ZARAH MARWAHSHAFI NA BIYAR
Baffa ne Ya kalleta yace zarah marwah? " dago idanuwanta tayi ta kalleshi cikin kuka " Naam baffa." " nasan banida matsala dake kuma zaki zauna da khalid amana banason ki canza daga yadda kike kiyi hakuri akan duk abunda zakigani dan adam a jizine, kuma rayuwar nan komai tafiyarta watarana dole wanin mu yabarmu abunda hakuri bai bakiba rashinsa bazai baki ba, aure ibadane tsan tsa acikinsa dan haka hakuri shine kaɗai ke kaisa ga dorewa.
Cikin kuka ta kalli baffa tace "InshaaAllahu zaka same yadda kake tsammani kuma zanyi masa biyayya daidai iyawata nagode da dawainiyata dakayi ubangiji Allah yasaka da aljannah nagode baffa kaine duk gatana uwa uba."
Ameen zarah marwah kitashi kibi mijinki gobe zamu shigo abuja kuma duk wani abu da kike bukata nasa antynki tasiya miki Allah yayimuku albarka.
khalid ne yace" ameen tare da kallon zahrah takasan idonsa yana mamakin makirci irin nata acikin ransa yana fadin dubeta sai kace tagari.
Mota ce ta daukesu zuwa Airport ita dai zarah a hankali take dubansa yanzu ne tabbas taga tsantsan kamarsa da yaran baffa dan kuwa jini baya buya sai dai shi acikinsu gaskiya bataga yanada hayaniya ba.
khalid irin mazajen nan ne dogaye gashi baki yanada hanci sosai amma bashi da ido kana kallonsa zakasan bafulatani ne don kuwa baƙin nasa mai kyau ne kuma yanada manyan gabbai. Shine babban ɗa ga baffa kuma mahaifiyar sa ta mutu tun yana karami saboda abubuwna da suka dinga faruwa agidan da kuma harin saka masa guba da akayi har sau biyu yasanya mahaifinsa yabawa baffan sa shi anan cikin garin fellora komai baffansa wato mahaifinsa yakeyi masa hatta makaranta masu tsada yayi bayan yagama secondary yakai shi Egypt yayi karatu nan yakaranci bussines ad... bayan yadawo mahaifinsa yabasa jari inda yabude manyan kamfanin sabulai da alawowi sannan yana shigo da kayan kitchen da atamphophi daga daga waje..manyan kasa da yawa sun sanshi... watarana wani costumer dinsa alhaji bala yazo saran kayan kitchen nan yake bawa khalid labarin diyarsa da aboki ya yaudareta tabada budurcinta anan yake sanar masa shi tsine mata zaiyi ya huta, dan yarinyar tasa bakarmin magana take jawo masa ba.khalid jin wannan furucin yace Masa zaka auramin ita? Alhaji bala ne ya zabura tare da fadin haba khaleed me zakayi da ita kai da kamilallun mata ya kamaceka.. khalid yace masa alhaji zan aureta kuma zan rike maka ita amana.. Jin haka alhaji bala yace to nagode.. khalid yasanar da baffansa akwai yarinyar da yakeso nan aka kai kudi sunyi shagalin biki da babu inda ba'aji labari ba, aisha tana kaunar yarima kamar ta mutu haka sukayi aure tun daren farko ta fahimci yarima bashida kuzari nagaba yana hawa kanta yakawo wani lokacin sai yayi sati 1 zuwa biyu bai nemeta ba tundaga nan sai suka fara samun kalubale kala kala acikin zamantakewarsu gashi babu damar ta kashe aure dan mahaifinta zai iya yimata baki ta kara lallacewa hakan yasa tayi hakuri ta kauda kanta.
Aisha irin matan nan ne gajeru wankan tarwada ce amma kuma batada jiki siriryace itace auta agurin babarta mama tanada yayye 4 ita ta biyar secondary kadai tagama tun tana ss1 kawaye suke zugata akan tafara bin maza don hakan shine wayewar ,tun lokacin aisha ta dinga yaki da zuciyarta gurin ganin bata biye musu ba watarana wasu kawayenta guda biyu suka gayyaceta dinner ashe sun hada baki da nawwar wanda yake masifar sonta haka suka dinga rudarta har zuwa hotel cikin rashin sani ashe takawo kanta gurin da za'a rusa ta da rayuwarta haka nawwar yayita kokarin ganin yayi lallata da'ita..
Aisha tashiga bala'i bakarami ba inda ta hadu da tsangwama da kyara da kuma wulakanci gurin yayyanta har iyayenta...
Bayan khalid ya aureta bayan shekara da aurensu ta tabbatar khalid rago ne a harkar aura tayya hakan yasa suka fara samun sabani da juna tun bai gane ba har yazo yafara ganewa..
Watarana khalid yake bawa abokinshi labari abokinsa yace ya nemi magani mana khalid yace shi lafiyar sa kalou haka rayuwa tacigaba tun abun baya damunsa har yafara damunsa yaje yasiyo magunguna yafara sha ...

YOU ARE READING
GIMBIYA SUHAYLA
عاطفيةWANNAN LABARI YANA MAGANA AKAN KALUBALE NA MA AURATA AWANNAN ZAMANI TARE DA KAUNA DA HADARIN MUGUNTA GA TSANANIN SOYAYYA GA KUMA RUDIN SHAIDAN DA KUMA ILLAR RASHIN SAUKEWA JUNA HAKKINSU DA MA AURATA SUKEYI..