Page 4

46 2 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*NA YARDA NA MUTU…!*     
            *2020*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
      
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

*04*

*SARAH POV*
  
*……* Wallahi kin kawo shawara ƙawata, wai kamar Aunty Ramlat ta rasa wa zata so sai Malaminta gashi kuma ƙungurimin talaka, wallahi ni dai na wuce tsaran Talaka mai kuɗin ma sai asalin mai kuɗi ba mai amsa sunan mai kuɗi ba, nifa a tsarina da Abi zai barni banyi Aure ba wallahi ina so dan sam bana son harkar takura, sai kiga Namiji yayi Aure sai waina matarsa yake kamar waina a tanda, in har zata fita sai ta tambaya in ko yaga dama yace baza ta ba ga girki ga wata uwar, Taɓ Yasin banda Sarah dan ni in har ni  in ka aureni tofa ba kai ne Mijin ba nice, ta faɗa tana wani yayyarfa hannu tare da yatsina fuska hakan sai yayi matuƙar ƙara mata kyau, Husnah ce ta sa dariya tace "Kai Besty baki da kyau wallahi, shiyasa nake ƙara sonki a ko da yaushe saboda komai namu iri ɗaya ne, "Aiko kuna tare da wahala in dai wannam rayuwar kuke tsarawa kanku dan Aure ana yinsa ne dan ka samu Aljannarka,  ku ko naga Alama dan ku samu wuta kuke so kuyi Auren, Ramlat suka ji tana faɗar haka juyawa suka yi suka ganta tsaye ta harɗe hannu tana kallonsu da Alama tun tuni take tsaye a wajen taci gaba da cewa "Kuma ku sani har yanzu baku san wa zaku Aura ba gwarani ma akan ku wallahi, dan haka ina mai baku shawara tun wuri ku farka daga magagin baccin da kuke ku gane gaskiya,da talaka da mai kuɗi duk Allah ne ya haliccesu kuma duk ɗaya suke a wajen sa sai dai wanda yafi tsoronsa, "Kai Aunty mufa ba wani abu muka ce ba kawai hiran mu muke, cewar Husnah tana shagawaɓe fuska, "Ai ki barta kaeai Besty shiyasa sam ban so nayi wata magana a kusanta yanzu sai ta hau mutun da wa'azin da duk sai yaji gaɓansa sun amsa wallahi, cewar Sarah tana hararan Ramlat da alamun wasa, Ramlat ta shigo ta haye gado tana cewa "Ni dai na faɗa muku ku dinga yi kuna tsoron Allah ato ni kunga nayi nam Asuba ta gri, daga haka tayi Addu'ar bacci taja blanket, cikin shaƙiyanci suka ce "To mun gode Auntyn mu amma tabbas sai mun gayawa Mommah abun da ke sakaninku da Malam Ahmad, ai da sauri Ramlat ta miƙe tace "Dan Allah kun san halin Mommah sarai wallahi zata sa Abi ya koresa dan Allah kat kumin haka wallahi ina matuƙar son Ahmad kuma shima yana sona ta faɗa kamar za tayi kuka dan tasan halin Sarah sarai zata aikata, Murmushi Sarah tayi tace "To shikenam bazan faɗa mata ba ai dole ya suki tunda yaga daukar da kike ciki ta faɗa suna tafawa da Husnah, "Ramlat tace  eh naji nagode hakam ma, daga haka ta kwanta suma shirin bacci sukayi kowa ta kwanta a gadonta dama gadon guda Huɗu ne a ɗakin.
*2weeks later*
      Sarah a kullum da wukaƙanci da take ma samari duk wanda yazo mata sam bata masa tarbar arziƙi, musamman in taga yanayin shigarsa, yau ma kamar kullum zaune suka a wajen shaƙatawa ita da Husnah da Ramlat, wani Saurayi ne yazo tare da musu Sallama, Ramlat ne kawai ta amsa masa a cikinsu tunda suka masa kallo ɗaya na ƙasƙanci suka ɗauke kai, Ramlat ne tace "Malam lafiya? Murmushi yayi yace "lafiya ƙalau wallahi dama ƴar uwarki na gani tun da na ganta naji ta kwanta min, "Wa kenam a cikinsu? ta faɗa tana nunasu, "Wannam dai wacce ta fiku kwarjini da kuma haiba, ya faɗa yana nuna Sarah, da sauri ta ɗago ta kai masa mari ji kake fau!!! tace "Malam kai jahikin ina ne duk wajen nam ka rasa wacce zaka ce kana so sai ni? kaga nayi maka kama da kalarka ne, kana nam ƙazami dakai kace wani kana