Page 13

73 5 3
                                    

*NA YARDA NA MUTU…!*
_19_
*BONUS!!!*🤾🏻‍♀️

'''Kuyi haƙuri da jina shiru kwana biyu, hakan ta faru ne saka makon rashin da aka mana, nima nazo na kwanta a asibity dafatan zaku min uzuri, ina muku son so fisabilillah.'''

*SARAH POV*
*…*  Husnah maza muje gashi nam yazo yana ɗakin baƙi, murmushi Husnah tayi tace "yasin bazan je ba karki manta yau ne fa zaku fara haɗuwa dan haka ke kaɗai zaki jeki, kuma sai wani sauri kike ya kamata ki ɗan ja aji mana. dariya tayi tace "lalle baki da hankali wani jan aji zan tsaya mutumin da na jima ina son gani kice in tsaya wani jan aji nikam kin ga tafiyata, ta fita tana wani irin taku, a falo ta samu su Mommah da Ramlat, da sauri ta ƙarasa gaban Mommah tace "Mommah ki ganni nayi kyau ko? ta faɗa tana wani karairaya, murmushi Mommah tayi tace "kinyi kyau sosai ɗiyar albarka maza kije yana jiranki. Ramlat ta kalla tace "Anty Ramlat yau kuma M ɗin ne ya motsa da baza ki iya cewa nayi kyau ba? ta faɗa cike da shagwaɓa. dariya Ramlat tayi tace "to  Baby Mommah kinyi kyau sosai ai kyan da kika yi ne ma yasa ba kasa magana jeki maza yana jiranki. "yauwa ko kefa Anty Bye sai na dawo. fa faɗi haka tana ficewa cike da takunta mai matuƙar ɗaukar hankali. a hankali take tafiya har ta isa babban falon baƙin, da sallama ta shiga zaune ta ganshi a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin, ɗago kansa yayi idanunsu suka sarƙe suka gauraya da juna, wani irin Shu'umin kallo suke aikama junansu ganin yayi mata wani irin kwarjini ne yasa tayi saurin janye idon ta daga nasa, Sanye yake cikin wani ɗanyen boil ash color wanda yayi matuƙar yi masa kyau, babu hula a kansa sai tukun gashi irin na bulani, hannunsa sanye yake da agogo na gold sai sheƙi yake zubawa, ƙafarsa sanye take da takalmi na fata, wanda ya ƙarawa ƙafarsa kyau, kallon farko ta ganesa, shine wanda yazo School ɗinsu wajen ta, fa bashi No ɗinta akan zai zo suyi magana bai zo ba, ashe suna tare dashi bata sani ba, hamdala tayi wa ubangiji dan tun ranar farko data ganshi taji ya kwanta mata a rai, bare kuma yanzu da ta sake ganinsa, sai taji kaf duniya bata da wani zaɓi in ba shiba, ɗaya kujeran dake kusa da nasa taje ta zauna, gabansa cike yake da kayan ciye-ciye daban daban, Murmushi tayi tace "dama kai ne ka wahalar dani, tun tuni ina jin ƙishirwar ganinka? "Ai nine na jima ina jin ƙishirwar ganinki sai yau Allah yayi zan ƙushi sosai da ganinki, ykk? yasu Mommah? hope kowa yana dai lafiya ko?. ya faɗa yana binta da wani shu'umin kallo, "eh duk suna nam lafiya lau, ya hanya dafatan ka iso ƙalau? "lafiya lau na iso cike da zumuɗin nazo naga abar ƙaunata. da sauri ta rufe idanunta da alamun kunya sannam tace "wai dama kai ne ka ta wahalar dani tun tuni? "Sorry Sarauniya ta dafatan za amin afuwa Ok?. murmushi tayi tace "ai dole na maka afuwa, domin in ban maka afuwa ba ni kai na bazan yafema kai na ba, haka suka ta hira kamar sun daɗe da sanin juna gaba ɗaya cikin farin ciki suke da walwala bai tashi tafiya ba sai ƙarfe 9 na dare, sai da ya shiga ya gaida su Mommah sannam ya ɓata tsarabarta su sweet da Ice cream da Cake tarkace dai na maƙulashe, gdy ta masa sannam suka rabu cike da shauƙin juna, gida ta shigo tana murna ba kowa a falon hakan yasa ta haura sama a nam ta tarar da