9:

1.2K 113 13
                                    

*♡TAKAICIN WASU🌺*
_the destiny untouched.._

   _A nigerian historical fiction_           _*WATTPAD SURAYYAHMS*_  
  _Brilliant writers association_

    
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

*9...motive*

Kwance tashi har labarin abunda ya faru da nashwan a kauye ya soma shafewa dan anan southong mansion bakaramin babbaka shiri akeyi ba,kan hanadi is already on fire dan bayan hamshakan mutanen da mahaifiyar ta ta gayyato daga fashion world an kuma tabbatar mata da cewa familyn babban abokan gaban su zasu zo.

Wato familyn BOSS OMAR KHALEEPHA Da dan uwan sa UNCLE BRAHIM Khaleepa tare da sangartattun yayan sa wayanda suke saoin juna da su hanadi wato NAIL KHALEEFA and NALA KHALEEFA.

A duniya in akwai wayanda hanadi ta tsana to wayannan mutanen ne,uban ta mayor Aseem shine mai dukiyar amma tafishi jin kishin duk wanda yake takun saka da shi.

Boss khaleepa irin murdaddun business men din nan ne masu tsananin iya makirci,mugunta zurmammen zuciya da kwadayi amma ance matar sa honourable bahijja mace ta gari ce a wajen haihuwa data haife yan biyun ta namiji dana mace Allah ya karbe ranta inda boss khalepar ya sa musu suna nail da nala,tsawon lokaci yana zama da su tare da kanin sa brahim dan yace shi bazai sake aure ba.

Haka nan yaran sa suka girma agabn sa da bro dinsa a sangarce basa jin magana sam,babu tarbiya bare addini.

Bincike ya tabbatar ma mayor Aseem cewa Boss khalefa ne mahandamin daya zauna akan sauran burbushin arzikin mayor wasim kaita dana matarsa bahiyya.

Abun a fili yake dan boss khalepa yana da alaka mai kyau da manyan hakiman gwamnati marasa gaskiya so duk anbi an rufa masa asiri an maida sunan sa akan qaddarorin mayor wasim in no time so shiyake rike da yankin west  ayanxu anan ma tsohon mansion din wasim din..."castle hill masion"..aka rusa aka gina masa nashi gawutacen gidan inda ake kira da "the sand castle'
Kuma Tsakanin castle hill da sand castle ba asan wanne yafi tsaruwa.

Hanadi dai ta tsane su kamar mutuwar ta,tsanar nata ma irin wanda baiya boyewar nan,she literally cant stand them musammn ma macen wato nala khaleefa data fito boro boro a media tace ma duniya ta na mutuwar son nashwan hakeem wamako kuma tun ranar hanadi ta sa mata kahon zuqa da mummunan karar tsana.

all thy life basa iya jure zaman lpya a tsakanin su,tun akan maganan arziki suka fara dan banzan competing da juna suna caccakar juna suna buga kishin jahilci sannan duk abunda daya tayi sai daya tayi wanda ya fishi kayan sawa gwalagwalai  motoci da jirage kwarkwasa da kwalisa abun ma har ya zama kamar zasu illata kansu dan yau idan hanadi taje plastic surgery aka ja kumatun ta to gobe zakaji nala taje anja goshin ta.

Sai kamannin dirin halittar su ya dawo kusan daya xak zak dukan su in sun bada baya bazaka ma tantance ba sai dai wanda sukeyi dominsan bai ma san sunayi ba
But is still to nala's advantage dan sosai yake kawance da ita,nashwan yana son kula nala sosai sabida arayuwa yana son abinda kowa baya so a familyn sa kuma yakan tsani abunda kowa yake so a familyn hakan tasa hanadi bata iya daurewa in nala tana waje itama tana nan to dole ne suyi fada.

Fannin nashwan kuwa tunda incident din kauyen nan ya faru yakejin kamar wani abu yadan sauya ajikinsa amma rashin bada muhimmcin ma abu naturen sa ne so baima bada hanklin sa wajen son ya gane komai ba,kwana biyu kawai dai zaka gansa so quiet kuma baya son shiga hayaniyar jamaa,sau dari za'a aje abinci a dinning dinsa sau goma za'a dawo a kwashe bai taba komai ba

Abun ya dame kowa amma babu wanda yake da liver tunkarar sa dan ko banafsha daya sake ma yasan ita sam bata iya takura masa ne intaga yayi shiru sai tayi shiru in taga ya damu sai ta kawo abun nishadi tasa shi dariya duk shakuwar sun nan bata hirar minti talatin da shi tana gamawa sai ta tafi abun ta.

TAKAICIN WASUWhere stories live. Discover now