sona, to bari kaji wallahi ni ba sa'ar irin ku bace wallahi nafi ƙarfin kace kana so na dubeka fa dan Allah Wawa kawai ƙazami, daga haka taja tsaki tabar wajen cikin takunta mai matuƙar jan hankali, shiko bawa Allah tunda ta fara masifa ya cika da matuƙar mamaki bai ɗauka sam bata da tarbiya ba, duk da kana kallonka kaga mai ji dakai amma baza ka zata tarbiya ya mata ƙaranci ba, Husnah ma bita tayi a baya, Ramlat ne tace "Dan Allah Malam kayi haƙuri da abun da ta maka, Murmushi yayi wanka yafi kuka ciwo yace karki damu ba koma duniya ce, daga haka ya shige ya bar wajen, mutanen da suka tsaya suna kallonsu  kowa da abun da yake faɗa akan Sarah wasu suce ta burgesu wasu kuma akasin haka, duk Ramlat tana jinsu cikin haushi itama ta juye ta tafi a mota ta samesu, Shiga tayi ta zauna a maxauni Direba ta tada motar ta ɗauki hanya suna cikin tafiya tace "Sarah yanzu abun da kika yiwa wannam bawan Allah kina gani kinyi dai dai kenam? Karfa ki manta shi fa ɗan adam ba abun wulaƙantawa bane saboda watarana zai iya taimakon ka, wallahi kibi duniya a sannu dan naga ke da mugun zafi kika ɗauketa, wallahi kibi a hankali domin baki san waye shi ba mutun ne ko Aljan duk baki sani ba,  "Kai Aunty ya zaki sako Aljani a cikin maganar dan Allah ki dai na saka Aljani dan ina mugun tsoronsu, Sarah ta faɗa tana shirin kuka, "Dole in saka miki Aljani mana dan naka iskancin kin yayi yawa wallahi kuma duk lefin Mommah ne da take ɗaure miki gindi kike yin duk abun da kika ga dama zance na faɗa mata in ko bata ɗauki mataki ba na sanarwa Abi, ",Ni ko na sanarwa Mommah tsakaninku da Malam Ahmad cewar Sarah tana dariya, Husnah tace Besty ni kai na yau kin ƙureni duk da abun da kika yo shi ne dai dai amma yayi yawa Yasin, "Ke dahalla ki rufe min baki munafuka ai gwara ni ma ke da kika gwale wannam Alhajin fa, dariya suka saka duka, Ramlat ta girgiza kayi tace Allah ya shiryeku wallahi…
      A haka suka ƙarasa gida, mai aiki kawai suka samu a falo Sarah cikin ɗaga murya ta kalli mai Aiki tace "where is Mommah", Mai aikin cikim sauri tace "she is in her room, "Owk da gudu ta fara haurawa Step sai suka yi kiciɓus da Mommah tana sauƙowa cikin shiga na alfarma rungumarta Sarah tayi tace, "miss u Mommah, "Me 2 My Baby", Kun dawo tun ɗaxu nake saka ido sai yanzu "Eh Mommah yunwa nake ji ta faɗa cike da shagwaɓa, Mommah tace maza je ki watsa ruwa ki fito kici ko Baby na, ta faɗa tana lakatan kumatunta, "To Mommah na daga haka ta shige, Mommah ƙarasowa tayi inda su Husnah suke zaune tace Yarana kun dawo 'Cikin haɗa baki suka ce "Eh Mommah sannu da gida, "Yau ta faɗa tana zaunawa, Ramlat ne tace "Mommah a gaskiya kina yiwa Baby faɗa wallahi bata ji tana wulaƙanta mutane ba dama mutun yace yana sonta shikenam wulaƙancim ta zai fara, "To! to!! zaki fara ko? Uwar sa ido wallahi Ramlat kinn da gulma to duka duka nawa Babyntawa take da za a mata wani zance na daban shima maganinsa da ya kulata, dafatan dai ta kifa masa mari, "Kai Mommah ai mari mai lafiya ya masa cewar Husnah tana dariya, "Yauwa ta min daidai ɗiyar albarka cewar Mommah tana dariya ita ma, "Wallahi Mommah sam abun da kuke ba mai kyau bane gaskiya taya na kawo miki laifin ƴarki maimakon ki ƙirata ki mata faɗa shine zaki ƙara ingiza lamarin, "Kinci gidan ku Ramlatu ni kike faɗawa haka anƙi a mata faɗan ki ɗau mataki ja'irar Yarinya kawai, ai Mijin da Baby zata aura na musamman ne wanda duniya babu inda ba'a labarinsa dan haka tun wuri ki kiyayeni a to, Ramlat miƙewa tayi ta nufi ɗakinta dan zancen ya fara ɓata mata rai, Mommah ta bita da harara.

