Page 11

28 2 0
                                    

*NA YARDA NA MUTU…!*
*11*

*NURUDDEEN POV*

*…* Cike da matuƙar mamaki da firgici yace "kece? uban mai ya kawo ki cikin gidan mu? Ok rashin kunyar da kika min da fitsara bai isheki ba shine har sai kin tako ki zo gidan mu, to wallahi yadda kika shigo ɗinnam bake ba fita dan sai na shayar dake azaban da baƙi taɓa riskar irinta ba. da sauri Nauwarat da ta gama daskarewa a wajen hannunta ƙafe yake tana nuna sa dashi da ƙyar bakinta ya buɗe ta furta kai ne?,"A'a ubanki ne bani bane, kuma wallahi kika yi yinƙurin yin wani abu sai na taka ki, talakar banza talakar hofi shi yasa nace duk matsiyatan nam, sai sun bada kan su saboda kuɗi, in ba haka ba mai zai kawo ki aikatau gidan masu kuɗi, maza ɓacemin da gani, in da nasan ke kika dafa abincin ma babu abunda zaisa naci nonsense, ya doka uban tsaki tare da barin wajen cike da matuƙatr ɓacin rai ji yake kamar ya shaƙeta a wajen ta mutu waje ya fito ya faɗa motarsa ya bata giya ya fice 360 ya nufi Hospital…

*NAUWARAT POV*

Tun da ya fara magana taji ƙirjinta yana mata wani irin bugawa musamman da ya furta cewa, suna bada kan su saboda kuɗi, tabbas ko giyar wake nake sha bazan taɓa bada kai na akan abun duniya ba, hawayene ya zubomun masu matuƙar zafi da ƙuna, ji nayi wani abu na taso min a ƙasan maƙoshi na, nace dole a yau na bar gidan nam domin bazan iya aiki a gidan su wannam jahilin da bai san darajar ɗan adam ba wallahi dole yanzu na bar gi… "A'a Nauwarat karki yi haka don Allah muje ɗaki muyi magana, Muryar Kaltume naji a gefena da alamu dai a fili nayi maganar ba a zuciyata ba, hanuna ta kama muka fara tafiya, ɗakina muka shiga ni dai binta kawai nake ina zubar da hawaye masu matuƙar zafi,kan gado ta zaunar dani sannam ta zauna riƙe hannuna tayi, na bita da kallo tace,"Nauwarat duk da ban sani ba nasan tabbas akwai abun da ya taɓa haɗaku da Yallaɓai wan da sam ban so hakan ba, amma in da hali zan so ki faɗa min abun da ya haɗa ku ko ma samu mafita, kima ajiye wannam zancen da kike na cewa zaki bar gidan. Murmushi nayi sannam nace "tabbas akwai abun da ya haɗa mu dashi, domin kuwa bazan taɓa mantawa ba, dan gani nake kamar shi ya min ajalin ƙanwata Shukrah nam na zai yane mata duk abun da ya faru ina kuka domin ji nayi mutuwar Shukrah ta zamo min sabuwa na ƙara da cewa, tun daga wannam rana naji duk duniya babu wanda na tsana irin sa, ban taɓa tsanar mutun ba amma naji tsanar Nuruddeen ya ɗarsu a zuciyata har sai  da Ammi tamin faɗa akan tsanar da na masa babu kyau sannam na haƙura na manta da babin sa a rayuwata duk, amma duk lokacin dana tuna Shukrah sai na tuna sa, a haka na manta da babinsa har sai yanzu dana gansa komai ya dawo min, dan haka bazan ƙara ko da kwana ɗaya ba a yau zan bar gidan nam kuma bari na har abada. "A'a Nauwarat kar kiyi haka ki sani wannam ita ce hanyar cin abincin ku daga ke har ahalinki in ko kika bar gidan nam baki san wani gida zaki faɗa ba, tabbas Mutanen gidan nam sunƙi jinin talaka, Hajiya ce kawai take da ɗan son talaka amma daga Abi Mamy da sauran Yaran gidan gaba ɗaya sun tsani talaka ya raɓe su sam basa ganinsa da daraja. Wayar falon ne ya katse musu hiran da sauri Kaltume taje ta ɗauka, ba aji mai aka ce a ɗaya ɓan garen ba tace "to gata nam zuwa, da sauri ta dawo ɗakin inda ta barta a nam ta sameta tace "Nauwarat kije falon su Mamy tana son ganinki yanzu maza miƙe kije. da to ta amsa mata sannam ta fito cikin sassarafa da Sallama ta shiga falon inda ta hangi Mamy ta hakimce akan kujera cikin shiga ta Alfarma sai kuma su Nuriya da suke cin abinci cike da santi, risinawa tayi tace,"Hajiya ina kwana? Mamy ba yabo ba fallasa ta amsa mata tana ɗan yasina sannam tace "Dama na ƙira ki ne dan na shaida miki Jummai ta faɗi irin ƙuncin da kuke ciki a gidan ku hakan yasa na ɗibi komai na abinci aka aika musu tun daga kan Shinkafa taliya da dai sauransu, wani irin Sanyi naji da sauri nace "Hajiya Allah ubangiji ya saka miki da gidan Aljanna, Allah ya baki abun da kike nema duniya da lahira, Allah ya dauwamar dake a cikin farinciki, Mamy taji daɗin Addu'ar susai hakan yasa cike da fara'a ta amsa mata da amin, sannam tace 'Maza ki haura ki fara yin aiyukan ki,"To tace ta tashi tana shirin haurawa, Nuriya tace "Ke Village girl!!! da sauri na tsaya gabana na faɗuwa a hankali na juyo nace "Ni?,"A'a ba ke ba cewar Nuratu tana galla mata harara, ƙarasawa nayi inda suke na risina, ceke da tsiwa Nuriya tace "ke wai ke kika dafa wannam abincin? cikin sanyin murya nace "eh nice.,"A ina kika koya girki haka? Nuratu ta jefo mata tambaya "A wajen Ammi na na koya, cike da zaƙuwa na faɗa musu dan sun fara isata, Nuratu tace "Okay za ki iya tafiya. Sim sim na miƙe na haura ɗakin Mamy na fara zuwa babu wani gyara na azo a gani nam da nam na kammala na nufi ɗakin Nuruddeen ɗakin yayi matuƙar birgeni dan sai tashin ƙamshi kawai yake a gyare yake tas kamar babu wata halinta dake rayuwa a ɗakin, kawai ɗan karka ɗe wajajen nayi dan kar dai ace banyi bane amma babu datti turaren ɗaki na kunna sannam na rufe na nufi ɗakin su Nuratu a nam ne naga a hargetse da alama in suka cire kaya basa adanawa ko ina suka samu zubarwa suke, a nam ne na ɗan ɓata lokaci kafin nam fito, ko da na fito ba kowa a falon hakan yasa na nufi ɗaki na, na faɗa gado ina sauƙe ajiyar zuciya da tunanin zuwa anjima zan waske gidan mu…

