03:Best friend

1.6K 192 15
                                        

♡TAKAICIN WASU
03.please vote ok
Cikin shigarta na Omo Blue prison uniform riga da wando da yadin dankwalinta madaidaici babu design ko kwalliyar komai sai katoton badge din central prison din dake manne daff da kimtsatsen kirjin ta,kayan ya mata matukar kyau duk dama fusknta tayi fayau kamar marar
Lpyar datayi jinya na shekaru sama da ashirin.

Har yanzu kuka takeyi zuciyan ta na mata suya mai tsanani Ita kanta wafiyya bata san kalar kukan datakeyi din ba dan sosai tasa komai acikin ranta aynzu.

Bakin ciki mai tsanani shiya ke ratsa Cikin kowani kiftawar dakika dake tafe da saukar numfashin ta, Har yanzu bata saka a ranta cewa zata iya rayuwa babu danta nashwan ba,abun da ya zarce so shi takeyi ma danta,that clouded and unxplainble feeling na tsananin kauna wanda ko ta rarrabashi a zuciyan ta bazai fassaru ba.

Aganin ta tanayi ma nashwan Irin son da mijin ta yay mata ne koma rubinsa,..
hakeem ya sota sona bilhaqqi dan tunda ya same ta gidan marayu ya zame mata uwa uba miji gata sannan ya bata dukkan rayuwar sa,ko sau daya bai taba sata kuka ba bare kunci.
He spend his life loving nd worshiping her ita da dansu kwalli daya wanda ayau takeji kamar babbar butulci ta aikata ma mijintan data bari aka raba ta dashi.

His words were more than clear to her ayayin daya umarceta data kare musu dansu ta rayasa karta barsa duk rintsi duk wuya amma meyafaru ayanzu?wasu Sabbin hawayen da suka fi kowanne rauni kwayar idanun ta suka sake ayayin da duk gabobn jikin ta dana zuciyarta suke tuhumarta da laifin gazawa da cin amanan mijin ta mayor alhakeem wamako

Cikin wani daki mai dauke da gadon yan boarding schl up and down bunk guda biyu aka tura ta ciki, ko daga kai batayi ba ta sulale kasa kan gwiwarta ta fashe da wani marayar kuka mai gigita kwakwalwa.

Duk surutayya duk tsawa da tsiwan inmate dinta baisa ta dena kukan ba bare ta dago kanta dan kansu suka gaji sukayi shiru suka tsura mata idanu suna kallon ikon Allah,numfashi taja can ta yanki jiki ta fada kasa"
Suma tayi?

Wacce ta taba gefen wuyar ta ta furta..

Su uku ne a dakin wafiyyar ce na hudu,biyu ne akanta suna surutun,na ukun tana zaune shiru a saman gadonta atakure batace da su uffan ba har wafiyya ta farfado.

Tsintar kanta tayi akan motsatsan katifan ta wasu munanan mata guda biyu na tsaye akanta cikin uniform din waden.
Wanda Tun kan ta gama dawowa hayycin ta suka tursasa ta taci abinci,kuma tun data fara ci suke mita suna kashe mata gargadi kala kala while ko kallo itakam basu isheta ba

Daga nan Dabiarta na shiru shiru da tsinannen zurfin ciki kyaliya da  rashin sabo saima abunda ya karu.

Babu ta inda matan dakin tan basuyi ba amma wafiyya macece wanda basu taba ganin irinta ba,hafsa da jennifer sune masu surutun maimoon itace shiru shiru mai lura da komai sosai da alaman suma bawai sun dade anan din bane.

Aganin su wafiyya is mentally rertaded,
Bata da lpyar kwakwala dan babu mai halayya irin nata face me ciwon kwakwalwa.

Yau kwanan ta goma sha takwas amma Ko sau daya bata taba ce musu cikanku ba bare ta musu kwakwaran kallo haka zasu karaci magana tsiwa watarana harda zagi saidai suna muugun shakkar tabata dan har yau basu san me zata iya yi musu ba.

Duk abunda take bukata zata fita ne dakanta ta duba kota nemosa awani wajen ita sam babu ruwanta da kowa da komai,she will spend her nigh praying tana mika kukan ta ma ubangij i sauran lokutan kuwa zuciyan ta acike yake da tunanin rayuwarta da danta nashwan kan kace wani abu wafiyya tayi suna a cikin prison bana waasa ba.

Kowani daki akanyi gulman yanayin ta,har aka samu tsageru da suke so su mata duka koda zasu maidata baiwar su cikin su harda jennifer da hafsa.

Ana cikin hakan ranar aiwatar da hakan ya zo,rana ne na labour so acan filin dake bayan dutsen dake bayan prison aka watsu su,duk an shirya kallon drama amma bazaka kalle wafiyya kace tasan me sukeyi bama,she is totally absent minded duk yawan yan prison din nan har yau bata kama fuskan kowacce ba bare muryanta duk da hakan yau da aka fito da su dukan su saitaga yawansu bai wani bata tsoro ba kwata kwata bazasu fi dari biyu ba.

TAKAICIN WASUOnde histórias criam vida. Descubra agora