CHAPTER 1:Wafiyya wamako

3.5K 300 120
                                    

♡TAKAICIN WASU
_the destiny untouched.._

By SURAYYAHMS

1.
Bismillahirahmarahim
*_new nigeria:The old rectory tropical rain forest escapedes brick construction site_*

Sauri takeyi rungume da yaron ta Cikin jejin da babu komai acikin ta sai wani katoton construction site na tsohon babban campanin buga kayan gini na shahararrren attajiri admr rotarian
Escapedes sarkodie da yake nan a lalace kamar an shafe tarihin sa an mantashi

Cikin kangon campanyn ta shiga daga ita har danta kyawawa ne irin siffar wainda ake cewa sadaka yallah amma saboda wahalan talauci da baqar dau'dar data Kama jikinsu harta dafesu tsananin baqin gashinsu da dan sauran hasken fatar daya rage musu kawai zaka gani kasan cewa ba asalin matalautan bane qaddara ne ya kawo su nan cikin jejin da tayi nisar fiye da tafiyar kwana talatin a kafa daga asalin cikin gari ..

Sam bata mance da hakan dan shekaru biyu da suka wuce itama a kafan ta iso nan musamman dan ta cika umarnin mijin ta ta kuma kare dansu kwalliya daya rage musu a duniya

Zama sukayi a cikin wata yar rumfa acikin kangon companyn dayayi shekaru sama da arabain ba'a qarasashi ba tsufa da alamun zubewa duk sun bayyana a ginin duk da ginine da'akayi na cement zalla Mai qarko da kyau.

Sam girmansa baya Basu tsoro dan kusan Hawa biyarne a ginin, sudai rayuwarsu suke aciki sbd basuda wani gurin xuwa bare zama idan ba Nan dinba

Akwai fatake matafiya da poor village hunters masu wucewa da masu aikin deban yashi suna sayarwa
So wannan kangon nasu kamar wani mafakane wa kowa kusan Sashi sashi ne dan haka ba su kadai bane anan suna tare ne da Wanda basusan ya zasuyi da rayuwar su ba ko idan Mai companin ya nemi su tashiba.

fili ne tarwal a tsakiyan wajen babu abunda yake giftawa se Wani razannen tagwayen tsawa daya bijiro da tsananin hasken walkiyar sa mai harshe biyu wanda ya tsaga sararin samaniya yana mai tsagawa bisa kasa ayayin da duk wani hallitan daya gifta a hanyarsa sai ya kone ko ya tarwatse koma ya rabe biyu.

tauyewar haske da tsawan ya gigita dan nata jijjiga sa take tana masa wani irin wakar raino mai tsaninin dadi da ban tausayi
ayayin da yaron ya kankame ta ya cusa kansa cikin kirjin ta cikin yanayin nuna tsananin shakuwar sa da ita not leaving out the immense mother and son love dayake fallasa kansa a tsakanin sa dn gaba daya hankalinta da dukan kulawarta akan sa yake jijjiga sa take har yayi bacci tana faman murmushi tana kiran sa da wani sunan karrawama wato _kahraman_ kalman kahraman kalmace dake karrama da namiji da harshen yaren musulmai na daular turkiyya musamman in dan ya kasance shine na farko kuma na karshe wajen iyayen sa kalma ne mr nufi da "hero" ko ace 'jarumi' a hausance

Ruwa ake zabgawa kamar da bakin kwarya ayayin da ta shimfide yaron ta akan gadon tsumma datayi masa tana mai sauke ajiyan xuciya

Ahankali dattijon dake kwance tsawon shekaru biyun ba lafiya ya bude idanuwansa daqyar ya 'dorasu akanta

Zaune take kusadashi ta kwantarda kanta kan gwiwowinta ta qurawa qasa ido Wanda yasan idan za sukai wata safiyar ahaka bazatai maganarda ta wuce biyu zuwa uku ba

Tarin da yayi ne ya dada farga  da ita tace...sannu..ya jikin?ko kana buqatar wani Abu?

Wainnan sune kadai kalaman dayasan zata iya furtawa ko kuma yace kullum sune iya maganarta saikuwa idan tana yiwa wayanda suke bata abinci,dan tun zuwar ta take aikin kwasar yashi da daukar blocks dan su rayu da danta
qwaya daya tal aduniya

Sam bata magana ko wasa Wanda shi baima ta6a ganin wasa irin nataba da Babu wata dariya ko motsa jiki saidai murmushi kawai....

Wannan tsoho shiya fara daukar su asalin sunan sa hamza  amma ita baba take ce masa dan ya tsufa sosai akalla xaiyi sabain,shi ya mata jinya ya ciyar da su dan a tsawon gudun tsira da tayi na tsawon kwana talatin xuwa nan babu wani abu na baqar axaba da wahala da bata gani ba.

TAKAICIN WASUWhere stories live. Discover now