*SARAH POV*

Tunda ta isa gida take tuna wannam Guy ɗin dan yayi matuƙar tafiya da imaninta, suna shiga ɗakinta ta shiga wanka ta faɗa sannam ta fito ta sanya ƙananan kaya maras nauyi duk da batayi kwalliya ba tayi kyau sosai gwanin sha'awa, gado ta faɗa cike da nishaɗi wayarta ne tayu ƙara alamun shigan saƙo da kamar baza ta duba ba sai kuma da ta ɗauka buɗewa tayi ta fara karanta Text ɗin kamar haka '''"Assalamu Alaiki ya ma'abociyar hankali da sanin ya kamata, ɗunbin gaisuwa na tatttara na dunƙule na turo miki da ita, fatan lafiya kike hutunki gida tare kuma da jin daɗinki, ina fatan komai yana lafiya, kasancewarki cikin kwanciyar hankali da jin daɗi shine babban abin fata a gareni, zamantowarki mai farin ciki da ganin saƙona shine abin alfaharin zuciyata, ke nake kallo na samu sauƙin ciwon da zuciyata take yimin zan so na zama mai kula da martabarki gami da kare miki duk wani mutuncinki, ina sonki.'''
*Zahid💕*  tashi nayi na zauna cike da mamaki dan ni dai ban san shiba sunan na ƙara maimaitawa *Zahid* so cute suna yayi to amma ina ya samu no ɗita kai mutane ma akwai shirme wayar na ajiye na saƙƙo ƙasa a nam na samu Anty Ramlat  tana cin abinci zuwa nayi na hau nace "Anty ki samun abincin, harara ta galla min tace "bazan saka ba in baza ki saka da kanki ba shikenam. ɓata fuska nayi cike da shagwaɓa nace "Allah bazan ɗiba ba ke zaki saka min na ƙarasa ina bubbuga ƙafa cike da shagwaɓa, murmushi tayi sannam tace "to rigimammiya bari na saka miki karki haɗa min gurmi wajen Mommah dan na sanki indai wajen sharri ne kinfi kauri ta wajen, dariya nayi nace "eh ɗin a dai saka min yasin ko na fasa ƙwam, miƙo min tayi tace "gashi nam jarabbabiya wallahi Sarah ki rage munafinci Allah ba abu mai kyau kike ba ni dai ina gaya miki ki dunga jin tsoron Allah ato ni dai ba ruwana."kai Aunty Allah ni fa ba abun da nake wai sai kice ina jin tsoron Allah to tsoron wa nake ji in ba nashi ba, ai kawai dai ayi harka kawai ato, yauwa Aunty ni kam ki tambaya mana Abu ya barmu muje gidan Hajjo wallahi nayi missing ɗinta in dai Mommah ne nasan zata bar mu amma Abu in ni na tambaya wlh bazai barni ba dan ba sona yake ba, kamar ba shi ya haifeni ba duk yafi sonki Mommah ne kawai take sona, ta ƙarasa tana kukan shagwaɓa. Ramlat tace "Uhum Sarah kenam wallahi Abu yana sonki halinki ne baya so saboda kima abu kamar ba ƴar gidan nam ba sam kin fita zakka a gidan nam wlh in da zaki gyara halinki za kiga yadda Abu zai ƙaunace dan Abu yana sonki sosai ko yanzu ma so ne ya jawo abun da yake miki, dan sai ana sonka za a gaya maka kuskuren da kayai...,"yanzu kina nufin Mommah ba sona take ba kenam? na faɗa cike da shagwaɓa, murmushi Ramlat tayi tace "ko ɗaya ban gaya miki ba Mommah tana sonki amma sonda take miki ya wuce shari'a dan ta sakaltaki sosai kuma…"Ke Ramlat da sauri suka juyo suka kalli inda akayi ƙiran…

