Page 8

30 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*NA YARDA NA MUTU…!*      
            *2020*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
      
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

*SADAUKARWA*
'''Darling'''
_Wannam page ɗin naki ne sai yadda kika yi dashi, ina miki son so fisabilillah_💋🤞🏻

*08*

*NURUDDEEN POV*
*……* Mamaki ne yayi matuƙar cikashi da jin zancen Abokin nasa, shi dai a iya saninsa tun lokacin da aka haɗa su da ƴar uwarsa za a musu haɗin gida yace baya so, tun daga lokacin bai ƙara yin zancen  buduwarwa ba, sai yanzu kuma yazo yace har an gama komai saura zancen aure, tabbas da wani abu a ƙasa anya ba da junnu suke soyayyar ba? dan shi a iya saninsa Kamal bai taɓa soyayya ba dan in yana yi ma shi zai fara sani sai kuma gashi ana zancen wani aure, dole na duƙufa dan ganin na gano gaskiyar lamari dan kar abu yazo yayi nisa sai anzo a kasa shawo kan lamarin, dan daga zancensa ma kasan ba shi kaɗai bane akwai wani abu, ko Aljanace ta auresa, a hankali zai gani komai, haka yayi ta saƙe-saƙen hanyar da zaibi dan ya zaƙulo gaskiya.
*3 months later*
Rayuwa yake cikin izza da taƙama, baya barin bashi matuƙar an taɓa sa sai dai wani abu ɗaya har yanzu hana riƙe da abun da Nauwarat ta masa sai dai bai san inda zai ganta ba, nam ya yanke zai je ya duba file ɗin majinyaciyar da suka kawo akwai Address ɗinsu, tsakanin sa da Salma kuwa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakamin su dan kusan du sati sai yaje gidan su, yau ya yanke hukuncin zai sanarwa gidan su domin ayi komai a gama dan a matse yake… da sallama ya shiga gidan, gaba ɗaya suna falo cikin murna suka amsa masa, nam iya isa ya zauna kusa da Hajiya wacce take ta masa tsiya tana "Oh su gauron gidan nam an kasa yin aure ƙila sai ƙannensa sunyi aure har sun haihu kafin yayi, cikin farin ciki yake "Hajiya kenam kwantar da hankalin ki san yanzu maganar da nazo yi kenam, nasan daga yau gori kuma ya ƙare ato, ya faɗa yana zungurin kanta, Hajiya kamar jira take tace "kaci gidan ku ni kake zungurew kai? ashe ko ka zungumi Zainabu, amma dai kaci sa'an wannam Albishir da kazo mana dashi, Nuriya da Nuratu cikin haɗa baki suka ce "Hamma Allah yasa dai ƴar babban gida ka samo mana kuma kyakykyawa? suka faɗa cike da ɗoki, Mamy da bata ce komai ba sai yanzu tace "Yo dama in ba ƴar gidan maya bane shima yasan wasa yake ammm in ƴar gidan manya ne ai abu yayi dai dai, Abi ne yace "to yanzu dai duk ku tsaya muji ta bakinsa ya bamu labarin duk abunda ke faruwa,"Yauwa Abi ashe ka fahimta suko da yasa surutu garesu basu tsaya sun saurarenba, Hajiya ne ta ɗaga masa duka tace "to muna jinka mai gidan tunda za a min Kishiya ai ba nutsuwa kuma, gaba ɗaya suka saka dariya… Nam ya nisa yace '''"Yanzu watan mu biyar da ina sunanta Salma gidan su yana nam a Federal locost gida mai lamba 2 gidansu gidane babba na nuwa sa'a da ka ganta kasan yadda gidan su yake dan ita kanta kalar manya ce, shiyasa nace bazan yi sanyaba sai nazo na sanardaku domin a tambayomin''' "Yeeeeeee!!!! su Nuratu suka zuba ihu cike da murna da jin daɗi, Hajiya ko guɗa ta saka Abi yace "To Alhamdulillah! insha Allah zuwa gobe zan saka kawunan ka da baffaninka suje su tambayo maka dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, Mamy tace "Aiko dai haka ne Abunsu gwara ayi da wuri gaba ɗaya suka amsa da amin, Nam suja fara zolayarsa ganin abun yayi yawa ne ya miƙe dan shi mutun ne dai bai cika son hayaniya ba, yana hauwara ɗakinsa ya shiga  yana zuwa ya cire kayansa ya saura daga shi sai gajeran wando toilet ya faɗa ya sakewa kanshi ruwa, bayan ya fitone ya sanya jallabiya wanda yayi matuƙar yi masa kyau Maroon colour gado ya faɗa ya ɗauko wayarsa ya latsa no ɗin *My Heart* bugu biyu ta ɗauka, bayan ta masa ban gajiya ne yace  "kinsan miye ma kuwa? cikin farin ciki ta zaƙuwa tace "A'a sai ka faɗa, murmushi yayi kamar tana gabansa yace "Gobe za azo a nema min Aurenki, Salma duk da baya gabanta sai da taji mummunat faɗuwar gaba, nam ta dake tace "kai haba wai da gaske?,"Uhum ke dai kawai ki sanar a gida domin su sani dan in sun zo baza su tafi ba har sai an saka ranar Aure, ni da son samu nane ma ace a ranar za a ɗaura ki tare a gidan ki. ya faɗa cike da buƙatuwa da kuma shauƙi, Zaro idanu tayi tace "What? kana nufin a gobe a ɗaura ni gaskiya ban shirya ba, ta faɗa kamar za tayi kuka, dariya yayi mai sauti yace "dama ao nafi sonki a kan ki, na san inda nineva madadin ki zan ce a ɗaura mana amma ba komai kamar yau ne dan nace kar su saka da yawa duk yawansa bazai wuce wata biyar ba,"Haba Deen wata biyar ai yayi kaɗan ina laifi shekara ni gaskiya ban yarda haka ba, Hamma ransa ne yaji ya ɓaci jin abunda take faɗa cikin faɗa yace "wai Salma mai kike nufi ne? wai shin anya ma kina sona? in har kina sona bai kamata ki faɗi haka ba in baki sona tun farko ki faɗa mim kar abu yaxo ya ƙara nisa kuma ya zama wani abu abun da kika nuna min hakan ya nuna baki ƙaunata dan haka kije kawai na nemi wata. ya faɗa tare da kashe wayar ya cillata gefe yana wani irin huci.

NA YARDA NA MUTUWhere stories live. Discover now