su Husna da Ramlat, da murna ta shigo ta rungumi Husna tace "Besty wlh na samu Mijin da na daɗe ina mafarkin samu, domin kuwa *My Zahid* ya haɗa komai da na ƙudira mijina ya kasance,  Allah ya cika min burina, dariya Husnah tayi tace "To a gaskiya na taya ki murya Allah ya kai mu ranar biki. "Amin amma ko kinsan ma waye ne? ina wanda yazo School ya sameni na masa kwatancen gidan mu, to shine dai ashe *My Zahid* ɗina wlh nayi farin ciki sosai dana ga shine. "gaskiya Bestie na taya ki murna sosai, Allah ya samu a danshin ki. "Amin dai Bestie, wai Anty Ramlat baza kice komai bane? Sarah ta faɗa cike da shagwaɓa. "Sorry Babyn Mommah ina tunanin My Ahmad ne shiyasa dan Allah kisa Mommah ta dawo dashi kinji? yadda kike farin ciki nima ki saka ni farin ciki, ta ƙarasa faɗa kamar za tayi kuka dan a duniya babu wanda take so kamar Ahmad, Sarah ta tausaya mata sosai dan ada bata san mai nene so ba amma yanzu kam ta sanshi farin sani, dafata tayi tace "Anty ba sai na faɗawa Mommah ba kice ya dawo kawai mu cigaba da Karatun mu, cike da murna Ramlat ta rungumi Sarah tace "nagode sosai Baby bari naje na ƙirasa Allah ya barki da *Zahid* ɗinki, ta faɗa ta fita a guje. murmushi Sarah tayi tace "amin Anty Ramlat ɗina, kema Allah ya barki da Ahmad ɗinki duk da talaka ne, dariya suka saka ita da Husna dan tuni Ramlat ta jima da barin ɗakin, ledar ta buɗe musu cike da tarkace har leda biyar, ci suka farayi suna cikin ci suna hira wayar Sarah tayi ƙara alamun shigowar text da sauri ta ɗauka ta buɗe saƙon Zahid ne nam ta fara karantawa kamar haka '''"Aslm Sarauniyata dafatan kin shiga gida lafiya? dan hakan shine fatana, ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar zuma suke ma'abocin zaƙi, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya naji ina sonki. sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! kin kuwa san menene dalili? saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa dasu, yau ganin ki da nayi ji nake tamkar kar mu rabu, domin a yanzu ji nake munyi kusan shekarun ban ganki ba,''' *ina sonki da zuciya ɗaya Zahid💞.* Murmushi tayi mai sauti, ji take duk duniya babu wacce tayi sa'ar samun Abokin rayuwa kamarta, a duniya babu abun sa tafi so irin kulawa tare da kalamai masu sanyaya zuciyata, cike da nishaɗi ta fara kai da masa kamar haka _"Bana tunanin zuciyata zata iya aiwatar da wani abu batare da tunanin ka ba, domin kai ne hasken da ke haskaka mata hanyar samun jin daɗi da annashuwa. samun ka a rayuwata tamkar samun dukanin farin ciki ne gareni, *Ina sonkane tsakani da Allah Sarah💕.*_
   Cike da murmushi ta kammala ta tura masa, sannam ta kalli Husnah tace "wlh Bestie ban san haka soyayya take da daɗi ba sai yanxu, ashe da duk hauka muke, gaskiya soyayya akwai daɗi. dariya Husnah tayi tace "Soyayya akwai daɗi kam wlh domin nima a satin nam na faɗa kawai dai ban sanar miki bane. dukan wasa Sarah ta kai mata tace "kut kina nufin kin faɗa soyayya amma shi ne baki sanar min ba, wato kin rama abun da na miki ko?."Oh ashe kin tuna nima ai baki faɗa min ba sai da kika gama lulawa duniyar masoya sannam kisa sanar min dan haka kinga yanzu anyi 1-1…

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 06, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NA YARDA NA MUTUWhere stories live. Discover now