*AMMI POV*

Zaune take tana cin Shinkafa da taji haɗi jelof ne sai tashin ƙamshi take, daga jiya zuwa yau sun wadatu da abinci a dalilin Nauwarat tana ci tana mata addu'a tare da saka mata albarka Sallama taji da sauri ta amsa, tare da fitowa wani ɗan saurayi ta gani risinawa yayi ya gaida ta sannam yace "ko nanne gidan su Nauwarat da take aiki a gidan Hajiya Zainab? Ammi sai da gabanta ya faɗi cike da tsoro tace "eh nan ne lafiya kuwa?,"lafiya ƙalau dama Hajiya ce ta aiko ni da kayan abinci take a kawo muku zan iya shigowa dashi? ajiyat zuciya Ammi tayi tare da hamdala tace "eh zaka iya shigowa dashi. fita yayi nam suka fara shigo da kayan abinci niƙi-niƙi shida wani da alamar tare suke, Ammi daskarewa tayi a wajen ganin uban kayan da aka liggo musu katon katon buhu buhu nam da nam ya cika tsakar gidan, sai da suka gama suka mata Sallama godiya ta musu sosai sannam ta aikawa da Hajiya nata gdy zama tayi a gaban kayan tana riskar kuka kamar an mata mutuwa.a haka Baba ya shigo ya sameta da sallama ɗauke a bakinsa ganin yadda Ammi take kuka ne ga wasu kaya da ya kasa ganewa ne sallamar ta maƙale Ammi da sauri ta tashi ta faɗa jikinsa ta ƙara sakin wani irin kuka, ka sa daurewa yayi da jin Kukanta yace "wai miye ne kam Aysha dan Allah ki faɗi min kin saka ni cikin duhu. share ƙwalla tayi sannam ta zai yane basa komai, wasu Hawayen farin ciki yaji ya wanke masa fuska ƙara rungumarta yayi suka cigaba da kuka gwanin ban tausayi,sai da suka gaji dan kan su sannam suka sarara cike da matuƙar farin ciki suka fara duba kayan suna saka musu albarka tare da sawa ɗiyarsu albarka, a nam suka ware wa Jummai na ta dan duk abun da suka samu ta sanadiyar ta ne, nam suka fara tattare kayan ɗakin Nauwarat suka tara kayan saboda yana da yawa sosai, bayan sun gama ne tun a lokaci Baba ya yanka musu kaji guda biyu dan guda Ashirin Hajiya Zainab ta aiko musu, nam da nam Ammi ta hura wuta ta girka musu tashi ɗaya gida ya ɗauki ƙamshi, ci suka yi suna tuna Nauwarat dan sun sam ita ma yanzu tana cin fiye da abun da suke ci yanzu dan yadda suka ji labarin gidan a wajen Jummai sun san ɗiyarsu zata huta, Baba ne yace "yanzu  bari na taro miki Napep sai kije ki kaiwa Jummai nata tare da ɗan ɗaukanin nam da muka yi, da to ta amsa masa shi kuma ya fita, tashi tayi ta shirya ta zubawa Jummai, nam ya dawo ya fitar da kayan ya sanya mata a Napep ta fito ya mata Allah ya kiyaye suka tafi shiko ya shigo cikin gida cike da farin ciki, yana shigowa gaban sa nw yayi mummunar faɗuwa…
*Wannam book ɗin na kuɗi ne duk wanda ya gansa a waje to na sata ne, dan haka ki garzayo ki saya ki karanta cikin aminci.*
08132761212

NA YARDA NA MUTUWhere stories live. Discover now