04:triple solidarity

1.5K 137 12
                                    

*♡TAKAICIN WASU🌺*
_the destiny untouched.._

   _A nigerian historical fiction_           _*WATTPAD SURAYYAHMS*_ 
on Wattpad https://my.w.tt/wb29cHKeBab
    
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

*04…tripple solidarity.*

"Sun dade ahaka rungume gam gam da juna sunata kuka ayayin da hanklin sauran inmate ya rabu kashi biyu daya na daga cikin mamakin su daya kuma nakan maira dake kokawa da ranta,manne da juna  wafiyya da bahiyya suke ta rabza kuka kamar ransu zai fice gaba daya ajikin su

Ana hakan waje ya dada rikicewa da surutayaya da rudani,Tahowar matrons da waden da zuka zukan bulalu ya sa kowa ya tsinci kansa cikin nitsuwa inda aka tattara maira aka kaita asibiti aka kuma tafi da wafiyya dakin horarswa.

Ranar tamkar mutuwa akayi a prizon din dan tun kan asake wafiyya da maira kowa yaketa kallon bahiyya wacce ta zauna shiru babu abunda takeyi sai aukin hawaye.

Tanajin an sake su wafiyya ta taho dakin ta,kusan atare suka iso, tsoro yasa su hafsa maimoon da jenifer suka barmusu dakin,sun dade suna kallon juna cikin tsumayi sanannan suka taho da gudu suka sake kankame juna sosai

Bahiyya ta riketa gam gam kamar wacce zata shige cn cikin jikinta ahankli tana sauke nannauyan ajiyan zuciya har sanda wafiyar tayi yar juyayi

"Am soryy..ure hurt?
Ai Saida nace miki karkayi fadan..all for what? look at u now..mugani toh.

Cikin sassanyar kuka mai kashe jiki bahiyya take tartaba fuskan wafiyyar tana jan sheshekarta ahankli
Jikinta yayi ja ja wani gurin yayi kumburi,a duk inda taji ciwon tabi tana dubawa fusknta cike da tsananin tausayinta da matukar kaunarta

Ajiyan zuciya mai rauni da nauyi wafiyya ta sauke
"Tun yaushe kika san ina nan?

Saketa bahiyar tayi ta juya mata baya jiki a sanyaye batare da ta amsata ba

"..meyasa kika share ni bahiyya..
dnt u wanna see me anymore,dnt u miss me?

cikin runtse ido bahiyya ta juyo ta ruko hannun ta zuwa kan gadon tace
" Zauna...

A hnkli wafiyya Ta dan fincike hannun ta hade rai tace
"Bazan zauna ba jus answer my question ok,"wani shiru ne ya gifta,murya kamar na wacce zatayi kuka tace
"Bahiyya inzaki guje kowa amma ai bandani,zaki share kowa amma banda ni...ashe kina nan wajen tuntuni amma Meyasa?kona miki laifi ne..ina babyn?babyn waye ne,kawata Baki taba cemin kina da ciki ba har Yaushe kuka haifu?

Bahiyya tasa hannu akan fuskarta ta share hawayenta dake ta zubowa, slowly. tana famar son ta taro karfin gwiwar fuskntanta juyowa tayi suna hade idanun su waje guda sai taji wani irin nauyi atake saita ji takasa cewa uffan a madadin hakan ma Wani
Matsanancin kuka ne ya kufce mata mai taba zuciya da ratsa imanin duk wani mai sauraro

"Yi takeyi cikin mawuyacin hali na damuwa Numfashin ta kamar zai fice daga kirjinta yay amon wuta..wani irin runtse idanuwanta tayi hawayen kunci da bakin ciki na ambaliya akan fuskanta,muryanta na amo ta dafe bango jikin dakin dan ta sama ma kafarta karfi,cikin azbabben kukan kalaman ya fara ficewa a bakinta batare da ma tasani ba,

"Wafiyya Sunce nina kashe shi,wai ni kashe mijina wasim.
Sauti ta kara ma maganan ta ta wanda ya dadu ne sanadiyar zafin rai da zuciya daya dabaibayeta
"..wafiyya ya za'ayi na kashe mutumin dana fi kauna arayuwata... ya za'ayi na kashe uban ya na?...babyn da kika gani dazun yarmu ce nida wasim muka haifeta
,bayan bacewar ku keda mijinki na same cikin ta
Mijina Wasim ya boye ni awani waje yayita tayani renon cikina  harsai da ciki nan yakai wata tara ba a san inda muke ba

To ranan da zan haihu banda lpya ne sosai ciwon dake damun zuciyana ya tashi,wasim baisan ya zaiyi ba face ya bayyana kansa danya samamin mafita "Na haife baby girl dina agaban idon mijina wasim,yy farinciki kuma ya dauketa ya sumbace ta ya sa mata albarkansa
Yasa mata suna ZAIRAH WASIM KAITA,daga nan shiru tayi fusknta dauke da wata irin guntun murmushi me tsananin ciwo

TAKAICIN WASUWhere stories live. Discover now