*AMMI POV*

     "Masha Allah Jummai wannam wani irin Hanya ce da kike tunanin zamu samu mafita cikin sauƙi, "Akwai hanya mai sauƙi wanda in har kun bi za ku fita daga wannam yanayi da kuke ciki insha Allah cewar Jummai tana kallon Nauwarat da ta kasa kunne tana jiran abun da xata ce, Ammi tace "Jummai maza ki faɗa min dan Allah na zaƙu naji wannam hanya ta ina zata buɗɗe, "Uhum Ƙawata kenam ba ko ina bane illa a kai Nauwarat Aikata zaku samu matuƙar Alfanu za kuma ku fita daga cikin… "Dakata Jummai wannam wani irin rainin hankali ce Ɗiyartawa zan ɗauka na kai wani aikata,dan baki da mutunci ai gara mu zauna yunwar ta kashemu da na kaita aikata, cewar Ammi data matuƙar fusata, Jummai ne tace "Haba Aisha wannam ita ce hanyar data dace kubi domin ku fita daga wannam ƙangi… "Ke Jummai fitat min daga gida ko yanzu na baki mamaki wallahi zaki fita ne ko yaya?, "Lalle Aisha zan fita miki a gida amma ki sani wannam ita ce hanyar da za kubi dan ku kuɓuta, "Wai baza ki fita ba kenam? Ammi ta ƙara fusata tayi kanta da sauri Jummai ta fice dan taga alamun Ammi kamar ta samu matsala, Nauwarat ne ta riƙota tace "Ammi dan Allah kiyi haƙuri ni ina ga zancen Jumman nam akwai ƙanshin gaskiya, Ammi cikin matuƙar ɓacin rao ta ɗaha hannu ta wanke Nauwarat da mari ji kake Fau!!! da sauri Nauwarat ta dafe wajen cike da matuƙat mamaki dan Ammi bata taɓa ɗaga hannu ta daketa ba amma sai gashi yau ta tafka mata mari lalle abun ba sauƙi, cikin fushi Ammi tace "Wallahi in kika ƙara cewa wani abu akan maganar nam sai nayi mugun saɓa miki taya zan ɗauke ki na kai ki aikatau da hankalina da tunani na sam hakan ba mai yuwa bace, ɗaki ta shige a fusace, Nauwarat zama tayi tare da shafa inda Ammi ta mareta dan ya shigeta sosai…

*NURUDDEEN POV*

      A hanyarsu ta komawa gida ne, a gefen Titi suka hangi wata Budurwa a jikin mota sai tsaƙi take da alamu ɓaci tayi motar, Kallo ɗaya Nuruddeen yayi mata yaji ta kwanta masa, da sauri ya samu waje yayi parking cikin Mamaki Kamal yace "Lafiya kuwa? mai za mu tsaya muyi? Nuruddeen bai tsaya bashi amsa ba ya fito cikin takunsa na ƙasaita ya isa inda take da Sallama ɗauke a bakinsa, Kamal ganin haka yasa ya fito ya kalli inda Nuru yake mamaki ne ya kamasa ganin yayi wajen wannam budurwa murmushi yayi tare da gyara tsayiwa dan yaga abunda zai faru, Cikin ƙosawa Budurwar ta amsa masa tare da cewa lafiya? "Eh lafiyarce ta kawo haka, na ganki ne kamar kina cikin matsala shiyasa na tsaya ko zan iya taimaka miki, taji daɗim hakan sosai nam tace "Eh wallahi ina cikin tafiya ne motar tawa ta samu matsala gashi ana ta jirana a gida, ta faɗa kamar za tayi kuka  "Murmushi Nuru yayi yace "Ayya ai tsiyar nasara kenam, in ba damuwa kizo muje na kai ki gidan in yaso ko daga baya kya turo mai gara ya ɗauka, "A'a Malam ai bazan ɗaura maka ɗawainiya ba daga haɗu, "Sunana ba Malam ba sunana Nuruddeen ya faɗa yana Murmushi, "Yi haƙuri Nuruddeen ita ma ta faɗa tana dariya, nam yace a amshi tayina dan Allah, "Tom shikenam nagode ba komai nam ya tafi tabi bayansa baya ya buɗe mata yace Bismillah ba musu ta shiga Kamal ma zama yayi shigo ya shiga maxaunin direba sun fara tafiya yace "Ginbiya ina muka nufa? "Taɓ wace kuma gimbiya ban kai nam ba Federal locost zamu nufa ta faɗa a taƙaice "An gama ranki shi daɗe…



_Amma ta Hanyar Nuna min Ƙauna da Soyayyarku wajen Siyan *NA YARDA NA MUTU...!* Akan Naira 300 kachal👌🏻Vip 500 ta wannam Account Number, 0134205910 HAFSAT AYUBA UNION BANK, sai ki turo shaidar biya ta wannam Number 08132761212 ko Katin waya na MTN, shima sai ki ɗauko hoton Katin a Turo kai tsaye ta wannam Number 08132761212 ga masu saya na farko zasu samesa a 200 Vip 400 sai kunzo Masoyana._

_Kada fa ku manta Akwai Garaɓasa na mai son siyan Biyu *IZAYYAH (Return)...!*  Shima Dai nawa ne a 400 Vip 500 ne Kachal👌🏻 Shima ta wannam Number Account ɗin da na bada da Number Wayan ta Sama ko Kuma kai Tsaye ku Tuntuɓe ni ta wannam Number domin ƙarin bayani._
08132761212

*HAFSAT A GARKUWA CE*🤙🏻

NA YARDA NA MUTUWhere stories live. Discover now