Page 10

38 2 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*NA YARDA NA MUTU…!*      
            *2020*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
      
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀

_Daga wannam Free page ya ƙare sai kuma mun haɗu a Paid grp._🙌🏻

*Last Free page*
*10*

*JUMMAI POV*
*……* Da sallama ta shiga gidan, Ammi dake zaune tana tankaɗe gari da taji muryarta sai da gabanta ya faɗi nam ta dake tace "A'a Jummai kece a tafe lalle marhabun yanzu nake shirin in na kammala naje na same ki, iso ga taburma, ta faɗa tana nuna mata kusa da ita, murmushin jin daɗi tayi ta ƙaraso ta zauna nam suka gaisa Ammi tace "dan Allah kiyi haƙuri akam abun da na miki wallahi rai na ne ya ɓaci da lamarin kinsan talaka dama zuciyarsa a kusa take, dariya Jummai tayi tace "wallahi ba komai ai komai ya wuce a waje na sai dai a kiyaye gaba, Aisha ina so ki saurareni ki jini da kunnen basira ki kuma fahimce ni, wallahi bani da niyar cutar daku daga ke har ɗiyarki, illa alheri da nake neman ku dashi, wallahi ina matuƙar tausayawa rayuwar da kuke ciki, nima bani dashi amma gwara ni sau dubu tunda bani da miji bare kuma ƴa ina da ɗan sana'ata ta isheni har zuwa lokacin da zan samu miji, amma kefa gaki ga miji ga kuma ɗiya, amma kuma babu jarin yin sana'a kinga dole ku tashi tsaye ku nema wallahi, shiyasa na baki wannam shawaran dan ita ce hanya mafi sauƙi da zaku rage wani abu naku, tunda ba wata kadara ko kaya kuke dashi ba, gidan nam ko baza ku sayar dashi har ku samu na jari da kuma na kama haya ba, in har kin yarda da batuna a tsukin anguwar masu kuɗin nam sai mu nemi inda za a ɗan ɗofana ta domin ku samu taro sisi, wannam shine abin da na ƙara zuwa miki dashi, Ammi nisawa tayi tace "to Jummai banvtari numfashinki ba amma ina ɗan tsoro dan kinga wasu masu kuɗin sai a hankali,"karki damu insha Allah sai munyi bincike sosai kafin mam fatan mu dai Allah ya tsare kuma yasa su karɓeta hannu biyu,"Amin dai kam cewar Ammi tana jajanta abun tace "nagode sosai Jummai bari Malam yazo na labarta masa duk da sukam sunyi na'am dama ni ne nayi ja akai ta faɗa tana ƴat dariya, Jummai ya miƙe tace "insha Allah baxa kiyi kuka akan haka ba ni bari na wucr sai naji ta bakinki daga nam zuwa gobe sai mu fara nema ko?,"Eh to shikenam sai kin jini nagode, daga gaka Jummai ta fita cike da fatin cikin amincewar Ammi.

*ABI POV*

Cike da matuƙar mamaki yace "wai ni yaron nam mai yake nufi da haka ne? yana nufin ya fasa auren kenam? Hajiya tace "yo ga alama amma dai wannam yaro anyi ja'irin yaro ɗan iska sai dai ya gama lasa mana zuma a baki sannam yace baza mu sha ba, ko dama dai ƙarya ya rangaɗa mana ne,"Ai ba hala ma ma Ƙaryarce kawai, cewar Mamy da take a fusace,"kai amma Hamma Nuru bai kyauta mana ba, har muna shirin fara shirye-shiryen biki a she ta malle ya mana, cewar Nuratu tana dariya, Nuriya tace "ni dai ban ga alamar da wasa yayi ba da gaske ne amma akwai wani abu a ƙasa,"kaga ja'irar yarinya dama ai bakin ku ɗaya dashi, Abi yace "bari dai mu jirasa ya dawo muji dalili dan nasan yanzu ko na ƙirada bazai ɗauka ba bare kuma yazo amma abun da bam mamaki wannam shine ta leƙo ta koma gaba ɗaya suka saka dariya.

*NURUDDEEN POV*

Yana fita bai zarce ko ina ba sai wajen Kamal yana zuwa ya faɗa masa duk abun da ke faruwa tare da ƙudirin sa, da mamaki Kamal ya kallesa yace "haba abokina kar ka ɗauka da zafi mana, ka sani shi so ya gaji haka, kuma baka san dalilinta na faɗar hakan ba da ka tsaya ka saurareta ƙila ma wasa take maka,"wallahi ba wani wasa da gaske take dan ba alamar wasa tattare da maganarta kawai fa ni na haƙuri dan na gaya wa su Abi ma karma gobe suje dan ko sunje ni dai na fasa eheee, ya faɗa da yanayin ko oho, dariya Kamal yayi yace "to mu dai bamu fasa ba domin ina bayan Salma dan Allah ka nutsu ka fahimce ni, nasan yanzu ka bar su Abi a zullumi dan Allah na roƙeka a matsayi na na abokinka amininka kuma ɗan uwanka in ka koma kacewa su Abi wasa kake baka fasa ba, kar ka faɗi komai da ya faru hakan shi zaisa suje da ƙarfin su kaji, ni kuma zan samu Salma naji mai ke faru dan Allah, da to Hamma ya amsa masa amma bai gama gamsuwa ba, sai kusan 9 sannam ya taho gida, a falo ya samu Hajiya da Mamy su ka ɗai, gaishesu yayi babu wanda ya kulasa, ya gane dalilinsu na ƙin kulashi dariya yayi yace "oh akan wata bare ahalina sun shareni to bari dai kuji ni wasa nake ban fasa ba, cike da farin ciki suka kallesa Hajiya tace ",ko kai fa ɗan albarka kace kawai dama ɗumama mana ciki kake so kayi,"kai amma wannam yaron Allah ya shirya mi kai, muryar Abi suka ji yana shigowa falon daga waje, dariya yayi yace "ai naga daga faɗa muku kun zaƙu da yawa ne shiyasa na sake muku gwiwa, Mamy tace amma sai navi gidan ku ta miƙe tana ƙoƙarin kamosa ya gudu, Abi yace "ko kaifa bari naje na ƙira iyayenkan a waya gobe da anyi i'sha sai suje ya faɗa yana taka step, Hajiya ne taje ta gayawa su Nuratu ihu su zuba cike da murna suka fito suka rungumesa suna dariya gaba ɗayansu.
*Washe gari*
Da dare su Baffa isah da Kawu Sale suka je neman Auren Salma vikin girmamawa Alhaji Abubakar ya karɓesu bayan an cike musu gaban su da kayan ciye ciye, bayan sun gaisa ne suka zo masa da buƙatarsu daga jin sunan mahaifinsa ya gane mutanene masu matuƙar mutunci da karamci nam aka bashi har aka saka rana nam da wata biyar masu zuwa in Allah ya kai, Kuɗi suka bayar dubu ɗari biyu na nagani ina so da ƙyar Abba ya karɓa suka rabu cikin aminci, bayan sun dawo ne suka fa ɗawa Abi duk abun da ya faru gdy ya musu sannam ya ɗan basu wani abu, shiga yayi ya sanarwa su Hajiya sunyi murna sosai, Nuruddeen tun jiga Salma take ƙiransa amma sam yaƙi ɗauka duka da yana jin ba daɗi a ransa dan basu saba ba, har yanxu da Abi ya shigo sanar dashi sai ƙiransa take amma yana gani yayi banza, nam Abi ya sanar dashi ya fita dan yaga alamun soyayya ɗansan zai buga.

NA YARDA NA MUTUWhere stories live. Discover now