Isa yayi horn aka bude maigadi  ya tsugunna ya gaishe shi suka wuce ciki,Bayan sun sauka ne ,sanan ya shiga gaba ta bishi a baya ,suna shiga parlour yace "zauna nan Ina zuwa."

  Bata Musa ba ta zauna ,tana cikin kallon yanayin parlour da Yana yin tsarin gidan don ya birge ta ;tana cikin yaba parlour sai ta fara cin karo da da hotunan yan mata tsirara haihuwar uwar su,jikin ta ya fara bari tana cewa a zuci"Amina mai kikai yadda da bako baki San shi ba!"yunwa da kishin ruwa duk suka bacce ,saboda rudewa  kwata_kwata Bata San hanya da tabi ba Ashe ta bullo ta lambu gidan ne ,tana cikin tafiya da sauri ta hango wani dutse Wanda aka kawata a lambun da shi to da yake rainon kauye ce kawai ta haye ta danne bishiya ta dira ta Bayan katanga ta fita a guje har titi.

   Ta juma a titi Tai zaune abinta sai ga wata mota zata wuce sai ta ja ta tsaya wata mace ta fito daga cikin motan sai tace "lafiya?"
   Sai Amina ta fashe da kuka tace"don Allah ki taimake ni ko aiki zan dunga miki,wani ne ya sato ni ."
"Eyyah! Yarinya Ina da masu aiki,sai dai na taimake ki na maida ke gida"
"A'a iyaye na sun rasu ,uwar riko na kuma ta kore ni Kuma dama azaba take Hana min"

   "Ok zo muje zan taimake ki ko wani wuri ne in samo miki aiki Amma fa in kika yi rashin hankali korarki zasu yi nima zan Kore ki"

Amina tace taji zata kiyaye
   Akwai Amina ta bita basu zame ko Ina ba sai rigachukum.

✍️ MAIYAMMALIBRARY!

KARKASHIN KASAOnde histórias criam vida. Descubra agora