🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*NA YARDA NA MUTU…!*
*2020*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*HAFSAT A GARKUWA*_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻♀️*05&06*
*NURUDDEEN POV*
*……* "Wai dama a garin Gombe akwai kyawawa har haka? "Uhum Malam Nuruddeen kenam ai Gombe garin kyawawa ne matuƙar a garin nam kake to sai dai ka bawa wani labari, ta faɗa tana dariya, "Kai gaskiya ni kam ban taɓa ganin mai kyau a garin nam kamarki ba, Abokina ko kai ka gani? Nuruddeen ya faɗa yana taɓo Kamal da yayi mutuwar zaune jin ƙaryar da Abokin nasa yake bugawa, nam yace "A'a banga wata mai kyau ba bayan Amaryata sai kuma ita wannam ya faɗa yana dariya, Nuruddeen yace "Wallahi ƙarya kake Gimbiya ce farko ita Amaryar taka ta biyu daga baya, kaji ɗan iskan mutun ya faɗa yana dari, ita dai gaba ɗaya sun bata dariya, dan taga alamama mutanene masu barkwanci haka suka ta zuba shaƙiyancin su ita ko tana faɗa musu inda zata a wani makeken gida tace su tsaya, Nuruddeen Hamdala yayi dan yau ya samu Macen da ya daɗe yana muradi Ƴar manya kamarsa ga kuma kamun kai ba yawon ta zubar, Fitowa suka yi tace gamu mun iso nam shine gidan mu nagode muku sosai Alah ya saka, "Ameen cewar Kamal yana murmushi, har ta juya zata tafi Nuruddeen yace "Am… baki ji ba, juyowa tayi murmushi yayi yace baki faɗan sunanki ba, "Sunana Salma ta faɗa a takaice, "Wow! nice name saura Number, "Kuma du ta faɗa da alamun wasa, murmushi yayi sannam yace "Eh ko bazan samu bane Gimbiya, "A'a mai zai hana Sardauna, Dariya suka saka duka nam ta ƙarɓi no ɗinsa ta saka masa ta ƙira sannam ta miƙa masa sallama suka yi, Kamal dai kallonsu kawai yake dan yaga alamu Abokin nasa ya gama tafiya, motar ya shiga cikin farin ciki ya tayar suka ɗauki hanya a Lokacin har ana Sallar Isha'i Kamal ne yace "Oh su Abokina an faɗa tarkon so, "Uhum kai dai Abokina ba'a magana dan tayi mugun kwanta min Yarinyar daga gani akwai Tarbiya a jikinta, "Babu laifi kam cewar Kamal a haka suka ƙarasa ya ajiye Kamal sannam ya nufi gida cikin matuƙar farin ciki, Sai da ya tsaya a massalaci yayi Sallah sananmmya shiga gida, ko da ya shiga ba kowa a falom hakan ya bashi damar shigewa Part ɗinsa, yana zuea ya faɗa toilet wanka yayi sannam ya sanya kayan bacci ya feshe jikimsa da turare masu matuƙat ƙamshi, yana wannam yanayin yaji wayarsa na ƙara kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauko yana duba Screen ɗin yaga New Number ya yawo a kai, Murmushi yayi dan kallo ɗaya ya gane mai No ɗin dan tana bashi baiyi Saving ba ya zira aljihu, kwantawa yayi a gado sannam ya ƙirata, da Salama ta fara da muryarta mai daɗin sauraro, nam yaji kasala ta mamayesa da ƙyar ya iya amsa mata, nam tace dafatan kun isa gida lafiya? "lafiya ƙalau wallahi ya faɗa a taƙaice nam tace "Dama na ƙira kane dan na maka ban gajiya na gode sosai, "Auya ba komai mun iso lafiya dan har na kwanta ma, "To sannunka na gaisheka sai da safe, daga nam ta katse wayar, Sam bai so ta kashe wayar ba dan muryarta ta masa daɗi sosai haka dai yata saƙe saƙe da yaga hakan bazai kaisa ba ya kwanta dan yana da aiki sosai gobe a Hospital…*3weeks later*
*NAUWARAT POV*
Zaune take tayi jugum dan tun wannam ranar da Ammi ta mareta ta rasa tunaninta dan abun yayi matuƙar bata mamaki abun ka da ba sabon ba, hakan yasa bata ƙara cewa komai ba ita ma Ammin bata ƙara magana ba talaucin da suke ciki ma ya ƙara ninkuwa fiye da da dan yanzu in har sun samu sunci so ɗaya a rana tofa shine cinsu da yawa daga ita kuma sai waje gari in an samu, yanzu haka zaman da take na jiran Baba ne in yazo ta sanarda sgi shiɗin ko zai yarda, tana wannam tunanin sai ga sallamarsa cikin murna ta taresa Ammi dake ɗaki ma ta fito nam suka baza taburma rogo ya samo musu, a haka suka cita ba tare da haɗi ba suka kora ruwa a kai, sai da ya ɗan tsirga musu Nauwarat tace "Baba dama ina so na maka wata magana ne amma ina jin tsoron kai ma hukuncin da zaka yanke amma wannam hanyar zai taimaka mana matuƙa gaya, Murmushi Baba yayi yace maza faɗa min ina jinki matuƙar hanyar bai saɓawa addini ba kuma zai cire mu daga wannam ƙangi to ba shakka zan amince, Ammi sai da gabanya ya faɗi tana so ta yiwa Nauwarat magana amma taga ma sam ƙasa take kallo, cikin sanyin murya Nauwarat tace "Dama Baba Jummai ne tazo tana yiwa Ammim mu tallan Aikatau ko za a turani domin ya rufa mana asiri duk da ban san a ina bane amma dai nasan a tsukin mun nan ne, kuma nasan ba kwana zan nayi ba jeka ka dawo ne,Baba dan Allah ka amince duk da ko a mafarki ban taɓa mafarkin zanyi aikatau ba hasalima na tsani aikatau, amma wannam shine kawai mafita tunda bamu da jarin da zamu kama sana'a kaga in nayi ko na shekara ne sai na ajiye sannam mun samu jari shikenam mu kama sana'armu hankali kwance, haka tata tsarasa jikinsa yayi matuƙar sanyi amma dai yasan wannam hanya itace mafita a garesu, nam ya nisa yace "Duk naji maganarki Nauwarat Allah ya miki albarka zamu tattauna da Amminki duk yadda muka yanke za kiji, "To Baba Allah yasa naji alheri, bari naje gidan su Siddiqa "To shikenam ki gaida su sai kin dawo cewar Baba , Ammi da murmushi ta bita duk da taba jin haushin abun da ta aikata dan ko za ayi yaya baza ta bar tilon ƴarta ta tafi wani aikatau ba…
YOU ARE READING
NA YARDA NA MUTU
FantasyLabari ne mai matuƙar taɓa zuciya da kuma tsantsar soyayya...