🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*NA YARDA NA MUTU*
*2020*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*HAFSAT A GARKUWA*_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN🚴🏻♀️'''_In the Name of Allah the most Beneficient the most mercifull praise be to Allah lord of the words._
*Wannam Labari mai suna NA YARDA NA MUTU, NURUDDEEN ne ya koma shi, saboda anyi book mai irin sunan shiyasa ni kuma na mayar da nawa NA YARDA NA MUTU.*
*01*
*FEDERAL TEACHING HOSPITAL GOMBE**……* Safa da marwa take tayi a cikin Asibity in da mutane da dama ke ta hidimarsu Wasu na Kuka wasu kuma na jimamin abunda ke faruwa dasu, domin duk wanda ka gansa a wannam Hospital ɗin ba daɗi ne ya kawosa ba akasin haka ne, haka ma ita Wannam Budurwar sam hankalinta baya jikinta, kana kallonta kasan da akwai abun da yake damunta matuƙa, dan tashin hankali ne ɓaroɓaro akan fuskarta, Agogan dake farfa jiyar Falon Asibityn ta kalla, nam taja tsaki dan Lokacin bai mata gudu ba, haka tayi ta zagaye a wajen har sai da taji Agogo ya buga 12:00am dot, da Sauri ta ƙarasa wani ɗaki dake rufe wanda aka rubuta *Tiata Room* da manyan baƙi, Wani kyakykyawan Saurayine Dogo Fari sol bashi da ƙiba sosai Fuskarsa ɗauke da Sexy Eyes mai matuƙar ɗaukar hankali hancinsa dogo mai haɗe da ɗan ƙaramin bakinsa mai kalan Pink Sajene kewaye a Fuskarsa, Kayinsa cike yake da gashi wanda yake sheƙi sak na Fulani wanda yasha gyara, Girarsa cike yake da gashi tamkar na Mace, yana sanyi da Koren Kaya wanda yayi matuƙar amsar jikinsa, Sanyi yake da takalmi sau ciki Fari irin na shiga Tiata, Fuskarsa sanye take da Glass ɗan madaidai ci Fari, Sai dai kawai muce Masha Allah, dan iya haɗuwa wannam Guy ya kai, da sauri wannam Budurwa tayi kansa tace "Yallaɓai ya jikin ƙanwar tawa? ta faɗa cikin matuƙar tashin hankali, Ɗan girgiza kai yayi yace "I'm Srry"sai dai ayi haƙuri Allah ya amshi abunsa, Ai wani irin damƙa ta masa tare da kwarma uban ƙara tace "Wallahi ƙarya kake yi, wallahi sai ka fitomin da ƙanwata Allah bazan yarda ba taya zaka ce ƙanwata ta rasu, Oh dama abun da yasa aka ce dole sai nam zan kawota saboda dama ku samu damar kasheta to wallahi bazan yarda ba sai kun fito min da ƙanwata, Cikin matuƙar ɓacin rai ya ɗaga hannu ya wanka mata mari ji kake Tass!!! da sauri ta dafe ƙuncinta cikin Maganarsa kamar ta ɗan koyo yace "Ke dan ubanki ƴar gidan uba waye ce ke da har za kici kwalata kina min iskanci, ku dama talakawa haka kuke matsiyata kawai, to bari kiji ni da kika ganni na tsani talaka ban so ya raɓeni ko waye, wannam aikin da nayi ma a ƙyanƙyani nayi sa saboda talaka ce futun ƙazama kuma, dan haka maza kije ki ɗauketa ki bar Hospital ɗinnam da ita, Ai wani kukan Kura tayi ta ƙara chakwameshi tare da kai masa mari, bayan tatattaro yawun dake bakinta ta zuba masa a fuska tace "Kaji matsiya ce, kai ma dukiyar da kake da ita ba wai Allah ya fi sonka bane ya baka A'a sai don ya gwada Imaninka dan haka ka sani wannam dukiyar da kake taƙama da ita watarana baza ka ganta ba, kuma sai kayi ladamar abun da kamin ka rubuta ka ajiye ni Nauwarat sai kazo ka durƙusa gabana kana roƙan na yafe maka, abunda kamin a lokacin kuma Lokaci ya ƙure maka banzaka kawai, nam ta daka tsaƙi tayi wucewarta, nam Mutanam da suka taru a wajen suka fara watsewa dan yau sunga abunda yafi ƙarfinsu Yaron da yake matuƙar ji dakansa yau shi aka yiwa haka lalle akwai aiki akwai ƙura, haka suka bar wajen suna ya maɗiɗi da shi, Wani Saurayi wanda yake sa'an wannan Matashi da sauri ya ƙaraso inda yake yace Nuruddeen mai yake faruwa haka? Uban wa ya zuba maka miyau a fuska? Kaga maza muje Office, nam ya jashi shiko haka yata binsa zakaɗai zakaɗai da Alamu babu nutsuwa a tattare dashi, haka har suka ƙarasa Office ɗin Nuruddeen, Shi kansa Office ɗin ma abi kallo ne balle ko azo kan mamallakin wannam Office ɗin, tsayawa faɗa muku yadda yake ma ɓata Lokaci ne...
YOU ARE READING
NA YARDA NA MUTU
FantasyLabari ne mai matuƙar taɓa zuciya da kuma tsantsar soyayya...